page 24

184 13 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*Dayawa suna mun ƙorafin bana tutturawa groups ɗin su to ku sani duk group ɗin da inna turo book ba sayin sharyi ko comment bana turawa koda kuwa group ɗinane ina fatan gane🤷🏻‍♀*


*Page 24*

Nan da nan zan can mutuwar Ameena ta kara ɗe garin, kowa yana jajan ta wannan rashin saboda kowa yasan kyahun halin Ameena daya wa mutane suna tausaya wa su Bilkisu maraicin da zasu shiga.

Imna Larai tana dawowa ya tarar da wannan labarin wani farincikine ya lulluɓeta ɗakinta ta shiga kai tsaye, wani tsalle ta daka tare da murguɗa ɗuwawu. "Kai Allah na gode maka, dama matar nan ta tsayamun a hanci na narasa yadda zanyi da ita, duk so nayi abincin da suka ci ita da ƴarta su zama karuwai na ƙarfi da yaji, amma tunda ke kin tafi to ai shikenan kuma yaran can kwanannan zaku bi bayan ta gaba ɗayan ku, gida ya zama daga ni sai ƴaƴana musha shagalinmu, hhhh." su Samira ne suka shigo dan sunji labari a waje, inna Larai ta basu hannu suka tafa suna dariya.

*******

Hajiya tana da wowa tatarar da Hannatu sai shiri takeyi. " Kekuma lafiyarki ƙalau ? Ina fatan dai kunshirya?" "Hajiya tun ɗa zuma muka shirya, yanzu anjima ma zaizo ɗin." washe baki hajiya tayi. "Yauwa kokefa, yanzu gashi zamu ɗanɗani arziƙi mu barshi a mazaunin sa, wallahi inkika auri yarannan ƙawaye nama saina sanjasu." "Kai hajiya waɗannan ƙawayen nakima ai matan masu kuɗine." "Ke dallacan maikika sani, waɗan da suka fisu arziƙi zan samu ke ni aminiyar babar sama zan zama."

"Kai hajiya kya bari ayi bikin tukunna ko?" "Keni matsa ki bani gu na ɗakko gajiya duk baya nin da zan miki ba ganewa zakiyiba, maza jekisa masu aikinnan su zubo mun abinci su kawo mun, na ɗebo yunwa." "To hajiya." da sauri ta fuce daga ɗakin, maganin data amsowa Huzaifa ta ɗakko shi ta sami jok babba ta juye shi, fiya wata ta ɗakko ta jujjuye aciki saida taga yayi damm sannan ta rufe ta ajiye agefe sannan ta samu guri ta zauna, Fatima ce ta shigo ɗakin. "Hajiya sannu da zuwa." washe baki hajiya tayi. "Yauwa ƴarnan kinga wannan jok ɗin maganine na amsowa mijinku nanda wata ɗaya zai warke suɓul abunsa." murmushin dole Fatima tayi saboda yanzu ba wannane a gaban taba. "Hajiya dama zuwa nayi in gaya miki gobe za'a kawo kayan garar ɗazu aka turo daga gida kuma baƙya nan." wata irin dariya hajiya tayi. "Kai Allah ya kaimu, iyayenki suna sonki sosai ƴar nan daga magana harsun cika aiki, gashi duk cikinsu kece iyayenki masu rashin kuɗi amma kuma sunfi masu kuɗin hazaƙa,Allah ya sadai suhaɗo da babbar jarkar manja da su albasa." saka to Fatima tayi tana kallon ikon Allah wannan wace irin mata ce, take tunani, ƙaƙalo murmushi tayi tare da tashi ta futo, tana futa Hannatu ta shigo ɗauke da flat a rufe, agaban hajiya ta dirshi. "Gashi hajiya sun gama tun ɗazu ashe." janyo flat ɗin hajiya tayi ta buɗe shinkafa ce da taliya da miya. "Ai ingaya miki Hannatu munkusa fara warwa sawa da kayan abinci, gobe ƴan uwan Fatima zasu kawo gararsu." "Kai hajiya kice zamu ci su alkaki da dubulan dama na daɗe ban ciba, bara inje in yi wanka tunda nagama goge kayan, naga magariba ta kawo kai yanzu za'a fara kiran sallah." gyaɗa mata kai hajiya kawai tayi,saboda ta cika bakinta da lomar abinci.

Ana gama kiran Sallar magariba gari yayi duhu sossi Big boy ya tawo gidan su Hannatu, yana zuwa kai tsaye ya shogo cikin gidan dama mai gadi ya sanshi, ɗakin Zabba'u ya shige sannan ya turawa da Hannatu massage. "Salam byba ganinan nazo gidanku zan bawa Zabba'u saƙo ssnnan inzo in gaida hajiya." yana zaune afalo kan kujera yayin da Zabba'u take kan cinyar sa."Kinga maza rufe mana ƙofa muje mu yi abunda ya kawo mu, karsuga na daɗe ko? " "Kai dai Big boy rabu da sha'anin wannan matar karfa cefa ba ganewa zata yiba." gaba ɗayan su suka kwashe da dariya.

Hannatu kuwa ita da hajiya suna ta zuba ido suga shigowar sa amma shiru sai wajen 40mn sannan ya shigo kansa a ƙasa irin na masu kunyar nan.

Cikin girma mawa ya gaida hajiya sosai ita kuma sai washe baki takeyi, hannu yasa a aljihu ya ɗakko mukullin mota ya miƙawa hajiya. "Gashi da motar nazo, tana can farfajiyar gidan." "Kai amma yarannan nagode maka sosai, yanzu to taya zak koma gida?" "Ai hajiya da direbana nazo ya hawo tawa motar ni nahawo taki." "To to Allah dai yayi Albarka yanuna mana auranku ameen amee." tashi yayi ya fuce yayin da Hannatu tayi saurin bin bayan sa.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now