56

281 26 2
                                    

RUDIN DUNIYA

KHAIRAT UP

PG 51

Vote@wattpad khairi_muhd.

Muhaseen , na kasance mutum me San zuciya,me hassada,me San kai,me san duniya da abinda yake cikin ta na kyal kyale2, na kasance me son dukiya,na ki godewa Allah da abinda ya bani, na raina arxikin mahaifin mu ,burina na samu kudi na xamo babbar mace, na manta da cewa Allah shi ne me bayarwa, kuma shi ne me hanawa 😢, muhaseen wallahi nasan INA kaunarki saidai shedan ya rinjaye ni da kuma zugar kawaye , muhaseen na kai kaina Inda aka gama da rayuwata dubi jikina muhaseen ,dubi fuska ta muhaseen ni ce yau me kyau fuskata ta koma wata daban ta saki kuka dubi irin yadda na kasance wallahi muhaseen nasan hakkin ki ne yake kama ni saboda INA miki hassada da bakin ciki saboda kin fi ni kyau, ilimi,kowa ke yake so bani ba kuma na gano me yasa aka fi son ki saboda zuciyarki me kyau CE ba ki da mugunta ba ki da San duniya kin kasance me zurfin ilimin islama kuma baki da  burin samun duniya duk abinda kike dashi da shi kike amfani kawai bski da rainuwa ko hangen abun wani, amma ni nasan ba laifina bane ba hanyar da na bi  a rayuwata dorani akai aka yi ba kowa bane ya bata min zuciya ba illa ”MAHAIFIYAR MU” UMMA ita CE sila da sanadin halin da nake ciki a yanzu 😢, muhaseen me yasa ke baki bi hanyar da umman ta Dora ni ba a kai kullum maganar umma
      ”bana San talauci,na gaji da cin Abu daya,bans San talakan saurayi,ki kawo min me kudi,ki yi abinda kike so, ki daina kula tsamaye yara, ki samo babban kamu,ki samo babban alhaji,gida kato ,Me mota,me jirgi , me kayan alatu,Wanda ze sauya mana wannan rayuwar da Muke ciki, kanwar ki shashasha CE bats San me duniya take ciki ba se kana da shi a ke yi da kai in baka da shi da kai da babu daya kuke kina da kyau , kina da jiki me daukar hankali,😢 , hannun ta Muhaseen ta kamo ta hada da nata Muhaseen ki yafe min muhaseen Nima mutuwa zan yi.”

Aunty baki min komai ba wallahi in ma kin min na yafe miki ki daina kiran mutuwa cuts ba mutuwa bace ba ki yi shiru kin ji.

  Hmm Muhaseen nayi kokarin Raba ki da mijin ki Abdulkarim, ni na muku asiri ya rabu dake kina cikin halin bukatar kulawa ni sa ya aka sa mishi tsanar ki,da kin ki a kusa dashi ki yafe min nayi hakan ne saboda INA son Ak ni na fara sanin shi tun a  bikin kanwar shi muhibba har no muka yi exchanging be kira ni ba , saboda kudin shi nake son shi lokacin bikina na gan Ku tare ranan hauka ne kawai ban yi ba, sai dai a lokacin na sa a raina sena raba Ku baki cancanci ki kasance matar mutum me kudi da dukiya ba kamar AK , baki isa ki zama matar me kudi ba ni kadai nake da ikon zama matar me kudi sedai in San miki ki zamo baiwa ta 😢 ta sharce majina Ashe ban sani ba nice zan Shiga cikin musiba ba ban San cewa INA auren matsafi ba.

Innalllillahi wa INA illahir raju'un , aunty ”MATSAFI FA”?.

Ta kuma sakin kuka tace muhaseen MATSAFI Dan mafiya ne shi  ya kashe min kawa zee,ya ruguza rayuwar jamcy nima ga tawa tazo.

Umma ta saki kuka ta karasa kusa da su ta riko hannun me kyau ta dafa goshin ta , tana shafa Kanta a hankali Saffiya ki yafe min , Saffiya kaina na cuta na miki hudubar da ba ita CE daidai ba ,na lalata tarbiyar ki wadda mahaifinki ya Dora ki a kai na sa kin bijire masa, NASA miki kwadayi na sa miki San duniya na manta cewa Allah yana tare da mu yana sane da mu yana kallon mu kuma,na sa miki rashin San er uwar ki gashi ni da kai na na bata miki rayuwa , na kashe ki da kai na Saffiya Dan Allah ki samu wani GU a zuciyar ki Dan Allah ki yafe min nayi nadamar abunda na aikata sharrin shaidan da zuciya , na manta cewa abinda hakuri be bayar ba rashin sa ma bazai bayar ba, gashi yanzu min samu abun duniyar amma ba kwanciyar hankali 😢,wallahi duk ina kaunar Ku ki yafe min.

Um.ma ni na yafe miki Nima ki yafe min ki tayani da addu'a, .

Ina yi miki Saffiya, INA yi miki Allah ya yafe miki.

Amin umma.

Amin.

Muhaseen na rasa kyawu na.

Na rasa kafafuwana.

Na sha da kyar da rains har na samu na gana da iyayena da yan'uwa na , samu na nemi yafiyar Ku .

Aunty tayaya kika San matsafi ne?.

