page 34

188 15 1
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*Nayauma taɓa ka lashe ne🤭*

*Page 34*

Kicin ɗin ya koma ya tsaya har ruwan yayi zafi, sannan ya juyo a ɗan bokiti ya ɗora wani ya shigo ɗakin ban ɗakinta ya huce inda ya juye mata aroba mai faɗi ya buɗe duram ɗin ban ɗakin cikin sa'a akwai ruwa ya sirka mata da ɗan zafi tukun ya futo. "Garuwan can wanda zaki gasa jikin ki a roba na wankan a bokiti, kodai inzo in miki bazaki iyaba?" cikin zolaya yayi furucin, itama dariya tayi sannan ta tashi tashige ta rufo ƙofa, dama matar yayan ta tagaya mata duk yadda zatayi ta gyara jikinta.

Baffa yana ganin ta shiga wankan yayi wata miƙa. "Kai angwanci ma yana da daɗi sosai wallahi, jibeni yadda nadawo wani iri jina nake uwa duk duniya babu wanda yakai ni farinciki, kafun in haɗu da masifar Larai dan nasan tana nan tana jirana." ɗan girgiza kansa yayi tukun ya koma kicin ɗin.

Tana futowa ashina ya shiga ya tsarkake jikinsa tukun ya futo daga ɗakin zuwa masallaci, Rukayya kuma tayi sallar ta aɗakinta.

*Gurin su hajiya*

Ganin mai gadi bashida amfani yasa hajiya ta lalubo wayar likitan da ƙyar ta miƙawa mai gadin. "Maza yimasa magana." da sauri mai gadi ya amsa yasa akunnen sa yanajin likitan ya ɗaga ya fara magana. "Likita maza kazo inji hajiya bata da lafiya." daga can likita yace. "Ok ganinan zuwa." maigadi ya miƙa mata wayar. "Hajiya yace gashinan zuwa." gyaɗa masa kai kawai tayi mai gadi bai tafiba ya zauna yanata kiran Huzaifa amma wayar haryau baya ɗaga wa.

Ba yan ɗan lokaci saiga likita yazo nan da nan ya fara duba su, babu karaya aduk jikinsu saidai dukan dasuka sha baki ya face idon hajiya ɗaya ya kumbura yayi baƙi, magun gunan ƙara ƙarfin jiki da kuma na rage raɗaɗi ya basu sannan yace su dinga gasa jikin su.

Hannatu tana ɗakinta akwance barci ya ɗauketa zuwa can yamma ta farka kiran big boy ta gani awayar ta yafi guda goma,cikin hanzari ta bi kiran bugu na farko ya ɗaga. "Hany ina kika shigane? Tun ɗazu naketa kiran wayarki." "Kayi haƙuri bana kusa da wayarne baccine ya ɗaukeni." "Ok babu da muwa anjima ana ƙidar da sallar magariba zanzo mutafi." tunani take zata kwa iya zuwa dan duk jikinta tsami yake yimata amma kuma ta tuna yadda yakeson futarnan intace bazata jeba ransa zaiɓaci dan haka tace. "To shikenan saikazo." Ta kashe wayar sannan ta futo ta nufi ɗakin hajiya wacce ta tarar da ita tana shan shayi gefanta kuma ƴar aikin suce take mammatsa mata kafa, zama tayi akusa da hajiyar. "Hajiya ya jikin naki?" "Hannatu jiki gashinan dai wallahi yarin yar nan bata yiba kwata-kwata jibi yadda tamana duka shikuma wancan anata kiran wayarsa bai ɗauka ba, jiran sa nake yazo dan wallahi sai naɗau babban mataki akan yarinyar nan in banda hula ƙanci ni ɗin tabb." "Hajiya ai dama batun rabuwa da ita bai tasoba da ƴan sanda za'a haɗata tadaku ita ma, yanzu nake gaya wa big boy shine yace wai baiyadda da dubanin da akayiba inshirya bayan sallar magariba sai kaini asibintin sa daya gida adubani sosai." "Kunji yaran arziƙi mai kula da iyalin sa tunkan aure, wannan abun dayayi yass naƙara sonsa nasan ko anyi auran zai kula dake sosai maza jeki shirya Allah ya tsare hanya, kitawo mun da kayan dubiya." murmushi Hannatu tayi sannan ta tashi ta futo daga ɗakin tana murmushin jin daɗin tasamu damar futa dama tana ta tunanin ƙaryar da zatayi ta fece.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now