page 35

165 16 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 35*

Sun gama karya war tas yanzu hira sukeyi abunsu cikin gwanin sha'awa.

Inna Larai ce a tsaye a tsakar gida ta riƙe ƙugu tana kallo ƙofar ɗakin Ruƙayya tana ƙwafa, Laure tace. "Inna wai dan baffa ya auro wannan daƙiƙiyar shine yau ko zuwa ma ya bamu kuɗin abun kari bai yiba, duba fa kiga yanzu wajen ƙarfe takwas ba ma mukunna huta ba, gaskiya kije da kanki kiyi maganinsu ai wannan iskanci ne wallahi taɓɓɓɓ." girgiza kai kawai inna take, Samira ma tace. "Wallahi inna sai munyi maganin yarinyar nan acikin gidannan muzata nunawa rashin mutunci yayar ta tayi mana, munsamu ta kauce ita kuma tazo zata ɗora daga inda waccan ta tsaya." wani huci inna Larai kawai take dan haka ta nufi ƙofar ɗakin cikin masifa ta fara magana. "To tattabara uban aure kafuto nan ina son ganinka, muna fukin Allah da ni ce agidannan da tuni ka saka kai kafuce daga cikin gidannan amma dan muna furci yau kama ƙi zuwa kabamu abun kari to wallahi baka isaba."

Jiyo hayaniyar ta da baffa yayi sannan yama tuna baibasu kuɗin gasara da ƙosaiba ɗazu dama niyarsa inya duba yadda suka tashi ya bata amma masifar ta, tasa shi mantawa, Ruƙayya gani tayi da gaske tashi yake ƙoƙarin yi, Ruƙayya tayi wani malalacin murmushi, baffa bai ankaraba kawai yaji bakinta acikin nasa, wayyo tuni yama manta aduniyar dayake, Ruƙayya sai saƙwanni take tura masa shikuma yana amshewa.

Jimmm inna Larai taga bai futoba abun yabata mamaki, saboda lokacin Amina intaso muzguna musu data fara faɗan ta zai futo yana bata haƙuri amma yanzu shiru uwa anaiki bawa garinsu. " Au mahau kaciya ma kuka mai dani kenan? Zaka futo koni saina shigo ɗakin? Wallahi idan nashigo saidai ku akwashe ku zuwa asibiti dan saina illataku." shiru dai kakeji dan haka ta ƙarasa dab da ƙofar ta turata, amma gamm ƙofa arufe, bugu ta farayi na ɗaga hankali, amma ina Baffa yayi nisa a jirgin shauƙi baima san tanayi ba, Ruƙayya kuwa tas take jinta amma sai ƙara ma sabon salo take yi masa.

Inna Larai ta gaji da bugu dan haka ta dawo ƙofar ɗakinta ta tsaya. "Ni wannan mutumin zaiyiwa haka, wallahi ya taɓo abun da bazai iya tarewa ba, daga shi har ita zasusan dani suke." bawan da yayi magana duk sun zubawa ƙofar su Baffa ido amma shiru maƙatau kukeji ganin abun da gaskene inna Larai ta kunce bakin zaninta. "Maza Laure jeki kisiyo mana gasara da ƙosai mu karya, shikuma wallahi zai same nine saiya biyani ninkin kuɗina kuma ga kwandon bala'in da zai tarar nice ba hmm." Laure ta amshi kuɗin. "Inna ai dama kece kike raga musu shiyasa suka fara da haka, ni bara inyi sauri dan yunwar tana naiman fin ƙarfina."

Su baffa abu yayi nisa har an dangane da uwar ɗaki, yana dawowa dai-dai ya rungume Ruƙayya suka koma barci abunsu.

Laure ta dawo inna ta dama musu koko suka zauna suna karyawa bawan da yake magana kowa da tunanin daya keyi.

Sai 12:am sannan su Ruƙayya suka tashi sukayi wanka kowanne ya shirya jikinsa, baffa yayi shirin futa Ruƙayya har bakin ƙofa ta rakoshi tayi masa addu'a ya futo ita kuma ta koma ɗakinta.

Yana futowa ya tarar da Inna Larai azaune a kan kujera su Laure suna shara da wanke-wanke. "Larai ina kwana." baffa ya faɗa cikin sakin fuska. "Ban saniba uban ƴan kini bibi, wata kan ga ƴar rainin wayon ka ko, ko abun kari baka bamuba kaje ka maƙalewa ƙaramar yarinya sa'ar ƴaƴan ka, kuma dan rainin hankali inzo ina buga muku ƙofa amma kuka maidani wata mahauka ciya, to wallahi dai-dai nake da ku, kuma kayi gaggawar biyana kuɗin karin safen dana kashe naira ɗari huɗu zaka bani, sannan kaban kuɗin cefanen rana, kuma kassni karma ka kuskura ka ce zamu haɗa girki dan wallahi bazai yuhuba eheee." girgiza kai kawai yayi sannan ya zaro ɗari bakwai ya bata, ya juya ya koma ɗakin Ruƙayya saboda yama manta bai bata kuɗin cefane ba. "To jarababbe komawa zaka yi? " ko juyo wa bai yiba ya ƙwanƙwasa ɗakin.

Tana buɗewa ya shige. "Ya haƙuri na manta ban baki kuɗin cefane bane." yafaɗa yana lalibo aljihunsa. "A a baffa nidai nafiso kadinga siyomun komai da kanka kana kawomun bana son indinga amsar kuɗin cefane, kuma ma ai ga kayan abinci can kawai kawai kayan miya za asiyo." "To shikenan tunda haka kikeso yanzu ki gayan mai dame za'a siyo miki."

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now