54

318 25 0
                                    

RUDIN DUNIYA

KHAIRAT UP

PG48

Vote@wattpad khairi_muhd

Sossai aka dukufa yi ma jamcy magani ta hanyar yin addu'oi da kuma bata rubutu tana sha ga saukar qurani da ake mata kullum , kuma Alhamdulilahi komai na samin canji Dan kuwa ta na kokarin yin magana sedai ba a fahimtar me take cewa amma sossai sunji dadin canjin da take fuskanta.

Ak kuwa bayan ya dawo daga office din su ya kira matan shi a ways su same shi a falon shi.

Kowacce ta fito tana kwarkwasa taci ado ana zuba kamshi.

Zama suka yi hade da gaida shi.

Kallon su kawai yake irin na gama da babin Ku tsaki yayi a zahiri Wanda yasa kowacce ta sha jinin jikin ta suka saisaita kan su Dan sun San Ak ba dai fada ba kila ma a waje aka bata mishi yazo ze sauke musu ruwan bala'i a kan su sai suka Shiga taitayin su harda gyara zama aka nutsu 😂.

Seda yayi gyaran murya tukuna, ya Kare musu kallo sannan ya soma magana.

” dukkan Ku ,kun ban mamaki kuma kun bata min rai sai dai Allah ya sani bani da hakkin ko wacce daga cikin Ku, kuma ina kokarin ganin na sauke hakokin Ku da ke kaina. Ban taba zama daku da zuciya biyu ba kuma ina hakuri da ko waccen ku saidai am sorry to say lada ya isa haka ku fara hada yanakuyanaku ku bar min gidana dan na gama zama daku na sake ku ....”

Ak kasan me kake fadi kuwa? K...

Ke kada ki kuma kiran sunana da kazamin bakin ki wallahi bana son ganin Ku ko na sakwan daya ne wallahi na tsane Ku na tsane Ku na tsane Ku ya fada ya kuma nanatawa cike dabl Bacin rai kuma iya gaskiyar shi yake fada Wanda abinda ke ran shi ne.

Amina ta soma kukan makirci Ak Idan laifi Muka maka ka gaya mana mu gyara wallahi ina son ka in ma fada ne mun daina.

Shiru kin fi ban haushi a kan kowa dama a kaina kike kokarin kashe mutane? Kika saida mutuncin ki, kike shirka to Ni na yafe muku kuje Dan kan Ku na sake Ku bazan kuma zaunawa daku ba.

Jikinta yay sanyi ta kasa cewa komai.

Ita ko faridat cewa tayi ni kuma me na ma?.

Hmm kin sani ai  faridat wai kema so kike kiga bayana Dan cikin matata da matata kike San  a hallaka harda ma ita kawartaki to kiji Ni da kyau badan aikin asiri ba wallahi Amina kawarki bata isa na aureta ba bata isa na hada jiki da ita ba kin fi kowa sanin bana kaunarta Ashe asiri ta min na aureta wallahi faridat kin ban mamaki Ashe xaki iya kisan kai?.

Kuka ta saka wallahi Ak ina kaunar ka kuma kishin ka ne yasa na yanke hukuncin kashe su har ita maci amanar kawar tawa wallahi Ak ina ba kin cikin ban haihu da kai ba yanzu duk kuma Amina CE ta saka Ni ta zugani in na yards na haihu zaka min kishiya, Ashe so take ta aureka na zubda ciki yafi a kirga karshe ma juye mahaifar nayi amma karshena shi ne saki a gun ka Ak ka tausaya min ka yi min rai na zauna a inuwarka.

Kan shi yaji ya Sara masa ya zubda hawayen ba kin ciki faridat Ni ba kya sons da kina sona da baki zubda cikina ba ai in kana San mutum hada zuri'a kake dashi Ashe... Kuka ya kwace masa.

Ak pls....

Shut up ya fada a tsawace kamar ze maketa kije faridat keda Allah na barki da Allah insha Allah ze Saka min mesa kuka shiga cikin mutane masu San duniya gashi duniya ta rude Ku kun aikata Sabon Allah gaskiya ne kawa musiba CE a rayuwa duk kawar da take baka munanan shawara ka guje ta gashi ta cuce ki ta cuce ni ta kuma aure miki ni kuma ta yi sanadin Barin ki gidan mijin ki😢 Faridat ki kiyayi haduwar ki da Allah kije duniya ce.

Amina abinda kika yi kije Allah ze saka min hakkina bazai barki ba Ku tashi Ku  tafi dukkan ku bana San ganin Ku ko da na Minti daya ne.

Mikewa yayi ya bar musu gun.

