page 19

230 10 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 19*

Nusaiba kuwa waya take da ƙawarta. "Ke ani ko ajikina tunda dama nafi harka da mata maza basa bani sha'awa ko kaɗan, tunda hakan ta faru suje can su ƙara ta, ni ba wani damuwa zanyiba kuma yanzune na samu lasisin yin abunda na gadama." hirarsu suka ɗan taɓa sannan ta kashe wayar ta kwanta.

Hannatu tana ɗaki suna waya da ɓig boy. "Nifa wallahi ban iya wannan shan mintin ba, ina dai ji ƙawaye na suna yin hirar lokacin muna makaranta." daga can yace. "Kinga yanzu duk rayuwar nan haka akeyinta inkinga mutane basa yin haka to ba wayayyu bane, karki ɗaukeni ɗan iska kokuma wani abun kawai dai ni rayuwar ƴanci nakeyi akomai nawa, dan haka sai anjima." "Kaga wal... Kanta ƙara sa ya kashe wayar sa, da sauri tabi wayar amma bai ɗaga ba kira wajen biyar bai ɗagaba data ƙara kira kuma wayar akashe. "Nashiga uku wallahi bai fahimceni bane ni ban ɗauke shi ɗan iskaba kawaidai tsoro nakeji gashi kuma yaji haushi, yanzu yazanyi da raina." da wannan zulimin ta samu barci yasace ta.

Big boy kuwa yana kashe wayar yayi wata ƙara. "Yarinya takusa zuwa hannu, burina ya kusa cika wallahi heeehuuuu." ya daka tsalle tare da hayewa kan lallausan gadon sa wanda yasha shinfuɗa mai tsada.

*9:00am*

Dukansu sun hallara a falon hajiya Hannatu ce kawai bata gun. "Waini kunzo kunsa ni agaba gaba ɗayan ku baku cemun komai ba, inba za ku iya magana ba to kutashi kuba ni gu." cikin faɗa hajiya tayi magana, gyara zama Huzaifa yayi, yayi mata bayani dallal-dallah tare da bata takaddun gwajin. " Ƴo ni wani karatun boko nayi daza ka haɗani da wannan takaddar nasara, indai wannan ne matsalar aiba komai nanda sati biyu komai zai huce, abunda ga maganin garga jiya nan k... "Hajiya gaskiya ni bazan iya zama ba ina buƙatar ta kaddata." Sadiya ce tayi saurin katse hajiya. "To baza a sakeki ba ɗin kiyi abunda kika gadama." cikin harzuƙa yajiya ta mayar mata da amsa.

Miƙewa tsaye Sadiya tayi."Aikuwa wallahi baki isaba, kinyi kaɗan kihanani abunda nakeson yi inkuma kin isa to bisimilla zaki sha mamaki." ko tsaya wa bata yiba ta fuce afusa ce.

Bilkisu bayan sundawo ta shigo cikin gidan,cikin sa'a kuwa babu kowa a tsakar gidan, ɗakinsu ta nufa inda ta tarar da su Salisu dukansu azaune Auwalu yana yiwa umman su tausa. "Daga ina kike? Mundawo bamu gankiba." Auwalune yake tambayar ta. "Yaya wallahi nida yaya Musani ya dawo yazo mugaisa, shine naraka shi gidan kaka maiƙuli lokacin umma tana barci shiyasa ban gaya mataba." "To shikenan amma kidaina daɗewa kinji." "To yaya." "Maza zo ga kifi natawo miki dashi nasan kina sonsa." "Lah yaya Auwalu inka nada kuɗi kakawo inje insiyo mana taliya agidan su Barira." "Mai kuma za ayi da taliya? "Yaya Auwalu inna Larai ta hanamu abinci yau ma." shiru dukan su sukayi Rabi'u ne yazaro naira ɗari a aljihunsa." Zomuje musiyo hadda kayan miya ma sai mudawo muda fa ko? Murmushi tayi tare da saurin tashi Sani ya miƙo masa wani kuɗin. "Ungo ku ƙara akai kusiyo." amsa sukayi suka fuce, cikin ƙauna umman su take kallonsu tana mai farin cikin kasan cewar yaran ta suna son junansu.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now