13

263 22 0
                                    

🌐*HIKIMAH WRITER'S ASSOCIATION*

🌐*RUDIN DUNIYA*

🌐*✍🏻 KHAIRAT UP*

🌐   *PG 13*

*Vote@wattpadkhairi_muhd*

*✍🏻 Loading.....*

     Ranar su muhaseen suka dau hanyan jos su ma.

    A hanyar su ta zuwa suka tsaya sallah, tsautsayi, muhaseen ta shiga gidan wata tsohuwa kamin ta fito motarsu ta tafi a tunanin su kowa ya dawo,tana fitowa yaga wayam, nan hankalin ta ya tashi ta dauko waysrta dan kiran kawarta amira salisu,sai ko wayar ta, ta sanar mata ai bata da ko kwabo a ciki bata san ma sanda hawaye ya zubo mata ba ta durkushe a kasa tana hawaye ina zata sa ksnta? Gashi yamma tayi sossai.

    Lokacin A.K zasu wuce drivern shi nuhu ya ce :-"yallabai ga wata a bakin hanya kaman tana cikin damuwa".

   Ok dauke ta amma kayi sauri kasan mun makara fa.

To yallabai.

   Daidai inda muhaseen ke zaune ya tsaya ya ce mata :-"baiwar Allah lafiya?"
    Cikin kuka tace "mun taho zamu school trip se kuma muka tsaya sallah kamin na fito sun tafi kuma ba kudi a wayata balle na kira su."

  Ayya muma jos din zamu je shigo muje kin ji?.

To nagode, gaba ta shiga ta zauna.

  A karo na biyu tace nagode bawan Allah.

Ya murmusa ai ba komai sedai  ki godewa yallabai.

A.k da tun shigowar ta yaji wani irin yar,muryar ta,ta saukar masa da kasala.

  Ta juyo ta ce masa :-"yallabai nagode Allah saka da alkhairi ya bada sa'a a abunda aka je nema".,

A tsanake yace amin!.

Dan Allah ko zaka ban aron wayar ka na kira team dina na sanar musu ina lafiya?.

Ohk ba komai me ze hana, nuhu ya bata wayar sa ta amsa tana godiya.

     A cikin mota kuwa seda suka yi nisa sossai amira ta farga ba muhaseen a mota,nan ta daga hankulan mutanen cikin motar ta ce mun baro Muhaseen.

Nan dr da ya taho dasu ya rude ya ce what?.

A ina?

Inda muka yi sallah tunda nan kadai muka tsaya.

Subahanallahi, kai driver mu juya mun bar student daya a can.

Suna kokarin juyawa wayar amira ta shiga kara, a rude ta daga da niyar cewa a kira anjima.

Salamu alaikum,
    Wa'alaikum salam,
Amira salisu Muhaseen ce.
  Muhaseen ! Kina ina? Se yanzu muka lura ba kya cikin motar mun ma juyo.
   No ku karasa zan same ku a camp muna a hanya na samu wasu bayin Allah sun dauko ni zasu kawo ni.

   Ba matsala Muhaseen?.
   Ba matsala insha Allah.
Shi kennan ki kula da kan ki.
Insha Allah.
Tam se kun zo.
Ahan nagode.

Sir,tace muje kawai ta samu lift zamu hadu a can.

Are you sure?,bana san daukan risk ku responsibility din mu ne bana san a samu mishkila.

   Ba komai insha Allah muje kawai she was sounding ok ko a muryar ta ma.

To Allah ya kiyaye gaba.

Amin.

  A.K yayi msmakin nutsuwar yarinyar dako face dinta be gani ba se muryar ta da yaji da nutsuwarta ga kamshin turarenta da ya cika su, hakan nan zuciysr shi tace ka kalle ta mana ta mudubi ka gan ta.

   Yaso yaki bin umarnin zuciyar sa sai kasawa yayi ya tsinci kansa da daga kansa ya kalli mudubin sedai aka samu akasi kanta na kasa tana danna wayarta.
   Siririn tsaki ya buga ya koma kan laptop din shi.

