46

229 20 0
                                    

RUDIN DUNIYA

KHAIRAT UP

PG42

Votes wattpad khairi_muhd.

   Wani irin wawan mari ya tare ta dasu har guda biyu dama da hagu,tayi luu kamar zata fadi ta samu tayi balancing kanta.

   Ni ka Mara?.

Zaki rama ne?.

Saboda kun ci amana ta ? Ak dama kai  maci amana ne? Ni zaku yaudara Ku ci mutunci na wallahi sai Allah ya saka min, Amina ba yardar da ban baki ba na janyo ki jikina kina er matsiyata duk abinda nake ciki kina sani, ina amfani da shawarwarin ki amma yau ni zaki...kuka yaci karfin ta a gun ta durkushe ta saki kuka me ban tausayi kun cuce ni AK Amina se kin ga karshen ki baze kyau ba.

Muhaseen tausayin ta ya Kama ta,gunta taje ta tsuguna hade da rungumota jikin ta tana lallashin ta bata hana ta ba Dan tasan tana bukatar kafadar da zata yi kukan a wannan lokacin, Muhaseen yarinyar nan munafuka CE kawata CE fa Aminiyata CE fa ba abinda bana mata ita da iyayen ta hatta fada mun sha yi da AK saboda ita ba shawarwarin da bata ban Ashe muguwa CE mijina take son aure wa to wallahi sena yi maganin ki Baku isa kuci amana ta ba Ku zauna lafiya.

Amina ko ta harde hannaye tana kallon su ta sha mur a ranta ko fal dadi AK ya mari Faridat. ”zaki San yar matsiyata se na yi maganin ki wallahi yanzu muka fara muje zuwa wasan zeyi dadi ni da ke shege ka fasa”.

Bara kuji na gaya muku dukkan ku ni ba sakaran namiji bane ba kar ma Ku sake kuce zaku maids min gida tamkar gidan kaji wallahi kowacce ta kama kanta bazan laminci iskanci ba kuna jina ko zaman lafiya kawai nake so,duk wadda taga bazata iya ba ta tafi gidan su mtsw.

Muhaseen bin shi tayi da kallo kawai tamkar Wanda aka canjs ya zama mafadaci tamkar ba Abdool din ta ba.

Sa kai yayi ya bar gidan.

Faridat na ganin haka ta mike ta nufi gurin ta zagaye kawai take yi ta gama sa wa a ranta saidai AK ya saketa amma seta lahanta Amina yau din nan ba gobe ba.

Muhaseen kam sopie CE ta kirata wai sun zo

Fits tayi ta shigo da ita, aikam sopie bakin ciki kamar ta mutu a gun dan gidan ya gama tafiya da ita bata zata kudin mijin muha ya kai irin haka ba ga bangariri da dams har kwallar bakin ciki ta fitar.

Falon muha kam abin kallo ne ga wani katon hoton su a jikin bangon tabbas muhaseen da AK sun yi kyau kuma sun dace da juna ga daula.

Yaya ina kwana?

Lafiya Lou kina lfya dai ko?.

Eh Alhamdulilahi.

To madallah dama nsce bara nazo na gan ki .

Aiko naji dadi.

Nan ta cika musu gaba da kayan makulashe ita da jamcy.

Jamcy kam kama baki tayi aljannar duniya wai muhaseen CE a nan? Tabdi yayan mal.habu sun fece wallahi.

Amma ba komai gwara ma su kashe kan su muma mu samu mu rabi arxiki.

Ke muhaseen haka ake yi ne?.

Meya faru?.

Ai kyace taso yaya muje kiga gida ko?.

Lah yaya ai so nake ku gama cin abun ko se muje yi hakuri Ku taso muje to.

To shi Kennan muje.

Lallai aljannar duniya dubi gida kamar baza a mutu ba, tabdi gaskiya muhaseen kina cikin daula dubi wasu irin kujeru da shuke shuke ga garden me sanyi, ga manyan freezers ga ma'aikata ga manyan motoci, tabdi lallsi muha Dole kiji kan ki a sama,ina ma ya kira ni, ina ma nice ya aura gashi kyayyawa Dan gayu dashi fes ba ruwan shi da raina mutane gaskiya saffiya kin yi sake gashi yanzu kin auri alhaji amma ba bayani mtsew.

Ta juyo lafiya yaya?.

