page 4

331 23 0
                                    


NA
Real shaxee


Yamma tanayi kowacce ta dau kwalliyar tarbar mijinta ta zauna adakinta amma kowacce kunneta awaje yake.

jikin hajiya kuwa da sauki tana zaune afalo ita da Hannatu suna cin kayan marmari suna hirarsu.

Fatima tana dakinta sai safa da marwa take cikin yakini tace." Yau ko da tsiya koda azziki nice zan kwana da mijina nice zan fara dandana amarci kafun wadancan mahaukatan,surigani nasan habaici zantasha gwara ni inrigasu inta gaya musu magana wallahi zakuga kissa ganin idonku duk da dai nasan wancan dan iskan bokan ya kawarmun da budircina amma koda yake ainaje asibiti andinkeni banida wata damuwa ko daya." murmushi tayi tare da dakko turare ta fesawa jikinta ko ina da ina duk da cewa dazuma ta fesa.

Zabba'u kuwa cikin kananun kaya jins da tishet tasaka tazubo da kalbarta ta gashin doki tadau kwalliya tare da shafa turaruruka yaje firij dinta ta dakko ruwa tare da balle wata kwaya akan mudubi ta hadiya ta zauna." Yau ni amaryace ko anaso ko ana ki saina kwana adakin mijina wannan kwayar saita haukatashi wallahi indai ya dandanani to wadancan mahaukatan sai dai kuyi hakuri fa." wata dariyar mugunta ta kwashe da ita ta,dau wayarta tahau chating.

Sadiya kuwa tana zaune abakin gado ta dama wannan ta dama wancan tana sha sannan taje firij dinta ta dakko wani uban tsimi cikin jarka ta diddika sannan ta fada wanka tana futowa tadau wata damammiyar doguwar riga yar kanti tasaka tayi fakin din gashinta ko dankwali bata sakaba ta zauna akan,kujera tana jiran angonta.

Nusaiba kuwa tana kwance tana uban chating tana babbaga dariyarta zuwa can kuma saita kalli bango ta kwashe da wata uwar dariya." lallaima wadancan yaran basu sanniba zan koya muku hankali cikin ruwan sanyi." ta yi murmushi sannan ta cigaba da chating dinta.

Sadiya kuwa wayar ta take da mutanan ta baruwanta tun kwalliyar dazuce ajikinta ko wanka batayiba.

Ana kidar da sallar magariba saiga Huzaifa ya dawo kai tsaye dakin mahaifiyar sa yanufa domun wannan al adassace." A yaron kirki kadawo ashe." waje yasamu yazauna."Hajiya ya gida ya jikin." Jiki alhamdulillah maza ka tashi katafi gun matan naka ko kasan yanzu bakamar da bace da zaka zauna anan ko.'' danne zuciyar sa yayi yayi murmushin wahala yatashi yafuto daga dakin kai tsaye dakinsa yanufa ya cire kayan jikinsa yafada ban daki yana cikin wanka yajiyo haya niya na tashi a falonsa da sauri yafuto ya zira jallabiya ya futo falon su ukune banda Sadiya acikin dakin suketa cece kuce wannan tana wallahi yau kwanantane wannan tana kwanan tane zugumm yayi yana kallonsu somun ko alabari baitaba jin inda amarya take fadan kwanan ta bane hasalima gudun angon suke ganin fadan nasu bana kare duk sun zubar da abinci afalon wanda aka jera masa akasa da zumman yaci tare da matansa ransa yagana baci aikwa yadaka musu uwar tsawa." Ku mahaukatan inane bakuda hankali dama bansaniba wannan ai haukane da gidadanci zakuzo kunamun ihu cikin dare to wallahi ku kiyayeni mahaukatan banza mahau katan hofi kuma kuyi sauri ku gyara inda kuka bata yanzunnan sannan kowacce takama gabanta domun ba abunda zan iyayimuku maza nace." dasauri suka futa dan dakko abun gyara saboda yayi matukar basu tsoro gyara gurin suke kana gani kasan basu iyaba Fatice kawai acikinsu ta iya aikin suna gamawa suka fuce kowacce tayi dakinta.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now