https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*Page 15*
Duk cikin ƴaƴan Amina babu wanda inna Larai ta tsana kamar wannan yarinyar wacce aka saka mata suna Bilkisu Amina tana ƙunsar baƙin ciki amma kasan cewar tana da haƙuri sosai shiyasa baffa Jauro yake sonta.
Bilkisu tana da shekara goma sha huɗu Amina ta kwanta ciwo yayyan ta suna matuƙar ƙoƙari gun kula da umman su Auwalu da Sani da Salisu da Rabi'u suna bin baffan su kiwo kuma suna kula da ƙanwar su da umman su.
Inna Laraice a zaune a tsakar gida akan ƴar tsugunno tana gyara zogale, Bilkisu ce ta futo daga madafa ɗauke da kwano a hanun ta. " Ke ƴar gidan aljanu uban mai kika ɗakko a wannan kwanon?" cikin tsoro tace. "Inna koko ne na dama wa mama tace mun tanason ta sha." " To uwar kini bibi ni ina ruwana maza jeki kai kizo kimun wanke wanke da shara kuma ki jawo mun ruwa a rijiya kicika mun komai nawa." " To inna bara in bata kokon inzo." "iheee! Ni kike gayawa haka saikin bawa waccan gawar abu sannan zakizo kimun aikina to wallahi baki isaba maza jeki ajiye kizo kimun aikina ko in ɓallaki a acikin gidannan." da sauri ta shige ɗakin su inda maman su take a jingine akan gadon ta. " Bilkisu maza jekiyi abunda ta saki kibar wannan in wani daga cikin yayyan ki sun zo saisu bani insha, maza jeki karta bugeki watarana sai labari." " To mama." kwanon ta ajiye ta fuce da sauri ta fara aikin ta.Hannatu tasha mamaki a gun patyn kowacce cikin matsatstsiyar shiga rungume da saurayi wasu kuma suna shan ƙwaya wasu kuma suna rawa da samari taji daɗin gun amma takasa sakin jikin ta ganin hakan yasa big boy ya jawo hannunta suka shiga filin rawa suka fara takawa nan da nan abokan big boy suka fara yimusu ruwan kuɗi ana ihu, hannatu kuwa ta fara sakin jiki ta rawa, suna gama wa akazo a ka yanka cake sannan biki ya tashi su hannatu suka nufo gida naira dubu ɗari da hamsin ya ɗora mata akan cinyar ta. " Gashi wannan inji abokaina kisiyi kayan kwalliya." murmushi tayi ta ɗauka ta sasu a cikin jakarta suka cigaba da tafiya.
Huzaifa kuwa yana falon hajiya azaune yana cin abinci. " Hajiya nifa haryau banga Hannatuba kota ina ne? Washe baki hajiya tayi dama kaɗan take jira. " Ai in gaya maka wannan yaron arziƙin nan ne yazo suka tafi fatyn abokinsa yana so ya nunawa abokanan sa matar da zai aura, shine suke can." har ya ɗakko loma zaikai bakinsa ya tsaya yana kallonta. " Faty fa kikace hajiya? Awannan daran kuma da mutumin da ba asan kowane ne shiba."
