page 9

499 25 0
                                    

Na
Zainab Abdullahi
(Real_shaxee)🍒

Kuyi hakuri da jina shiru wattad dinane yasamu matsala da kyar ya gyaru.

A zabure Fatima ta mike. " wace matsala ce boka." " Matsalar ita ce akwai wacce ta wacce in bakiyi wasa ba zata war gaza miki komai bama ke daiba ga duk wani mai mugun shiri akan ta,sannan kuma in bakiyi wasa da wannan surukar taku ba to zata lalata wani abu." wani mugun huci Fatima tayi sannan tace. " Wannan hajiyar zan kiyaye da ita dayar ce dai nakeson sanin kowa ce ce ita." " Agaskiya ba a nuna mana ita ba kuma baza mu iya yimata komaiba, kidai kiyaye kawai." " to shike nan boka." wani garin magani ya mika mata. " Ungo wannan kizuba a abinci kowa yaci amma akansa da babarsa kawai zaiyi aiki ragowar kuma aikin da zai yimusu shine zasu dinga shakkarki." wani mala lacin murmushi tayi. " Angama boka ga kudin aikin ka."

Cikin farin ciki ta baro gidan boka ta tawo gida, tana zuwa ta shige daki ta kwanta abunta.

Hajiya kuwa da santin big boy ta kwana aranta da safe tana ta shita hau yiwa Hannatu hirarsa tare da yabonsa ganin hannatun itama tana sonsa hajiya takara jin dadi sosai aranta. " Hannatu kinga yayan ki jiya bai shigoba yauma bai shigoba ko lafiya kuwa." "Tayu ko wani abunne ya hana shi zuwa dama kin hadashi da wannan zuka zukan matan badole yadinga manta wasu abu buwanba." "hhhh kinji ja'irar yarinya, ai haka nakeso yaje ya taramun yara agidannan muyi ta wasa dasu kema kita haifa mun su."

Zabba'u kuwa tana daki tana waya da big boy. " Kaifa wannan matar haka take son kudin tsiyane da ita, gata dai acikin daula amma bata gani na hannun wani take hange." daga can big boy yace. " Ai naga alama kuma zata sha kudi kam indai buka ta zata biya kema zaki sami naki tukiycin." "hhh ai kuwa zaka samu indai zaka saki bakin aljihu yauma ka zo tare da siyayya mai yawa ka kawo mata, zaka sha mamaki." "Ai kuwa ki jira ni saina zo." ta kashe wayar tare da yin murmushin jin dadi.

Big boy kuwa sahad ya shiga inda ya keta lodo siyayya kala kala sannan yashiga Alwabil yasiyi atamfofi masu tsada da takalma da dogayan ruguna ya kashe kudi sosai, sannan ya koma gida yana jiran dare yayi yaje gidan su Hannatu.

Fatima kuwa saida ta san anfara girkin dare sannan ta nufi kicin din yan aiki sunata aikinsu, ta wayan ce uwa ta yasu takeyi su biyune suke girki, ta kalli babbar ciki wato Indo tace. " Indo maza jeki falona ki dakko mun waya ta kar a kirani ina nan, banji ba." " To hajiya." tana ganin ta futa ta kalli dayar tace. " Shamsiyya maza jeki debomun dan kali zanyi amfani da shi." " To hajiya." ta fuce da sauri aikuwa tayi sauri ta zuba ta juya miyar sosai suna dawo ta basar ba afi minti shida ba tabar kicindin.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now