Kuka suka sa a tare faridat tayi nadamar hada kwance da Amina Dan tana mugun San Ak gashi Tasa tayi ba wan ba kanin ba Ak ba d'a bare 'ya ta kalli Amina cikin takaici da kuka tace da ita ” Allah ya isa tsakani na dake nayi nadamar haduwata da ke a rayuwa ta kin cuce ni kin zalince ni kin yaudare ni kin ci amanata na yards da ke me na miki kika rabani da mijina kika sa na lalata mahaifata wallahi Amina ke anamimiya CE muguwa CE se ubangiji ya mana hisabi nida ke I hate the first day I met u in my life 😢, wayyo ni faridat naga ta kaina na rudi kaina Wanda nayi domin shi ya guje ni wayyo Allah na Ak ina son ka ina son ka ina son ka pls kar ka rabu dani ”.

Hmm ko a haka na barki faridat na gama da rayuwarki naji dadi kuma na rama ke in kin manta wulakancin da kika min ni ban manta ba so munyi equal nida ke na auri Ak ne Dan na nuns miki matsayin ki ke ba kowa bace kamar yards kika wulakantani sai kuma Allah ya Dora min son Ak amma gashi yanzu ni da ke min rasa shi amma ba komai tunda munyi 1_1 ni da ke I don't care.

Kallo kawai ta bita dashi lallai Muna days daga cikin wadanda duniya ta rude su mun bi San zuciya da gangar shedan mun rasa komai se mu koma gaban iyayen mu gwsra ni Amina iyayena masu hali ne kr kuma ki koma gaba inna da baba a cigaba da cin tuwo miyar kuka.

Ba komai faridat ba komai RUDIN DUNIYA  ne ya debe mu kuma ya sauke mu saduwae alkhairi daga nan tayi gaba zuciyarts na mata kuna.

✨✨✨

Kan shi yay masa mugun nauyi yana fita a farfajiyar gidan yaji wani irin jiri na dibar shi hakan yasa ya dan dakata ya Dan ji dams dama da ya huta ya yafito driver Dan baze iya driving ba kaini gidan hajiya.

To yallabai an gama.

Koda suka je gida ya jima kamin ya fito daga motar da kyar ya Shiga ciki kan sa na Sara masa yana ganin juwa .

Hajiya na kallo muhaseen na kasa tana cin Dan malele ga yaji a gabnta ga manja .

Yadda ta gan shi tasan ba lafiya seta ji wani iri ita kanta hajiyar seda ta tausaya masa amma ta kasa bayyanawa a kan fuskarta.

.haji ..ya ya fada yana kakarewa.

Kallon shi suka yi a tare sedai hawaye kawai suka ga yana yi ya dafa kan sa yana jin wani irin ciwo.

Lafiya Ak? .

Ita ko muhaseen gaba daya hankalin ta ya tashi so take ta je gun shi amma tana kunyar hajiya.

Ak lafiya?.

Muhaseen ki yafe min ki tallafi rayuwa ta ki rike ni da amana  kin ji kar ki cutar dani wallahi asiri....be idda karasawa ba ya fado Tim kasa ya sume cikin rudewa muhaseen ta soma furta innallillahi wa inna illahir rajun tana kuka ta juya waje da gudu tana haki tama manta da cikin dake jikin ta.

Karo suka ci da ayman ya rikota ganin zata fadi tana kuka.

Auntyna lafiya? Meya faru?.

Ayman yaya Abdool a ciki..

Hannunta yaja suka shiga ciki tare yanda yaga wan nasa sedai ya tsorata.

Subahanallahi! Hajiya garin yaya meya same shi.

Ayman muje asibiti.

Nan ya cicibeshi yasa a mota Tare suka tafi asibitin dukkan su.

Daddy suka kira a ways suka sanar masa be jima ba ya karaso gun su.

Hajiya faridat ta kira ita da Amina su zo asibiti mijin su ba lafiya.

Haka asibitin ya cika da jama'ar Ak kowa jiki yayi lakwas.

Faridat meya same shi ne?.

Ta sa kuka hajiya ya sake mu fa dukkan mu ni da Amina.

Saki? .

Hajiya ya sake mu,Muna shirin tafiya ne ma kika kira mu.

Subahanallahi meya jawo hakan?.

Ak ya fara hauka ne? Inji Daddy .

Duk yadda aka yi wani abun kuka masa haka kawai Ak bazai sake Ku ba. Ki fada min gaskiya me kuka masa?.

Hajiya ban...masa..komi..ba ta fada ba kin ta na kakarwa.

Hajiya kawai kallon ta tayi ta CE Allah kyauta.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now