3

388 31 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

    🌐

*RUDIN DUNIYA!*

*Na khairat up*

*pg 3*

Yau dai sofy an taki sa'a an yi babban kamu hakan nan ta shirya ta dau make up tayi zoo road bata san kowa a gun ba titin da ke jikin sahad shi ta bi manya manyan gidaje ta dinga gani tana marari hankalin ta ya tashi dan ita fa in zata ga gida kato to ka tafi da imanin ta.

Tana cikin tafiya ne wata mota ta nufo inda take da fari tai Mata horn ne taki tsayawa ta cigaba da takun ta dai cikin dai irin efixy din nan ita ga babbar yarinya,  shi kums ya nace mata da horn hakan yasa ta juya irin a fusacen nan an dameta 😂 nsn ko ranta fal dadi tamkar ana tsalle a cikin sa.

Glass ya zuge wani mutum ne a ciki dan baza a ce masa saurayi ba.

En mata ina zuwa?

Tana jin haushin fadar sunan unguwar su ba kadan ba ta ce a tsanake GWAMMAJA!.

OH shigo mana na kai ki

Ayi haka kuwa?

Eh ba komai ki shigo.

Ta bude ta shiga wani sanyi ne ya fara ratsa mata kwanya sai kamshi ta lumshe idanuwan ta.

Sunana na alhaji.usman dalla

Tayi wal da idanuwan ta jin inkiyarsa wai dala ai tuni ta saki wani irin fara'a ni kuma sunana sofy me kyau.

Ya murmusa gaskiya kin ci sunan ki ya dace dake kina da kyan sossai. sedai zaki iya kuls ni kuwa?ina da mata ta aure guda daya ya'yana biyar gidana a nan unguwar yake ni dan kasuwa ne ina yin canji ma sannan ban fiya zama a Nigeria ba sedai gaskiya bazan boye miki ba na gani ina so ki bani dama zan baki farin ciki na rayuwa.

Ranta fal dan murna tace nagode sedai ni din banda damar fara kula ka se baffan mu ya sanka.

Kar ki damu duk wannan ba damuwa bace ba zan je ai ni bana harkar yara saboda ni ba yaro bane ba.

Tayi hakan ne dan kar ya gudu ko yaga lagon ta ita me son  kudi ce.

Suna hira suka je gwammaja tana nuna masa sega sofy a dankareriyar mota yau an kawota har kofar gida kanta ya dinga wani fizga da dagawa.

A kofar gidan kuwa da muhaseen kawanr ta da saurayin ta ahmad suna zance suka ga mota ta tsaya fyallelilyar mota me numfashi sega kuma sofy ta fito daga cikin motar kai kawai muhaseen ta gyada tana msmakin hali irin na sofy.

Sofy ko bata rai tayi tamkar bata ma san muhaseen ba dake tsugune ba ta ce alhaji nagode kwarai da gaske se yaushe?

Se munyi waya kennan? Ki ban num ki na ma manta ban karba ba.

Tay fuskan tausayi alhaji jiya jiyan nan aka sace min wayata banda waya dama ina sa sena sami hali zan je na siyo wata.

Asha asha hakan bazai yuwu ba kina tare dani motar ya koma ya fito ya mika mata wata waya iphone 7 sabuwa kal da ita akwai sim dina a ciki zan kira ki daga baya zan taho miki da naki sim din.

😄 kai amma nagode sossai Allah kara budi.

Amin nagode fa da wannan addu'ar.

Seda taga tafiyar sa tukun ta kalli muhaseen kinga irin wayanda ake so masu harkar girma da sanin girma kin nacewa me saida kayan shago mtsw haka zaki kare a talalauci kina yawo da talakawa tsamaye.

Muhaseen dai ranta ya gama baci shiko ahmad kai kawai ya jijiga dan inda sabo ys saba da tijarar sofy da umman su.

Zatayi magana yace kar kice komai kinji ni ba komai wallahi.

Nagode ahmad!.

Da ihu ta shiga wayy umms fito ki taya ni murna yau mun yi babban ksmu wallshi hannun sa a bude yake wallahi umma yau kam kwalliya ta biya kudin sabulu.

Yaya? yaya? Meya faru?

Abin arxiki man umma nan ta fada Mata komai ai tare suka yi shewa hade da soma rawa suna nuna jindadin su.

Baffah dake cikin uwar d'aka yayi gyaran murya suka nutsu suka koma daya dakin.

Ke er'nan ya sunan sa kika ce da aikin sa?

Alhaji usman ke dallah kuma dan kasuwa ne yana yin canji ma yace a kasashen waje yake harkallolin sa.

Ki saki jiki ki mori arxiki kinji ko?ni dama nasan ke din matar manya ce.

Bari inje gidan su jamcy in bata labari

Sokuwa dawo nan  mesa ke baki da wayo?  Wannan sirrin ki ne basai taji ba baki san akwai kawaye masu snatching ba? To ko da wasa kar ki fada mata

To umma na gane



lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now