2

437 30 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

    🌐


*RUDIN DUNIYA!*

✍🏻 *khairat up*

*pg 2*

Kawata ki san yadda zaki yi ki samo kudin ankon nan ni kuma zan san duk yadda zan yi na samo miki gate pass.

Allah kawata kice abun ba sauki?

Eh ! Man ke ai harkar da d'a'a nake fad'a miki bikin manyan mutane ne sati za ayi ana shagalin bikin fa.

👀  ke jamcy da gaske bikin mutum guda sati?

Sossai na su masu kudin nan an fada miki su din wasa ne? Basa jin kashe kudi wallahi nake fada miki kuma manyan masu kudi zasu hallarcu bikin nan ki dai daure ki samo kudin.

Oh ni sofy ina zan ga dubu hamsin?

Jamcy ta bushe da dariya kar ki bada mata mana, ina samarin naki ? Duk wannan kyan naki me kike so ya zama na banza?

  🤨 kinsan bana kula tsamayen unguwan nan sam sam sabida abin kunya ne ma a ga ina kula yaran unguwar nan ,amma ke kin samu kudin ne?

Ni din wasa ce na samo su harda kari ma ta fada tana bushewa da dariya 😄.

Fada min tayaya kika samo?

Ko na fada miki bazaki iya ba so kawai ki bar maganar nan.

Jamcy to ki ara min

Ki biyani when?

Nasan dole zan yi kamu a gun dinner din bikin zan biyaki

Shi kennan zan siyo miki da less din da atampar da kuma material din kedai ki rike alkawari zaki biyani.

Haba kar kiji d'ar kema kinsan zan biyaki nida ke ai mutu ka raba.

Suka tafa hade da shewa.

Wai ke fada min ya kike da amaryar ne?

Wallahi nima ban san ta ba kawai dai a makarantsr mu naji coursemates dina suna maganan bikin to haka dai na cusa kaina a gun er'uwar amaryar muka zama kawaye har ta gayyace ni bikin ta kuma ban labarin irin kudi da girman bidirin da za ayi.

Shegiya ina yin ki kawas

Ai mu duk in da harkar hutu take muna gurin wallahi.

Suka kuma tafawa hade da yin shewa.

Umman ta leqo tace ta samu kennan?

Wallahi umma wani bidiri ne ya kunno kai ba a magana wallahi harkar da d'a a akwai fita a cikin ta da yardar Allah sena yi babba kamu a harkar kedai ki taya mu da addu'a.

Ta ko washe hakornya to Allsh ya taimaka yasa ayi nasara a sami mani suruki me budaddan aljihu.

Amin umma amin

Ta koma kan aikin da take dan sofy me kysu bata aikin komai saboda karta zama wata iri ko tayi baki jikinta besan wahala ba balle wani aiki tamkar wata yar sarki haka take a gidan duk wani ayki umman ta gwamace tayi amma me kyau ta huta.

Se yamma jamcy ta tafi gidsn su while sofy aka soma tunanin irin adon da za ayi a bikin dorin dosanon da zasu

🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Cikin wata dakakkiyar shadda koffe ya shigo falon wanda ya sha ado da kujeru seti biyu da yake katon palo ne setin farko ash ne da purple hatta carpet din gun dayan kuma light blue ne komai na gun.

Wata hamshakiyar mata na gani sanye da tsadaddan less ta sha gwalagwalai a wuyan ta da kuma kunnuwanta da hannayen ta.

Yana karasawa rungume ta yayi ta baya yana cewa mum sannu da gida.

Son saukar yaushe?

Dazun nan bikin lil sis ace nazo late ai ba daidai bane ba

Haka ne  son ya hanya kuma?

Hanya alhamdulilahi, sedai kewar ku data addabe ni ga matsin big bro a gun aiki abun ba sauki wallahi mum.

To ai haka ake so ya hanaka sukuni da zaman banza.

Ai mum ke ce kike daure masa duk ya bi ya takura mutane yay ta harhade rai yana cicin magani kamar baya son mu'amala da mutane.

Iye haka kace? Tamkar a kunnen sa wlh

Ya kama kunnen sa tuba nake mum a min afuwa badan hali na ba.

Matsoraci.


Ina amaryar take ne?

Uhn auta ai ba sukuni tana can suna tsare tsaren su basa zama sai hidima.

Toa se dare zan ganta Kennan.

Wallahi kam

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now