25

240 18 1
                                    

🌐 *Hikimah Writer's Association.*

🌐 *✍🏻 khairat up*

🌐 *Loading.....*

🌐 *Rudin Duniya!*

🌐 *pg 25*

    *vote@wattpadkhairi_muhd*

Ran kamu dangin su AK sun zo manyan mutane cikin shiga ta alfarma, ga likin dubu dubu da suka dinga yi.

  Amarya ma ta sha kyau.

Tana zaune a kan kujerar da aka mata na zaman amare ga kuma dec da aka yi a gun kums gidan alhamulilahi ya ci mutsne sossai, dan basu wani kama hall ba.

  Muhibbat  cikin wani rantsatsan less ta karasa gun Muhaseen ranta fes, ta dafa ta.

      "Sannu auntyn mu nasan baki san ni ba, sunana Muhibbat yar autar su big bro gaskiya yaya yayi dace mun ji dadin samun ki wallahi kin yi Allah baku zaman lafiya."

     "Nagode nace da ita ina murmusawa a takaice."

Haka dangin shi suka dinga tururuwar zuwa ganin amarya ita kuma faram faram take amsa masu kuma basu nuna mata 'kyama ba.

Hakq taro ya tashi washe gari daga gidan su AK Muhibba tazo da wata cousin din ta jidda sun kawo wasu kaya wanda zata sa anjima a program din da zasu yi, na launching harda me make up suka zo da ita.

Duk bidirin da ake Saffiya bata zuwa kowa yasan bakin ciki take yi ana ta yi da ita a dangi dan gidan ma ta bari kuma ran Umma ya sosu da abinda ta yi.

  Aiko ba karamin kyau tayi ba a hall din afficnt aka yi gun ya tara manyan mutane masu kudi ,yan kasuwa, da abokai da dangi.

An yi taro kam yayi kyau .

Washe gari aka yi daurin aure tun da aka fadawa Muhaseen an daura aure take kuka kamar ranta ze fita idanunta suka yi luhu luhu suka yi jajir dasu tun ana lallashin har aka hakura aka barta a dakin ita kadai dan ita kukan rabuwa da AK take yi,shi kennan yaya ABDOOL dina an raba mu ni da kai wayyo Allah na.

   Wayarta ta kunna tana kunnawa kuwa ta dinga ganin messages rututu na AK, ya dinga shiga wayarta.

"Muhaseen wai ina kika shiga ne? Gaba daya kin daga min hankali pls ki kunna wayar ki ina bukstar jin muryar ki."

"I really miss u my sunshine."

"My baby doll ki kasance dani har karshen rayuwan ki,dan Allah ki dinga tunawa kin bar dan maraya yana kewar ki."

"Muhaseen am sick".

"Muhaseen ina hanyan zuwa nigeria yau din nan dan na gaji da rashin ki, jikina yana bani kina boye min wani abu."

Innsllillahi wannan ai sakon yau ne yaya zan yi?.

Kuka ta kuma saki ta kwanta a kasa tana kuka.

Wani irin jiri nake gani dan rabo na da abinci har na manta gaba daya ban da kwari.

Misalin karfe uku na yamma aka turo motocin daukan amarya.

Toilet na shiga dan yin wanka, na hafa da waya ta, na soma rubutawa ya Abdool sa'ko.

"Salamu alaikum yaya na abin alfaharina, nasan lokacin da zaka ga wannan sa'kon nayi nisa a rayuwar ka,sedai ka sa ni na kasance me kaunar ka tsakani da Allah da zuciya daya, sedai ba wanda ya tara sa ni da Allah, ni ma na hakura na yarda da kaddarar da Allah ya dora min, amma ina so ka yarda cewa ni Muhaseen ban yaudare ka ba sedai na bi umarnin iyaye na ne kuma ban ki ka ba har na mutu kai ne a raina.
   Ina so ka yi min alkawarin zaka manta dani kuma zaka dau hakurin rashi na,ina so ka kasance me yarda da kaddara.ysya na bazan manta da wannan ranar ba a rayuwata ba,yau ce ranar da aka daura aure na da wanin ka ,ina maka fatan alheri a rayuwar ka,kuma ina maka murnar auren ka nasan zaka yi musu adalci kai din jarumi ne se wata rana!."

Daga nan ta kashe wayar gaba daya ta cire layin gaba daya ta balla shi ta jefa cikin shadda tayi floshing din sim din.

Wanka tayi,ta fito less ta saka fari ta dan murza powder, ta yafa mayafi fari.

Nasiha aka dinga min ta ko inq haka ba baffa na da kuka muka rabu,Umma ma tay min fada da nasiha nidai a raina nace "uhm ashe dai Umma an san dokokin aure amma ake takewa saboda Duniya."

Hannu na rike da na Muhammad muka nufi mota dan naki cika shi muna kuka duk jarumtar shi kuka yake na rabuwa da ni haka nima , a motar aka yi daru dan da kyar aka raba mu ni da muhammar har muka je main housr din su kuka nake yi ban ma san da suwa muka taho ba ni dai ina kukan rabuwa da masoyina da kuma baba na,da kani na.

Hannu na aka kama aka shiga dani gidan nasu seda muka yi er tafiya naji an na cewa ki shiga kiyi wanka amarya ki shrya ga kayan nan a kan gado ki fito zaku gaisa da jama'a kuma za ayi budan kai washe gari da safe kennan wato suna al'ada  nan kenan.

Kai na gyada karar rufe kofa naji alamar an fita hakan yasa na bude fuska na nayi bandakin na sake wanka ina tsaki wai an maida kai ksmar wani agwagwa ayi ta saka wanka mtsw.

Ina mita dai nayi wankan nan.

Na fito na saka kayan material ne seegreen na saka na kuma wani lullubin na zauna.

Mintuna kusan ashirin na debe kamin aka shigo dakin.

Amaryar mu mun barki ke kadai ko?.

Nidai ban yi magana ba.

Aunty na ki bude idanun ki kanwar ki ce fa  lil sis din yaya ce.

Naki dai budewa suka rike ni muka fita daga cikin dakin.

A kasa muka zauna ana ta maraba da amarya duk wanda yzo buden fuska ki nake yi na rufe ta gam.

Se suyi dariya ai zamu gani gobe.

Nidai ban ce ci kanku ba ko na nuna wata alama ba kuka kawai nake a hankali ina shasheka kawai fuskar ya Abdool nake gani , da kuma irin halin da ze shiga nake.

A hankali na soma nanata innallilahi wa inna illahir raju'un nake.

Jiki na a matukar mace yake ga gajiya kaman sun karanci halin da nake ciki naji ance ku rakata ta ci abinci ta huta ta kwanta gobe ma wani hidimar za a yi.

Su Muhhibat din dai su suka kuma raka ta dakin ta zauna kan cerper suka mata seda safe suka fita daga cikin dakin.

Ina bude lullubi na kuma naji ana kokarim bude kofar da sauri na mayar na rufe ina tsaki.

Murya kawai naji ana cewa amarya barka da dare, ga abincin nan an kawo inji Hajiya ,seda safe.

Gyada kai na kawai nayi duk na gaji tana fita ko na mike na sa wa kofa sakata na kulle.

Tuwo nw miyar agushi da kuma friedrice a daya kulan sa kuma paper chicken.

Kadan na tsakura naci kawai na kuskure bakina ko kaysn ma ban iya cirewa ba na kwanta a gun dan na gaji na jima ban kwanta ba.

   Amarya asuba ta gari,.

Share

Comment

Like

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now