   Na ganta in zata sauka.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐

*KANO*

A KANO kuwa ana ta shirye2n kai amarya gidan ta.

Se kuka take yayin da Faridat ke mata dariya, kefa kika ce kina so kuma yanzu kukan me zak yi?,lokacij tafiya yayi a tafi a bar hajiya,da big bro gani daga nesa2,.
  
     Daka mata duka tayi ta cigaba da shasheka keda Allah kuma sena fadawa big bro in ya dawo.
    Ahyye ashe ba dadi kin manta sanda kika min lokacin biki na?.
    Ta galla mata harara tashi muje jare ana jiran ki za a miki nasiha lokacin fligh yayi yamma tayi sossai fa.

   Da kyar ta mike suka fita babban falon gidan ,nan tsofaffi da iyayye suka sata a tsakiya ana mata fada kowa seda ya mata nasiha sannan Faridat still ta raka ta dakin da hajiya da daddy suke a zsune aka kai auta, wohoho zo ku ga kuka da rawan jiki ta rungume hajiya tana kuka daddy na shafa kanta hajiya daurewa kawai tayi karta yi kuka a gaban Muhibat ta karaya.

     Daga karshe dai suka mata fada,suka mata nasiha sannan gwagwanin mijin suka amshi amarya.

     Mutum ashirin aka dauka sai airport dan zuwa gidan amarya.

Faridat da kawayen muhibat guda goma kuma A.K ne ya biya musu kudin zuwa dana dawowa.

Ni khairi nace Allah bada zaman lafiya.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐

Lafiya suka isa garin Jos , wayar dai shi suka yi da amira ta fada mata inda suka yi campiny , A.K ya ce su kaita.

  A sanda zata sauka ne ya gan ta, wani irin bugawa kirjin sa yayi da karfi yarinyr tay masa kwarjini sossai gata da sanyin hali ,.

Tsugunowa tayi jikin window tace nagode fa sossai ubangiji ya saka muku da alkhairi, ya biya ku.

Amin suka amsa.

A.K yaji dadin addu'ar sossai ya tsinci kansa da murmusawa.

Juyawa tayi ta tafi.

Suma suka ja motar su.

  Yallabai yarinyar nan ta na da kirki wallahi bata da rawar kai gentle ce.

Indeed ya fada a ransa a fili ko be tanka masa ba.

Shi dai nuhu yace da ma na karbi num ta dan ta min sanyin halin ta yayi yawa.

A bangaren Sopie kuwa yan gidan alhaji sun zo an gama magana aka tsaida biki wata shidda. Baffa yaso a kara suka nuna masa kar ya damu alhaji zeyi komai su kawo ta da abunda Allah ya hore musu shi yar su yake so ba kayan kyalkyalen duniya ba.

   Yaji dadi sossai kuma ya yaba da halin su na dattako duk da haka be hana a masa bincike akan alhaji ba.

   Cikin gida ya shiga ya bawa umma kudin da aka kawo dubu dari cif kudin na gani ina so da akwati guda biyu na sa rana.

Aifa kar kuso kuga murna a gun Umma har rawq ta yi ta dinga godewa ALLAH. Yarta tayi goshi har dubu dari ga akwatuna kaf dangin su ba wanda aka taba yiwa haka.

Yadda suka yi dasu ya fada mata.

Yo ai ba komai tunda zasu yi ai alhamdulilah, zamu yi amfani da wannan kudin wajan wasu hidimar bikin ko ya kace? .

Allah shige mana gaba.

Amin.

Har ya tafi ya dawo yace kuma ina ganin wani watan ma za a kawo kayan auran Muhaseen.

Muhaseen kuma?.

Eh Muhassen .

To waye?.

Zaki sani in lokaci yayi.

Ba ta wani damu ba tace to Allah kaimu.

Amin.

   To yanzu zamu fara

*Like*
*Share*
*comment*

    *sannu sannu bata hana zuwa se dai a dade ba a je ba.*

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now