35

251 22 0
                                    

🌐 *Hikima Writer's Association.*

🌐 *Khairat Up*

🌐 *Rudin Duniya*

🌐  *Loading*

🌐 *Pg 32*

    *Vote@wattpadkhairi_muhd.*

     Saffiya sanye cikin doguwar rigar nan da ake yayi me suna kimono, ta sha nadi da wani dan mayafi.

Fuskar nan ta sha make up, da alama unguwa zata je.

Saukowa take daga bene tana yatsina kamar wadda aka zubawa kashi ko ruwan gutter.

A falo ta tarar da umman ta su tana cin abinci .

Gefen Umman ta zauna ta ce da ita.
     "Ina kwana Umma?".
"Ina gajiya Mekyau kin tashi lafiya?."
"Alhamdulilahi Umma ya kike?"
"Gani garas, kin yi karin naki ne naga kaman zaki fita ne ina zaki je?."
  "Uhm,wallahi booking zamu je ni da jamcy da zee na gyaran jiki."
   "Ikon Allah dama ke zaki yi da kan" ki?.
  "Eh Umma na samu labarin wata er saudi ta iya sossai da sossai idan."

"Hmm! Allah ya sauwake miki ke kam, to kije ki karya."

"Umma me kika dafa?"

"Doya ce muka soya da kwai ga ruwan shayi nan ki hada ki sha kici ki tafi."

To.

Umma ina ne unguwar su Muhaseen?.

Ke ni sunan wuya yake min sedai in tambayar miki ita.

Umma kennan ki tambayan min da kuma sunan mijin ta zan kai musu ziyara in sun dawo kar aje ayi abin kunya  a hanya mijin kanwata ya wuce na wuce ba a san juna ba.

Mekyau anya kuwa ba bu abin da ki ke shiryawa? Any.....

Kai Umma ke mesa kike yin haka ne wai dan Allah ta juya tayi waje abinta.

Uhm iko se rabbani kaji ni da yarinya yaya za ayi bazan damu ba bayan nasan ba san yarinyar nan kike da alkhairi ba nan kika ce se kin ruguza mata rayuwa yau kuma ki dawo kice kina yi da ita? Ai abin akwai ayar tambaya,to koma dai meye Allah ya fiki Muhaseen kuma ba dai malam ko boka ba dan ko tana tare da ayoyin Allah.

Duk kwane2n ki Umma sena cimma buri na, komai kareta da zaki yi, wallahi sena ga bayan Muhaseen tunda tayi gasa dani, taje inda zani ta yi gogaya dani nima sena koya mata darasin rayuwa.

BAYAN KWANA 2!

Anyi aiki alhamdulilahi komai yayi kyau jiki yayi sauki sedai baya wani magana sedai yayi musu yake.

Faridat duk ta damu dan kuwa ta gama gane cewa tabbas AK  ba karamin so yake ma Muhaseen ba dan clearly yake showing a fuskan shi.

Daddy ya ce "my son kaji sauki ko?."

Daddy ba komai ni na yarda da kaddara amma Daddy she is a gem,nayi rashi sedai ko yau auren ta ya mutu sena aureta sedai in bata fito ba.

Subahanallahi! Son ka daina fadar haka ba kyau Allah ya musanya maka da wadda ta fita.

Hmm Daddy kennan ai Muhaseen ta daban ce,babu irin ta a guri na kuma baza ayi ba,am damn sure about that.

Faridat ranta in da za a buda gobara ake a ciki,gaba daya ta fita hayyacinta kuka ke san kwace mata amma ta danne sedai idanunta sun ciciko da kwalla sosai wai ita da suka debe shekaru hudu da wani abin da AK be taba nuna mata irin wannan attention din ba ko kulawa se a rana tsaka wata banza ta same shi a arha, wallahi sena dau mataki bazai yuwu ba sam bazan yarda ba.

Number Amina ta kuma kira amma amsar daya ce a kashe take bata ma san sanda ta saki wata iriyar tsuka ba, gaba daya suka zubo mata idanu, dan kame kame ta fara erm dama kawai..

You dnt need to justfy is ok inji AK.

Tashi tayi tace "am sorry", sannan ta fita waje.

Zaka zo hannu ne,zan koya ma hankali seka dawo kana min kuka akan in soka ai akwai matakai na neman abinda ake so da yawa zan yi following din wannan dan na kwato ka a lokacin zan koyawa kowanne munafuki hankali masu nan nan da Muhaseen in yaso inga ta tsiya ,mtsw mutane se kinibibin tsiya yan yan yan shi kadai suka iya mtsw sakararru kawai.

   RUDIN DUNIYADonde viven las historias. Descúbrelo ahora