Ba komai muhaseen muje naga dakin ki.

Tom muje to.

Tare suke hau sama dakuna kusan biyar ne a saman ko wanne da kayan daki na alfarma, an zuba masha Allah muhaseen kin ga duniya.

Murmushi kawai muhaseen tayi, ta haba dai ai nasu ne ni da nazo cin arxiki.

Uhm gaskiya muhaseen kina cikin daula.

Aa aunty jamcy ba wani daula kawai ina cikin farin ciki da mijina.

Haka ne!.

Dakin ki fa?.

Gashi nan mu Shiga ko?

Tare suka shiga numfashin su ne kawai be dauke ba Dan wani irin decoration aka yiwa dakin ga wani showglass me fitar da wani irin haske tamkar fitilu ga tursrukan wuta a ciki sannan dakin zagaye yake da hotunan su ita da AK Wanda suka yi a India da wands tayi ita kadai gaskiya sun yi kyau.

Kan gado suka zsuna suka dinga hira wajan karfe Biyar suka yi shirin Barin gidan seda suka fita daidai step race musu lah kuyi hakuri kuje zanyi fitsari ne.

To se kin sauko.

To.

Seda ta dauke wani tutare kudin shi zeyi 40k tasa a jaka ta dau pawder ta sa a jaka,sannan ta dauko garin maganin ta barbada a bakin kofar dakin.

A falo ta samesu seda suka Debi snack's a Leda suka tafi.

✨✨✨✨✨


Amma muhibbat kina da labarin Amina zata auri mijina kika kasa fada min?.

Hmm to ai an saukaka miki ne tunda kuna aminci ne ai gwara da ya sa Ku a guri daya kinga kwa huta da yawo.

Wato laifi na ne bana yayan ki ba?.

Kwarai kuwa ai kece kika ja Dan kowa yasan Amina Nada muhimmanci a gunki to me Dan kin bata fuska ta auri miji ki?.

Muhibbat ai Ak yaci amana ta.

Ko dai Amina taci amanar ki?

Kuka ta saki wallahi muhibbat nayi Dana sanin Amina a rayuwata kuma sena yi maganin ta wallahi..

Oho miki daga baya Kennan ai kin bar damar ki kuma kin bata wayon ki.

Kashe wayar tayi ta ji wani irin kuka yazo mata har ga Allah bata ki ta kashe Amina ba shedan kawai ingixata Yake yi da miyagun shawarwari tsam ta mike ta fita daga
Dakin ta tamkar wadda iska ke kada ta.

Bangaren Amina ta Shiga aiko Amina na falon kallo take yi ssboda haka hankalin ta na kan TV bata ji zuwan Faridat ba.

Kawai ji tayi tartsatin glass na tashi a haukace ta mike a tsorace tana Neman kofa tama rasa kofar,

Munafuka kallo kike ko? To ahir dinki kin yi karya kin yi kadan wallahi se kin gane kuren ki yau wallahi dani kike zancen er matsiyata wato ko a jikin ki? Kin auren miji kin hada shimfids dashi kina jindadi ko? To yau zaki ci ubanki sena lahanta ki wallahi In yaso a kama ni nima.

Seda Faridat ta tabbata ta FASA duk wani muhimin Abu a falon nan sannan ta kara da cafko wuyan Amina 😂 ta kai mata shaqa ta dinga gwara kanta da Gary bake me kwacen miji ba? To yau zan koya miki hankali.

Duksn ta take baji ba gani idanunta ya rufe Sega Amina na ihun Neman agaji.

Hehe au da baki shirya ba , baki shirya kwatsr kan ki ba kika auren miji he he to yau zaki gane kuren ki shegia butulu maci amana me mugun zama kika dinga ban gurguwar shawara Ashe so kike ki kashen auren to Allah ya fiki ina nan zama daram sede ke ki barshi.

Jin ihu yayi yawa yasa ma'aikata yin gun da gudu  duk sun tsorata da yadda suka ga amarya Amina 😂.

Muhaseen kam kiran AK tayi ta ce ya dawo gida akwai matsla a gidan nasu.

Key ya dauka kawai ya baro office din nasu ya dinga taka mota a haukace.

An kasa kwatar Amina a hanun Faridat Dan tsoranta ma suka ji su kam.

Tsayuwar mortar AK yayi daidai da faduwar Amina ta suma.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now