page 42

166 23 2
                                    

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*mutane dayawa kunamun ƙorafin inƙara yawan type yayi muku kaɗan karku manta inayi abunane akan yadda zan iya, yawan comment ɗinku da sharyi yawan type ɗin dazaku gani shiyasa zakuga wani da yawa wani kuma kaɗan, inkun gyara nima na gyara🤷🏻‍♀*


*Page 42*

Bilkisu ta fiya take tanata wai waye kuma cikin sauri. "Wacece wannan anan gun." taji an anbata daga bayan gaban ta yayi wata muguwar faɗuwa jikin ta ya fara rawa, a hankali ta juyo, samari ne guda biyu kowanne ɗauke yake da kayan fulani da kuma sanda a huyansa. "Inna tace ta turo ni nan inmata itacen dazatayi girki." ɗaya daga cikin su ya karkata kansa yana kallonta. "Kice dai ta turo mana icen da zamu gasa babbar kaza ko bahaka ba yallo." wata dariya wanda aka kira da yallo yayi sannan yace. "Ƙwarai kuwa dama kwana biyu ban buɗe sabuwa ba sai tsofaffi gashi yau na samu cikin sauƙi." hawa yene ya fara zuba afuskar ta. "Dan Allah kuyi haƙuri wallahi bantaɓa zuwa nan ba yanzuma dole akayimun ne shiyasa nazo." "Wannan kuma ke kika sani amma mukan babu abunda zai hanamu abunda muƙayi niyya ragowar kuma ya rage naki kokiyi shiru asirinki ya rufu koki futo ki faɗa kizama abar kwatan ce agarinnan kuma kin san kaf garinnan babu wanda ya isa yayi mana wani abu, kinga kekuma ko mijin aure bazaki samuba." yallo ne ya fuzgota zuwa jikinsa icen kanta ya faɗi kokawar ƙwacewa tafarayi amma ina riƙon ba na wasa bane, kokawar rabata da kayan jikinta sukeyi duk sun yaga mata kaya, ƙafarta ta ɗaga ta take ƙafar yallo da ƙarfi ta murjeta, wata ƙara ya saki tare da sakinta ya riƙe ƙafar sa, shikuma abokin yallo ta gartsa masa cizo ahannu take ya saketa, aikwa ta kwasa da gudu, suma suka rufa mata baya.

Gudu take iya ƙarfinta suma suna binta, duk abunnan daya faru tsuntsuwar nan tana hannunta.

Cikin sa'a tasamu ta ɓullo cikin gari, su yallo ganin ta shigo cikin mutane yasasu cizon yatsa suka koma, bata daina guduba har saida taganta a tsakar gidansu.

Haki kawai takeyi saboda gudun data sha, baffa ne yayi sauri tashi yazo inda take ya riƙe mata hannu. "Bilkisu maine ne yasameki haka? Ko wasune suka biyo ki?" wasu hawaye ne suka zubo mata afuska. "Baffa inna ce ta aikeni wancan jejin insamo mata itace, danaje harna ɗebo na tawo su yallo suka kamani shine nasamu na yadda icen nagudo." daga can bakin rariya inna Larai tace. "Shine kika tawo baki ɗakkomun icen ba? Uban mai zasuyi dake da har wani kike gudu, to wallahi yau kinga ta kanki tunda kika dawo babu icen maimakon ki tsaya sugama abunda sukeso ki ɗakko icen ki kawo mun shine kikaƙi ko? To kingamu da tawa kalar wahalar agida." baffa ko ƙala baiceba shiru kawai yayi, inna Larai ta nufi bakin murhu data kunna ɗazu dan ta dafa ruwa, bakin huta ta ɗakko guda ɗaya ta nufo Bilkisu bata tsaya komaiba ta ɗora mata ahannu, wata uwar ƙara ta saki saboda azaba.

Baffa ya rintse idonsa ƙwallah ta futo ya juya bayansa kawai.Cikin masifa inna Larai tace. "Wallahi kaɗan kika gani acikin gidannan indai bazaki yi abunda naceba to kuwa zakiyi gamo da abubuwa da yawa acikin gidannan." maida icen tayi murhu sannan ta shige cikin ɗakin ta.

Baffa yayi sauri yazo inda take, ya kama hannu ya riƙe yana hura mata da bakinsa, Sani ne ya shigo ɗauke da wata baƙar laida, da sauri ya ƙaraso inda yaga su baffa a zaune. "Baffa maiya sameta? Garin yaya ta ƙone?"


*Adadin comment adadin type🤷🏻‍♀*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now