       ”muhaseen na dawo daga gidan su jamcy, ranan a gajiye nake ga ciwan kai dake damu na, na hau sama Ina kokatim shiga daki na idanuwa na suka hango min wani takalmi irin na mata sai na hasala raina ya baci nayi tunanin alhaji ne yazo min da wata cikin gidana sai na dauko takalmin na Kare mishi kallo sai na gano ai nasan takalmin nan amma na manta a INA na San takalmin, ganin wata kofa a rufe ya sa na nufi gurin na bude kofar , shigata keda wuya na soma dube2 dakin na da matukar duhu sai na nemi switch na kunna futular dakin amma sai me wani irin katon mudubi na hango an rufe shi da Jan kyalle gefe wasu irin kokuna ne manya cike da wani irin abu ni kuma da San kwa kwa na karasa na zare Jan kyallen nan mudubi na gani , na tsoma hannuna a cikin wannan kokon naji ruwa sena ji karni bayan na shinshina, sai naji ai wannan karnin na ”JINI NE”. Sai hankali na ya tashi na kuma juyawa sai na hango mayafin zee Wanda ta sa ranan da tazo gidan su jamcy har ma da Jakarta jikina ya soma kakkarwa na soma hasashen cewa a nan aka kashe zee Kennan?

Ihu na saki ban ma San nayi ihun ba sai dai me wani irin dariya na dinga ji me razanarwa da firgita me sauraron  shi wani irin fitsari naji yazo min ganin wata hallita me matukar tsoratarwa da muni ya bayyana a gaba na tsulum daga cikin wannan mudubin,

Fukar wannan abun a juye take ma'ana keyar shi CE a gaba , goshin kuma a ta baya, hannayen da kafafuwan na kallon gaba suma gashi jibgege kato na saki wani irin razananan Kara nayi waje da gudu INA Neman dauki, INA kiran ma'aikatan gidan Wanda basa ma  jina sai guguwa kawai nake gani da iska tana kadawa komai na gidan na gani yana yawo a sama yana juyawa, hatra su TV kujeru da sauran su.

Ganin Abu a jikina ya kuma firgita ni kafata ta yi missing step na fado daga saman bene,.

        Saffiya! Meya sa kika kai kan ki Inda na hanaki shiga said a kika shiga bana so kisan komai a kai na amma kin kai kan ki dole muyi maganin ki, saffiya INA San ki amma ba yadda zanyi kungiya ta gama amfani da ke tana bukatar jinin ki amfanin ki ya kare saboda haka ki  shirya zaki bakunci lahira kamar yadda muka amshi jinin kawar ki zainab muka kashe ta, muka lahanta rayuwar kawar ki jamila saboda tasan komai a kan mu kuma mune muka karya asirin da kika yi wa kanwar ki da mijin ta kema zaki bakunci lahira yanzu., sunan Allah na dinga kira na dinga yin addu'oi, ihu ta ko INA nake ji  karshe wani Abu me zafi aka zuba min a fuska Wanda a nan gun na suma. Ban kuma sanin Inda kai na yake ba. Koda na bude idona a gida na same ni a tsakiyan su Umma , kinji yadda na kasance ki yafe min muhaseen.

Na yafe miki aunty Allah ya baki lafiya . dama tafiya zamu yi to ni INA ganin fasawa zan yi aunty bazan iya tafiya in barki kina cikin wannan halin ba .

Hmm muhaseen kuje kinji ba komai kar ki da mu Dani ni tawa ta riga ta kare.

Aa aunty bazan bishi ba.

Nan suka zauna jigum  har baffa ya dawo suka kuma jajantawa juna.

A kullum shi yasa nake muku nasiha da Ku daina sa ido a kan abinda Baku dashi,Ku kasance masu godewa Allah da abinda ya Baku kar Ku raina arxkin ku, ita duniya ba ta auran rago, gashi nan kin fada tarko irin na RUDIN DUNIYA!   Kin rasa Kyan da kike takama da shi kin rasa kafafun naki kin rasa jikin  naki kin... Hawaye ya zubo masa na yafe miki Saffiya ya fits daga falon.

Koda AK ya dawo daukan muhaseen kuka ya tarar suna yi sai jikin shi  yayi sanyi ya tambayi Muhammad me ke faruwa ya fada masa komai, ba Karamin tashin hankali ya shiga ba, ya samu ya musu nasiha mai ratsa jiki ya kwantar musu da hankali nan ya bar muhaseen ta kwana.

Ways suka jima Suns yi ya dinga lallabata yana kwantar mata da hankali daga bisani suka yi sallama da juna suka kashe wayar.

Kusa da saffiya ta kwana   sun Dan taba hira koda barci ya dauketa adduo'i ta tofa mata suka kwanta.

       ”bazamu barki ba.
         Sai kin mutu.
         Jinin ki namu ne.
         Se kin mutu.
         Se kin Mutu.
         Ha!ha!ha!ha!.
         Se kin mutu.”

Wani irin kakari ta dinga yi ta soma aman jini , daga kan gado ta fado kasa tim jikin na kakarwa .

Muhaseen ta dinga kuka ta nufi hanyar kofa tana Kiran su Umma tana kuka nan suka shigo dakin a halin da suka ga saffiya said a suka tsorata dama ana mata barazana amma ba ta taba shan wuya ba irin na yau, sun kasa komai kamar an  rufe musu Baki suka kasa yin addu'a, Suna gani saffiya ta daina motsi.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now