12

292 23 0
                                    

HIKIMAH WRITER'S ASSOCIATION

RUDIN DUNIYA

NA KHAIRAT UP

PG 12

VOTE@WATTPADKHAIRI_MUHD

LOADING.........

Haka aka tashi dinner karfe dayan dare. Nan kowa ya kama gaban sa.

Su Sopie ana waje suna jiran me motar da ya kawo su, lokacin kuma A.K ya fito gaban motar kuma faridat ce ya dan dakata ya zuge glass din sa yana murmushi ya ce Saffiya baku wuce bane?.

Wallahi muna jiran driver ne.

Ohk to seda safe mungode sossai Allah huta gajiya.

Amin mun gode.

Uwargida ki gaida gida.

Banka mata harara Faridat tayi ta buga siririn tsaki ta juyar da kanta.

Saffiya bata damu ba sedai a ranta ta kudurta seta tarwatsa zaman lafiyan ma'auratan.

Motar yaja suka wuce.

Ko minti biyu basu yi da barin gun ba drivern su yazo suka shige gidan su jamcy aka maida su.

Faridat ban ji dadin abunda kika yi wa Saffiya ba.

Ta juyo ta masa wani irin kallo wanda ita kadai tasan ma'anar sa sedai ta kasa ce masa komai kawai kwafa tayi.

Haka dai suka je gida ya sauke ta shi kuma ya dau hanyan zuwa gidan su.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐

Da misalin karfe takwas na safe Saffiya ta gama shirin ta, suka yi sallama da Jamcy a zuwan zasu hadu da yamma zuwa kai amarya.

Jamcy tace kee bafa nan zata zauna ba saboda haka ban zuwa ina da wata sabgar anjima dan alhajina ze zo.

To ina za a kaita?.

Abuja mana.

Kai Allah dai ya kaimu wannan garin.

Amin.

Har zata fita Jamcy ta jawota ke kawata dama ina ta son tambayar ki fa.

Sopie tasan za a yi haka seta yi kaman bata san me za ta tambaye ta ba.

Wai wannan zazzafan guy din ina kika san shi?.

Hmm!kawata kennan ni din ai ba ta wasa bace Allah ne ya bani kifi daga sama gassashe.

Suka tafa suna kyalkyatar dariya.

Kinga tafiyata kar baffa ya farga.

To se munyi waya.

Ahan.

Mama se anjima.

To yar kirki kin wuce?.

Eh mama.

To ki gaida umman taku.

Zata ji insha Allah.

Haka ta tari napep ya kaita gida cikin ikon Allah kuwa baffa na kofar gida sedai be ce mata komai ba haka ita ma.

A soron gidan nasu tayi tozali da muhaseen tana shara.

Sannu da zuwa yaya.

Youwa ta fada a yatsine.

Tana shigewa ko irin sallamar nan babu suka fara shewa da umman su ana yaba surveniers da aka samo.


Muhaseen ta girgiza kanta kawai.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now