57

449 29 3
                                    

RUDIN DUNIYA

KHAIRAT UP

PG 52

Vote@wattpad khairi_muhd.

Innallillahi wa inna illahir raju'un shi ne kawai abinda ke fita daga cikin bakunan su lallai dukan rai mamaci ne , yau kai ne gobe ba Kai ne ba, kana naka Allah na nashi ba Wanda yasan meze faru gobe, ka shuka alkhairi ka girbi alkhairi,ka shuka sharri ka girbe sharri ga me kyau dai duniyar ta rude ta yanzu kuma ta tafi ta bar duniyar gaba dayan ta kaico, ya kamata musan cewa duniyar nan ba matabata bace ba, mun zo ta kuma zamu barta, mu kama Allah kawai mu yi koyi da hakuri,juriya,da godewa Allah da abinda ya baka kada ka hangi na wani kace se shi kowa da kaddarar shi,kowa da jarabawar shi komai na gidan duniya rubutacce ne.

   Umma kam kuka take muhaseen ma kuka shi ko Baffan nasu sunayen Allah kawai yake kira zuciyar shi ta karye, na yafe miki saffiya Allah ya yafe miki, Allah ya jikan ki,Allah ya amshi tuban ki .

Ko Ak bata iya kira ba was he gari ne ma ta samu ta sanar masa ya jajanta sossai tare ma suka taho da daddy da hajiya harda auta , an yi mata sutura aka kaita gidan ta na gaskiya .

Koda Ak ya kebe da muhaseen rungumeta yayi yana lallashin ta da kalamai masu taushi da dadi, ya kuma roketa karta sa damuwa a rnta saboda lafiyarta da ta abinda yake cikin ta,sannsn ya mata nasiha ya kuma CE mata ta daina kuka addu'a zata yi mata.

Jsmcy kam ta sha kuka tasan cewa tayi rashin kawa Dan kuwa da zuciya days Sofie take zaune da ita amma ita saida ta cuce ta ga makomarta nan.

Ak yasa a binciko masa Alh.me dala saboda ya zama dole a hukunta shi Dan matsafi ne kodan a ceci wasu matan daga kaidin shi.

Abu kamar wasa saffiya tayi kwana bakwai a kasa, ba kwarkwasa,ba magana,ba gayu,ba kyan kai babu ita ma a cikin duniyar gaba daya saidai a tuna da ita ko kuma a kalli hotan ta.

Umma tayi kukan Abu daya kukan kuwa shi ne na Dora wa saffiya tarbiya ta daban gashi nan duniyan data Dora mata buri a kai ta tafi ta barta, tabbas uwa ta gari ita CE daidai Allah kasa mu dace.

   ✨✨✨✨

Ido da aka sa ma alh.me dala ya fara damun shi Dan gidan shi gaba daya an sa masa matakan tsaro, ta ko INA gardin shi ake yi.

Yaran shi ma yanzu basa San motsawa Dan gidan alh. ne meeting point to saboda yan'sanda an kasa yin meeting din.

Satin su biyu underground dake duk wayon ka kana da Wanda ya fika Alh.na kokarin guduwa har ya kai airport aka samu cafkarsa duk da yaso ya botsare musu,yaso yin amfani da sidabaru saidai ayoyin Allah sun fi nasa, a sume ma a ka wuce dashi station.

Bayan ya farfado ne ya ga en kungiyarsu su biyar jage jage alamun sun daku sun sha wuya sai zazzare idanuwan shi yake yi kamar na mayu yana muzurai.

Alh abokanan aikin ka sun fadi gaskiyar Ku sun fada man's Ku kuka kashe zainab,da saffiya da ma wasu mutanen da da ma saboda San zuciyar Ku da bukatun Ku  muna san kaima ka yi confessing.

   Ni fa ba Dan kungiyar asiri ba ne ba.

OK taurin kai zaka yi mana kennan?.

Ni Dan kasuwa ne ba matsafi ba kuma mata ta bani na kashe ta ba ni zainab din ma ban San ta ba saboda haka INA bukatar ku kyale ni INA da aikin yi.

OK muna san masu taurin kai ai irin Ku officer?

Yes sir!.

Officer , ku ladaftar dashi Ku samu flyer Ku cire min faratan shi, Ku bashi barkono yaci ya koshi Ku jajjaga masa lemon attarugu.

An gama sir.

Duk da cikin alj.ya kadu hakan Besa ya saduda ba ko ya nuna masu ya tsorata ba, sai ya kuma Kame bakin  shi ya tsuke ya gyaran zaman shi.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now