20

260 29 0
                                    

🌐 *Hikimah Writer's Association.*

🌐✍🏻 *Khairat up*

🌐 *Rudin Duniya*

🌐 *Loading......*

🌐 *Pg 20*

*vote @wattpadkhairi_muhd*

Kin ji ni da kyau *Ina Son ki*

Bawan Allah hakan nan,ban san ka ba baka san ni ba....

Kar ki damu zaki san ni ai ba damuwa bace ba ki fada min me kike son sani a tare dani?.

   Ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin karfin hali irin nasa.

Kinga kar ki shiga damuwa dan ina son ki ba yana nufin ki daga hankalin ki ba ne ba.

Ba damuwa nayi ba kawai ina mamakin karfin halin ka ne,.

Hh,yan mata kennan kiyi kokari ki bani lokacin ki, ki bani dama dan na nuna miki irin son da nake miki,wallahi lokaci daya son ki ya shige ni, kinga fada min sunan ki .

Muhaseen shiru tayi
Kawai tana ganin ikon Allah.

Dan Allah ki fada min.

MUHASEEN ABUBAKAR suna na.

Masha Allah gaskiya sunan ya dace da ke dan kuwa ke din me kyau ce.

Hmm nagode.

Ni bazaki tambayi nawa sunan ba?.

To fada min ai ba sena tambaya ba.

Uhm!abun naki son kai ko ince kina so ki min kora da hali,to bara kiji ni bazan kyale ki ba ,koda kuwa kullum zaki zane ni.

Murmushi tayi wai na zane ka kato da kai ta ina zan iya zane ka?

Dadi yaji yadda ta dan ware yanzu.

Zaki iya mana ai ke din gimbiyar mata ce.

Uhm ka fiya zolaya.

Baki yarda ba?.

Nidai ina aiki ne zan koma.

Kai dan ALLAH ya fada a shagwabe kamar wani yaro,gaskiya ni ban gaji da jin muryar ki ba Allah kua.

Dariya ya bata kuma ta dinga yin ta ranta sak.

Shiru yayi shi kuma jin dariyar ta ta seta burge shi.

Gaskya kana da abin dariya to fada min sunan ka.

Ni suna na ABDULKARIM YUSUF LAMIDO amma ana ce min AK,kuma ni bussiness man ne,ina zaune a cairo nakan zo nigeria ganin iyayena,ko wasu harkokin kasuwanci,ina da mata guda daya shekarar mu hudu da aure,ina da kanne biyu Ayman da Muhibbat,kanwata anyi bikin ta last week, Ayman kuma yana can cairo to kuma a halin yanzu AK ya gani ya na so ko za a bashi dama dan ya dama?.

Murmushi tayi tana son mutum straight foword,ba murdadde ba ji yanda ya bata labarin shi kai tsaye ba boys boye.

Kin yi shiru ko ba kya sona?.

Naji labarin ka amma kai baka san ni wace ba.

Nace miki sanin ki ba abu ne me wuya ba indai zamu saba to zamu san juna a hankali2.

   To ai ni ban ce maka ina son ka ba.

Kuma baki ce min ba kya sona ba kinga kuwa ina da hope!.

Wayon ka yayi yawa to ni dai ba er kowa bace,er talaka ce talakan ma tukuf ,wani lokacin ma sau daya meke ci a rana,makarantar ma baffa na dani muke biyan kudin reg in ya taso ina dinki jefi2,ina da ya da kani,muna zaune a unguwar gwammaja, to kaji labari na.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now