1

1.1K 65 2
                                    

                          

loadιng...........✍🏻

    🌐

   *RUDIN DUNIYA!*

*NA KHAIRAT UP*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*PG 1*

Sanye take cikin hijab dogo fari ya sha guga, fuskar nan ba walwala a cikin ta da ka ganta kasan tana cikin damuwa da bacin rai a hankali ta dago kanta ta watsa masa harara da alama maganar da aka fada mata ce bata yi mats ba ko kuma bata yi da wanda ke mata maganar.

A hankali ta motsa bakin ta kaga malam ka saurare ni da kyau kaji ni ba ajin ka bace ba kuma ba tsarar soyayyah da kai ba, kada ka kuskura na kuma ganin ka a kofar gidan nan da zummar wai guna kazo kana jina ko?

Shiko da kallon mamaki yake binta ganin yarinyar dake fada masa magana bazata wuce sa'ar kanwar sa ta uku ba lallai *So ne silah* da bata isa tana masa irin wannan wulakancin ba ta zauna lafiya be sauke mata lafiyayyun marika ba a 'kuncin ta.

Mtsw mutane se tsaurin ido da kinibibi wai ni ze ce wai yazo guna zance to wallahi ahir dinka ko iskar data kwaso ka bata isa in shaqe ta ba shashasha,gara kawai ta fada tana juyawa cikin gidan su.

Abu biyu ya tarar masa a kwanyar sa mamaki da kuma ta'kaici lallai sena koya miki hankali ya juya cikin bacin rai ya bar kofar gidan.

Ganin ta shigo a fusace yasa umman ta dakatawa da tankaden da take yi ah'ah *me kyau*  ya na ganki kamar ranki a bace ina saurayin?.

_wai umma kamar ni tsamin saurayi saboda raini ze kalli cikin ido na yace wai ni yake so?_

Subahanllahi wai kina nufin talaka ne ya zo?

Eh man umma wallahi duk na muzanta kunyan masu wucewa ma na dinga ji duk girma na da darajata wai yazo yana min wasu surutan iska an fada masa ni kowane gara nake kulawa?

Kar ki bata ranki zan san mezan yi ai ke babbar yarinya ce wadda ya kamata dan babban gida me mota da jirgi ne zai na kula ki ba wai waddanan sakararrun mazan ba wayanda yar yanzu a tukunyar iyayen su suke cin abinci.

_wallahi umma wannan sam ba rayuwa kike koya ma *yaya saffiya* ba, da talaka da me kudi duk na Allah ne_

Wannan wannan ba dan a gida na haifeki ba se in ce a asibiti an min canjen ki marar san abun arxiki me bakin cikin daula.

_hmm umma ki kyale ta ai er bakin ciki na ce shi yasa ko a hanya in na ganta bana nunawa na santa, so take mun taso a cikin wahala cin tuwo miyar kubewa mu karashe sauran rayuwan mu a wahala to karya kike yi munafuka idanuwanta kaman kwan lantarki da anyi magana tace Allah yace annabi yace insha Allahu sena auri me mota ba wai me karamar mota ba me motoci da gidaje da shaguna da abben hutu ehe_

Bakin ta,ta tabe 😏 kunyi nisa Allah ya ganar daku.

Ummaj ya jefe ta da murfin tukunya tana zagin ta.

Tana sosa gun ta mike ta yi dakin su ni isllamiya ma zan tafi .

In kinje ki gaida malam .

Bata kuma cewa komai ba ta fice daga gidan.

Yayin da *saffiya* ta kishingid'a tana  mafarkin data saba gaya a makeken gida me bene da masu aiki birjik ana mata tausa, ga abun son ta dinning area baje baje da kulolin abinci ga kaji da soyauyan nama 😂 bata aikin komai sai na ci da kallo (mafarki dadi).

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now