page 17

260 14 1
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*Dayawan ku kuna mun ƙorafin cewa inƙara yawan type ɗina karku manta ina yawan cewa adadin comment adadin type nadaina wahalar da kaina inta rubutu in ƙiyin abun gabana inturo muku babu sharye bare kuma godiya shiyasa nadaina wahalar da lokacina da hannuna inkunyi comment da yawa kuga type da yawa 🤷🏻‍♀*


*Page 17*

Hannatu tana ganin yabar ɗakin tahau bawa ajiya labarin gun paty tare da bata kuɗin da Big boy ya bata wata shewa hajiya tayi tare da rangaɗa buɗa. "Aini nasa ban haifi yara masu ƙashin tsiya ba, insha Allah saiburina ya cika aduniya in ganni cikin hamshaƙan matan masu kuɗi ke harda matan gwamna, ina fanta mawata abuna ko ina masu kula da ni, ƴaƴana ma su zama masu faɗa aji a garinnan." "Kai hajiya yanzuma ai mu masu kuɗine." "kedallacan rufemun baki ina muka ga kuɗi akan wasu masu kuɗin garinnan inaso inzama daga cikin mutannan da in za ayi labarinsu ace basusan adadin dukiyar suba." "To aishike nan hajiya ni bara in je in kwanta dan nagaji sosai nasha rawa." "Ke tsaya ni baki ma gayamun a ina kika samo waɗannan kayan jikin nakiba nasan dai bada su kika futaba a ina kika samu? Dawowa tayi ta zauna sannan tabawa hajiya labari.

Fatima tana ɗakin Huzaifa tasha kwalliya, yana shiga ya ganta zama yayi. "Sannu da zuwa ongona." gaban sane yayi wani mummunan faɗuwa jin ta ambace shi da ango, ɗago kai yayi ya kalleta sannan yace. "Maza jeki kira womun ragowar ƴan uwan naki." duk da taji babu daɗi amma bata nuna akan fuskar taba, tana futa yayi ta gumi, cikin zuciyar sa yake cewa. "Gaskiya anty ta faɗa gwara inbi shawar ta kona rage wani ɓacin r... Shigowar suce tasashi katse guntun tunanin sa daya keyi, kowacce acikin su tana tunanin faɗa zai musu akan abunda sukayi, kowacce waje ta samu ta zauna, kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya sannan ya fara da cewa.

Inna Larai ce azaune ita da ƴar ta Samira suna tsakar gida suna gyara wake. "Inna wai yaushe zaki yi maganin waccan yarinyar ne? Nifa har mamaki nakeyi taya akayi tafimu kyau gashi baffa yafi sonsu akanmu." "Hmmm kedai Samira ki kwantar da hankalinki ina nan nakusa yin maganin su kwanan nan, bakiga nadage da naiman kuɗiba nan da wasu ƴan kwanaki zanje ƙyauyan su Barira ina dawowa zakisha mama ki." "Kai inna da kuwa naji daɗi, yauwa inta dawo ma kisa ta wanke mun waɗan can kayan nawa saboda gobe su nakeso insa intafi tallah." miƙewa inna Larai tayi ta nufi madafa. "Karki damu bara ta dawo kedai yi maza ki ƙarasa wannan aikin naki, waini yaushe yarannan Sabi'u zai turo iyayen sane? ya kamata yazo ayi agama." "Inna karki damu zan gaya mass kinsan bashi da matsala tunda baban sa mai kuɗine shanunsa fa sunada yawa banda gonaki." wata buɗa inna Larai tayi. "Ai shiya sa zamu ƙara mallakeshi kedai bari kuɗi su shigo mun zamu yi yadda muke so." wata dariya suka kwashe da ita.

Umman Bilkisu duk tana jinsu Addu'a take azuciyar ta akan Allah ya tsare mata yaranta aduk inda suke.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now