https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*DEDICATE TO*
*BINTA UMAR*😘😘😘*Page 40*
Tana zuwa bakin rijiyar ta wani fizge gugan a hanun Ruƙayya, ko ƙala bata cemata ba taɗau iya wanda taja tashige ɗakinta, shiru-shiru basuga ta futoba har suka gaji da jira suka haƙura amma ransu yayi matuƙar ɓaci.
*Bayan wata ɗaya.*
Bilkisu da su Auwalu sun dawo gidan baban su Ruƙayya tana matuƙar ji dasu, hakan ba ƙaramun ƙona zuciyar Inna Larai yake ba.
Inna Larai ce azaune acikin wata bukka cikin jejin Allah ta'ala. "Boka inaso akashe mun wannan kishiyar tawa saboda ba ƙaramun hautsinamun kai take ba." wani mutun daya ke kan buzune yayi zane-zanen sa aƙasa sannan ya ɗago kai ya kalleta. "Bazata mutuba yanzu saboda tanada ragowar rayuwa anan gaba saidai ki faɗi wani abun da za'ayi mata." shiru tayi na ɗan wani lokaci sannan tace. "Inaso amaida ita uwa matacciya kai ni kawai ma ayi mata kucciya ta ɓace ɓat adaina ganinta, shikuma mijina inaso ya zama mujin tace sai abunda nace kuma ya dinga matuƙar tsorona, sannan kuma ita Ruƙayyan inta ɓace arufe bakin kowa kar wanda ya ƙara maganar ta." zana ƙasa yayi tukun yace. "Wannan aikin ki ɗauka tamkar an gama miki shi, jeki bayan bukkar nan zakiga wata kucciya ki ɗakkota da hanunki ki kawota nan." da ƴanzari ta tashi taje aikuwa kucciyar tana tsaye ta kamota ta kawota.
Wata laya yasa ahuyan kucciyar sannan yace. " Kije can gaban jejin nan ki saki kucciyar kifaɗi sunan yarinyar sau ɗaya tak to indai ta rashi itama zata shiga duniya, wannan layar kuma ungota inkije hanyar futa daga jejin nan zakiga wata shekaraeriyar rijiya ki cilla aciki, to duk wanda ya santa bazai ƙara maganar taba har abada, wannan kuma garin maganin kije ki sami ƙaton ƙadan gare ki tsaƙe masa huya ya mutu sai ki samu laida mai kyau ki ɗaure maganin nan sossi kisamu allura guda goma sha biyar saimi saka maganin abakin ƙadan garan aluran kuma ki tsitstsira masa ajikinsa shikenan kin gama da mijinki kamar waina a tanda." wani washe baki tayi cikin farin ciki ta kwaso duk ƙuɗin jakarta ta rage kaɗan ta juye masa dama ta daɗe tana tarasu.Kallon ta yayi tukun yace. "Duk wannan aikin danayi miki su akwai makarinsu guda ɗaya tak, karki kuskura kici nama kowane irine sannan kuma karki kuskura koda da rana ɗayane ki kusanci mijinki yin hakan zaisa komai ya wargaje amma zaki iya mu'ammala da kowane namiji, inma ba damuwa zaki iya zuwannan ki kashe ƙishirruwar ki." yafaɗa yana washe baki yana siɗe leɓe.
"Ai malam karka damu zan kiyaye komai indai buƙatata zata biya nikuma zan baka komenene dana ke dashi aduniya." cikin ƙwarin gwiywa take faɗa, tashi taƴi ta futo daga bukkar.
Duk saida ta tsaya tayi komai kamar yadda yace haka tayi a ƙauyen dayake gabansu ta tsaya tasai aluran tayi aikin ƙadan garan ma sannan ta sashi ajaka ta tawo gida.
Inna Larai tana zuwa gida ta kalli ɗakin Ruƙayya tare da wani yin mugun murmushi. "yarinya iyanzu kinzama tarihi ko zaki ko damusa ko ƴan fashi su ƙarasa ki, angaya miki niɗin wasace kinata wani feleƙenki yau nayi maganinki." afili take faɗar hakan ko ajikinta,Bilkisu taga ta futo daga ɗakin anty tasu tanata dube-dube, cikin tsawa tace. "Uban mai kike naima! Saiwani juye-juye kike." ta buɗe baki da niyar magana saita kasa, kawai sai tayi shiru.
Ganin haka da inna Larai tayine yasata gane aikinta yayi nasara yadda takeso."Maza huce kije ki ɗoramun tuwon dare." da sauri Bilkisu ta huce madafar Inna larai tafara kunna huta.
Inna Larai cikin isa ta huce ɗakinta tana cewa."Aini kuma yanzu kakata ta yanke saƙa ssi abunda nagadama zanyi acikin gidannan."
