51

309 25 4
                                    

RUDIN DUNIYA

KHAIRAT UP

PG 47

Vote@wattpad khairi_muhd

Juma'@t mufeedah to you oll. Ina yinku khairat Fan's irin over din nan.

Tsaki ta buga wadda bats San tayi ba ma ta kashe wayar ta ajiye karshe da ya dameta da kira switched off tayi gaba daya.

Hankalin AK ya tashi ya mimike ran sa ya soma masa suya gaba daya ya Shiga wani yanayi ya kuma kira a kashe daga karshe ya yanke hukuncin zuwa gidan su Muhaseen Dan ya tabbata tana can.

Kai tsaye gwamaja ya nufa ya Shiga Kennan Sega Muhammad nan ya masa iso zuwa cikin gida.

Umma barka da rana.

Barkan mu ya gidan ya iyali?.

Alhamdulilahi.

Yau Kaine tafe? Jiya mutuniyar taka nan ta wuni kai ma ysu wunin za kai? Ta fada cike da raha.

Dam gaban shi ya buga ma'ama muhaseen bats gidan su to INA taje?.

Innallillahi wa'inna illahir raju'un ya dinga maimaitawa a ranshi ko ruwsn be sha ba ya mike ya CE umma zan je na dawo.

To seka dawo? Ka gaishe su nan ys ajiye mata kudi  tayi2 ya dauke ya ki ya fice a wajen ma ya bawa Muhammad dubu uku da kyar ya amsa.

Gidan su yaje kuma tun zuwan shi hajiya tace muhaseen ta zauna a daki karta fito dan ta fada mata ya kirats dazu bats dauka ba.

Salamu alaikum
    Wa'alaikum salam ta amsa cike da fara'a tamkar ba abinda ya faru.
Hajiya barks da rana.
Barkan mu AK ya gida, ya matan naka? .

Suna lafiya.

To masha Allah .

.hajiya muhaseen tazo nan ne?.

Muhaseen kuma tace nan zato ne?.

Ya soma kame2 aa nayi tunani......

Kaga ban San shirme kaida ka barta zuwa unguwa baka San Inda ta nufa ba?.

Ya Sosa keyar shi hajiya wallahi ni ban San me yake damuna ba kuma ban San tana INA ba.

Ban gane ba? Fahimtar dani AK INA yarinyar mutane?.

Hajiya wallahi ban Sani ba hasalima ban San Inda take ba rabona da ita tun wattani shidda da suka wuce.

Ta katse shi da salati tana tafa hannaye Abdulkarim wattani dai dai hat guda shidda er mutane, amanar ka, matar ka ? To ksna jina ko? Maza2 kasan Inda dare ya maka ni ba ruwa na ka nemo musu yar su wallahi tun kan Daddynku yaji wannan zancen.

Hajiya naje gidan su yanzu ma daga can nake kuma sun fads min jiya taje ta wuni ni kuma bats gidana ko ta na nan hajiya?.

Harara ta zabga masa ta nuns mashi Dan yatsa ka fita daga idona kana ji na ko? Ka fitar min daga gida kar na kuma ganin ka seka nemo musu er su kaji ko?...

Hajiya amma...

Amman me ta daka masa tsawa matar taka zaka salwantat aksn me saboda kayi aure ka maids gidan ka gidan dambe gidan bala'i to wallahi tun kan rains ya baci ka nemo muhaseen wallahi ka nemo ta shashasha kawai tashi ka bani guri sokon banza bawan mata.

Yayi rau rau da idanuwan shi kiris yake jira ya fashe amma ya daure ya tashi ya CE se anjima hajiya ko kallon shi bats kara yi ba ta nuns masa kofa jikin shi a matukar sanyayye ys bar gidan.

Duk abinda suka yi muhaseen taji sai kuma taji tausayin shi kamar ta fito ta masa magana haka taji saidai tasan yanci da mutunci hajiya take Neman mata dole ta dauke kanta ta zama jajirtaciya ta kwato wa kanta da abinda yake cikin ta ysnci a gun mijin ta.

✨✨✨✨✨✨✨

Kullum tana hanyar gidan su jamcy dubiya kullum ne seta je saidai ba canji a jikin jamcy ko kadan saima Dada lalacewa da jikin nata yake yi.

Kullim da kuka take baro gidan su jamcy.

Ita ko jamcy kullum rokon Allah take ya bats bakin magana Dan ta kubutar da kawarta daga cikin makirci da sharrin alh.me dala.

Alamarin zee kuwa takanas ta shirya ta nufi gidan su jamcy Dan taji labarin bats jindadi a yadda ta ganta seda ta tsorata.

   ”subahannali, jamcy kece kika zama haka? Kece kika koma haka? Tabdi jam keko me kika aikata haka kika samo wannan sakomakon? Gaskiya na tausaya miki yanzu fa da kina da baki da kin maidan martani lallai duniya makaranta me ajujuwa da yawa yau kai ne gobe wanin ka to Allah ubangiji ya sauwake ya baki lafiya amin. To hajiyar dala se yaushe zaki tafi?.’

Cike da kufula tace se dare nake komawa ai.

Tab ba kya jin kyankyami da tsoro look at her fa.

Hmm zee Kennan ba komai lokaci ne kuma makaranta CE me ajujuwa da dams kamar yadda kika fada darasin ki na nan zuwa kowa da kaddarar shi kije kawai mungode da ziyara.

🤨 to sai anjima na duba ki jamcy sai wata rana.

Wannan Abu shi yasa jamcy kuka wato kowa ba Dan Allah yake zaune da kai ba sai dan duniya ita dai garin cutar aminiyarta ta gaskiya ta fada wannan sabuwar rayuwar me wahala amma dake da zuciya guda soppie ke zaune da Ita bata kyamace ta ba illa ma janta a jiki da take yi gaskiya amana tana da dadi.

Zee kuwa daga can gidan mekyau ta zarce dama taje hada kai da jamcy ne suzo gidan mekyau dan ta Barbada maganin asiri a gidan ne to sai kuma taga yanayin da jamcy ke  ciki kuma ga mekyau a gidan ma..
Koda me aikin mekyau tace mata bats nan cewa tayi ta sani kuma ita tace ma ta jirata dan sun yi waya yanzu..

Ba tare da shakku ba ko damuwa tace zauna ta ko zauna aka cika mata gaba da lemo da ruwa da snacks seda ta gama ci tayi nak tukuna ta mike ta hau sama ta soma aikinta.

Daidai wani daki tana kokarin zubawa ledar ta fadi ta tsuguna dauka sai taji an janye Leda tayi gaba , ha'a me haka? Ta kuma ynukurin dauka sai ta kuma yi gaba dakin nan ya bude Leda tayi ciki ta kama kugu cike da bakin ciki tana tsaki haka ta sa kafa ta Shiga daki ba tare da fargaba ba saidai me ? Tana Shiga aka buga kofa bammm ta kulle kanta da kanta ga daki bakikirin wani uban ihu ta kurma ganin wasu irin mutane marasa Kyan fasali idanunsu jajawur ba a ma ganin su sossai sai wannan Jan Idan hankalin ta ya tashi ta FASA ihu wayyo Allah jama'a a taimake ni ba kawo kaina gun da za a kashe ni wayyo Allah duhu a cikin duhun taji an ca.......

Muje zuwa

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now