8

308 23 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

    🌐 *RUDIN DUNIYA*

*✍🏻 KHAIRAT UP*

            *Pg 8*

*Vote@wattpadkhairi_muhd*

Kalar farin ciki da murna da Saffiya ta kasance ranar Allah ne kadai yasan shi, dan bacci ma gagararta yayi.Sake sake take a ranta cewa "dole na auri alhaji me dalla ,dan na tabbata in na kasance matar sa na gama morewa a rayuwata gaskiya sopie me kyau kin gama morewa a rayuwa wallahi kakar ki ta yanke sa'ka." 

Muhaseen ta katse mata tunanin da take yi, "ya Soffiya ina son magana da ke."

Ta yamutsa fuskarta hade ds juyowa a dan fusace "ina jin ki meye?".

Ya Saffiya ko kin san abun da kike yi ba daidai bane sam?.

Kanbuu Muhaseen ni zaki nunawa hanya?.

Ai dan na nuna miki hanya ba laifi bane kuma dole ne na fad'a miki gaskiya a matsayina na kanwar ki me san cigaban ki a rayuwa,  me san farin cikin ki......

Dakata mun shashasha wallahi na jima da sanin cewa ke din yar bakin ciki na ce, ba kya farin ciki da cigaba na, makiyata ce ke na dade da sanin hakan amma ban san kin kai intiha ba a kan farin cikina, to kina jina ko? daga yau se yau kar ki kuma sa min baki a al'umarn rayuwata ko me zan yi kuwa kinji ni ko "ta fada tana jan kunnen ta 👂🏻.

Allah ya baki hakuri insha Allah zan kasance me duke ido a kan sha'anin ki wannan ma kuskure ne , ina me baki hakuri!.

Mtsw, ke se kace ba kanwata ba? Kiyi ta min hassada saboda kinga zan je makka,zan yi aure na zauna a gidan daula, na mallaki mota to ahir din ki wallahi in ma ke mayya ce sedai ki ci kan ki ke kadai ehe a daina shiga al'amuran rayuwata.

Mikewa Muhaseen tayi ta fice daga dakin tana dana sanin yi wa saffiya magana "nima banda zuciya ,amma in Allah ya so ya yarda bazan kuma tanka mata ba".

*ASALIN SU*

Malam Abubakar muhammad dan asalin garin kano ne an haife shi cikin unguwar gwammaja,mahaifin sa ma'keri ne,ba wasu masu hali ne ba saidai rufin asirin Allah yaran sa biyu rak da abubakar da kuma kanwar sa saudat wadda take aure a unguwar kurna iyayen su sun rasu a halin yanzu sai su biyu.

Mal.Abubakar ya gaji sana'ar mahaifin sa duk da ita Ce sana'ar gidan su duk suna zaune ne a unguwar ta gwammaja. Abubakar mutum ne me hakuri, juriya,da dauke kai a kan abunda ba nasa ba,yana da ilimin islama yayi boko sedai a matakin sakandiri ya tsaya saboda rashin kudin da ze je jami'a.

Shekarun shi ashirin da shidda wan baban (cousin brother din baban shi kennan) shi ya aura masa yar sa Suwaiba.

Suwaiba kowa yasan halin ta na son kudi,da son rayuwar hutu, auran ma dan ba yadda zata yi ne aka daura shi aka kaita gidan da Abubakar ya gada me dakuna uku da bandaki daya da tsakar gida se dan kitchen madaidici. Burin ta shi ne ace yau ta auri me kudi,sananne,gawurtace,an kaita katon gida me hawa hawa😂 , G.R.A se aka kawo ta lungu ranar da aka kaita kuka kam ta sha shi na bakin ciki bana rabuwa da iyayen ta ba.

Da ta samu ciki adduar ta Allah sa ta haifi ya mace dan ta cika mata buri na zama me kudi ta hanyar auren hamshakin me kudi na kece raini dan ta nunawa dangi da kawaye cewa ita din fa ta musu zarra. Allah cikin ikon sa ko ta haifi ya mace Saffiya wadda tun tana karama ta sa mata laqabin (Mekyau). Shekarunta biyar ta kuma haifo wata macen aka sa mata Aisha (muhaseen) shekara uku ta bawa dan autan su Muhammad sani suna ce masa (me babban suna).

Akwai banbanci tsakanin Mekyau da Muhaseen ko ta hallaya dan duk wata huduba ta mahaifiyar su Mekyau ta adana shi a memory din ta, bata ganin kowa da gashi ga rashin kunya da kyar ma ta sauke al'qurani me girma boko kam daga ss ta dakata tun da ta fadi a jamb.

Mekyau fara ce,doguwa,tana da manyan idanuwa, tana da gashi fuskarta dai is okey saidai bata da shape a tsaye take. Tana da fada, ga raini saurayi ko in ba me kudi ba wanke shi take tas ita se me mota. Saidai tana shakkar mahaifinta sossai.

Ita ko Muhaseen tsaf mahaifinta ta dauko da hallsyen sa na dattako da ibada, hakuri, ga sanyi, ita ba fara bace kuma ba baka ba ,gashin ta me cika ne da tsayi, idanuwan ta masu kyau ne ga girma, bakin ta dan karami ne,tana da diri tama fi Saffiya kyau sedai anfi ganin kyan  Mekyau saboda fara ce.Amma Muhaseen tafi ta komai,kyau,ilimi,san mutane, girama na gaba da ita abun duniya baya gaban ta.

Hakan yasa Muhaseen bata shiri da mahaifiyarta ksmar yadda mahaifiyar ke san saffiya, dan ita saffiya tana kawo mata abun duniya duk da bata san ya take samun su ba.Wani lokacin kawarta ke samo musu cikakkar er duniya ce ita, in ta samo seta ara wa sopie bashi ita kuma in tayi kamu ta biya ta biyun abunda ta ara a gunta. Gasu da shishigewa yayan manya duk wani biki na gani na fada in za ayi suna gun hatta anko da gate pas se sun samo ,hatta motar da zasu gun biki gangariya suke nemowa duk wanda ya ganta da sutturu da kayan kwalliya yace er manya ce.Duk abun ta bata yarda ta bawa namiji kanta ba saboda mahaifiyarya ta karanta mata muhimmancin budurci da mutuncin 'ya mace, kawai dai ita lashe money ce.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐

Wayarta da alhajinta ya bata ta dauko ta hau online, garin dube_duben ta  ko ta hango wani hoto wanda ya dau hankalin ta sossai a fili ta furta "akwai class a nan gun, da alama akwai naira bara na dan latsa na gani ko zeyi accepting."

Friend reauest ta tura wa me hoton sedai data shiga profile din seta ga,:-

Married,bussiness man,bla bla bla, "Wow" shi ne abunda ta fada ,aikam "dole nayi wasa da hankalin guy din nan nasan zan tatsi cash a nan gun 😂 ,seta tsinci kanta da yin addu'ar Allah sa ya amshi request din ta dan tasan cewa zata ruda shi da kyanta.

*Let's play the game MR.ABDULKARIM YUSUF LAMIDO (A.K)*.

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now