page 41

175 16 2
                                    

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 41*

Su Lami sun dawo daga gun talla sun riske innar su azaune akan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yayinda bilkisu take ta fama da tuƙa tuwo duk da yafi ƙarfinta.

"Inna yau kuma waccan uwar kini bibin tabarmiki wannan yarinyar kina morarta kenan." Laure ce tafaɗi haka tana mai nunu da bilkisu, wata shewa inna Larai tayi ta tafa hannu. "Ai wannan ingaya muku yazama tsohon tarihi, zan baku labari anjima, yanzu wannan yarinyar da kuke gani ku ɗauketa tamkar ƴar aiki acikin gidannan ba ƴaba, duk wani abu naku ita ce zatayi kuma wannan makaran tar datake zuwa bazata ƙara zuwaba har abada, ku bara kuji daga yau kundaina zuwa tallan nono itace zata je tunda ubanta bayaso nikuma sai anyishi agidannan hhh." dukan su suka kwashe da shewar farin ciki suka shige ɗaki dukansu.

Da sannu da sannu har bilkisu tagama tuƙa tuwon ta rufe shi ya sirara, magana tajiyo daga waje kuma ba shakka yaya Musa ne, da sauri tayi wajen, aikwa shine a tsaye yana danna wayarsa. "Yaya Musa ina huni." cikin sakin fuska yace lafiya lau ya karatun ki." "Alhamdulillah yaya." "Yauwa Bilkisu ɗakko litafinki saimuyi karatu ko?" ɗan jimm tayi tukun tace. "Yaya Musa kodai zamu barshi zuwa gobe? Saboda yanzu inna ce ta sani girki." "Ayya karki damu kije kiyi aikin ki gobe mayi karatun." "To yaya na gode." da hanzari ta koma cikin gidan shikuma yabita da kallo saida yaga ta shige tukun ya girgiza kai tare dayin murmushi ya huce.

Da sanɗa ta koma cikin gidan, ta cigaba da aiki tana jiyo shewar su, tana gama girkin ta gyara gidan tayi wanke-wanke sannan taje ƙofar ɗakin inna Larai tace. "Inna nagama aikin duka." daga ɗakin inna Larai cikin ɗaga murya tace. "Dan ubanki shine zakizo kina damuna ko? To maza ki huce kije can ɗan jeji kiyomun karare dan daga yau nadaina asarar kuɗin itace maza jeki kiyomun da girkin safe." ɗan dummm tayi saboda tunda take abunda bata taɓa yowa ba kenan. "Dan ubanki saina futo na shaƙeki anan kin mutu na huta, wallahi inna zo na tarar dake anan gun baki tafiba saina illata ki." da sauri Bilkisu tayi waje.

A ɗakin inna Larai kuwa Samira ce tace. "Inna mai makon kibata wankina tayimun duk na haɗa wankifa sosai." "Ke barni ninasan abunda nakeyi, wanki kuma duk daran duniya saitayi muku shi ayau ɗinnan, abunda yasa na aiketa can saboda kinsan gun bashida kyau musamman ma da daddare sonake Allah yasa su Yallo su danne shigiya suyi mata fyaɗe inga ta tsiya." wata muguwar dariya suka kwashe da ita gaba ɗayanzu.

Baffa ne ya shigo da sallah marsa ko ƙofar ɗakin Ruƙayya bai kallah ba saɓanin dah da koba girkin tabane saiya kalli ɗakinta yayi murmushi, ɗakin inna Larai ya nufa,yana zuwa ya shiga duk suna zazzaune suna kallon sa amma babu wacce tace masa kida sannu da zuwa. "Yah yah ne bawan Allah kazo kawani tsaya mana akai kuwa dogarin mai gari." dubur burcewa yayi. "Larai dama dawowa nayi daga kasuwa shine nashigo." "To ina ruwana da wani kasuwar ka kodan yanzu babu R..." da sauri ta gimtse bakinta saka makon da tunowa da tayi da wani gargaɗin boka akan karta kuskura ta faɗi sunan tarinyar agaban wani indai tayi haka to akwai babbar matsala dazata tunkaro ta. "Malam maza huce kaje tsakar gida ai akwai tabarma saika zauna." baice ko ƙalaba ya fuce daga ɗakin su Lami kuwa in banda taɓe baki abu abunda sukeyi masa.

Bilkisu duk atsorace take gashi tasan anan su Yallo anan suke iskancin su su kama yarinya suyimata abunda sukeso suyi tafiyar su kuma ankasa yimusu komai saboda baban su masu kuɗine agari kuma abokan mai garin ne, a hankali take tsinto kararen da itacen bishiya tana haɗawa awani tsimma tana ɗaurewa, wata tsuntsuwa tagani mai mugun kyau akwance daga gani bata da lafiya kuma ƙafarta ma guda ɗaya tayi jah ta ɗan kumbura, da sauri taje inda take tasa hannu ta ɗauketa. "Wayyo Allah na ƴar tsuntsuwa ko wani mahar binne inaga ya harbeki kikaji ciwo, kai amma maharba sun iya mugunta bara inkaiki gida." itace ta ɗaure ta ɗora aka sannan ta riƙe tsuntsuwar ahanunta tayo hanyar gida.

*Tsuntsuwar waye? Wane abune yake tattare da wannan tsuntsuwar? Mai zai faru agaba, kaddai inna Larai ta amsheta ta gasa ƴar banza🤣🤣🤣*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now