19

239 24 0
                                    

🌐 *Hikimah Writer's Association.*

🌐✍🏻 *Khairat up*

🌐 *Rudin Duniya.*

🌐 *Loading......*

🌐 *Pg 19*

   *vote@wattpadkhairi_muhd.*

     Lokacin da ya kira ta sun tafi round wayan a silent take kusan missed call goma ya mata.

   A matukar sanyayye ya ajiya wayar ya kwanta da bayan shi hankalin shi a tashe mesa bata dauka ba?. Kila suna wani aikin ne, zan kuma kira anjima. Ya lumshe idanuwan shi ruf barci me dadi ya dauke shi,.

  Ita kuma da suka dawo dakin su a gajiye take da kyar ta sauya kayan ta, sannan ta duba wayarta missed calls ta gani guda goma cike da mamakin wanda yayi kiran "to waye wannan? Meya faru irin wannan kira haka?".

     Kiran shi tayi,sau uku ta kira be daga ba ta tabe dan karamin bakin ta,sannan tayi salolin ta kamar yadda ta saba tayi adduo'i wa Baffan ta da Umma, sannan ta rokawa Sopie sauyin hali da shiriya,daga karshe ta kwanta.

   Asuba ta gari.

  🌐🌐🌐🌐🌐🌐

Kamar yadda alh.yusuf ya fada haka aka yi da yamma yazo aka auna komai kuma yace gobe yake so a fara aikin, a ranar suka harhada en tsumokaran su suka bi alh.yusuf gidan da ya basu kamin a gama gyaran gidan nasu.

Sossai Baffa yayi godiya kamar zeyi kuka daga karshe seda ya bata rai tukun ya hakura suka rabu akan gobe ze aiko a dauki masu zuwa ganin gidan.

Shigar sa keda wuya Umma ta nufe shi.

   "Malam ina ka samo wannan mutumin me kirki?."

  "Uhm abokina ne".

"Gaskiya in har haka abokanai suke Allah ya baka su guda dari,kalli daular da aka kawo mu ,kai ko a mafarki ka taba tunanin zaka zauna a killataccan guri?."

"Murmushi yayi yace ai abin na Allah ne".

"Wallahi naji dadin wannan harkar ai ni na dauka wannan dagargajajan gidan a ciki zan mutu ba wani cigaba,duk da nasan cewa idan Mekyau tayi aure a gidan masu kud'i,se mijin ya gyara mana ashe ma kai kana da abokai masi kirki ka mana mugunta saboda ba ka san cigaban mu."

"Ke a kullum burin ki *DUNIYA!*?."

"Yo to wa ya 'ki daula?."

"Hmm kiji tsoron Allah,ki koyi godewa Allah da abinda ya baki, abubuwan da kike yi ba daidai bane ita waccan da kika dorata a kan tsarin ki ta hau ta zauna Allah ya shiryeta kuma duk talauci na mahaifinta ne ni kuma mijin ki ne ni ban fidda tsamani da samun rabo ba bani nayi kaina haka ba Allah ne kuma yana sane dani,kuma ze duba min ,kuma yana jin kai na bazn tabe ba ni Duniya bata gaba na fata na ,na gama da duniya lafiya."

"Ai kai matsalar ka kennan wa'azi nima ai nasan Allah,kuma wa ya ki cigaba da hutu a rayuwa?dole ka dinga hangowa kan ka cigaba da kuma jindadin rayuwa ni me nawa ai talauci abin gudu ne abin ki ne sutura ma gagarar mu yake,badan Allah yasa yarinyar nan tana da goshi ba ai wata ran ma ruwa gagarar mu zata yi."

"Hmm!, Allah ya shiryr ki."

"Amin".

"Kina sane da bikin Muhaseen ko."

"Au wai dama da gaske kake?.

"Ya bude baki wasa kuma? Ai na gaya miki bikin wani watan ko? To ki soma shirin na Muhaseen dan wani watan ne nata."

"Har wani shiri zan mata? , ai tunda bata tanadar mani ba nima banda shi,ai ita er'uwarta tayi wa kanta kuma ta samo inda zata huta  ita kuwa fa? Ta ringa ta sa a ranta talaka zata aura seta je can ta karata ni nan ko taron wuni bazan yi balle in samu kudin siyan mata ko cokali ai saboda haka na ce ta dinga kula alhazawa."

"Haka ne, Allah ya sauwaka,ni zan mata komai da ya kamata ayi in sha Allah bazai gagara ba,"

"Wannan kuma kun fi kusa dama ai ta wurin ka ce."

Shi dai wucewa yayi kawai daki yana mamakin hali irin na matar shi wadda Duniya ta rufe mata ido, taks bambamta tsakanin ya'yan ta.

*********    *********

Washe gari dake yana da meeting be wani bi ta kan waya  ba ya gama shirin shi ya fito.

Kan dinning ya tarar da mutuniyar tasa ta sha ado cikin kananan kaya.

Tashi tayi ta rungume shi ta masa peck a goshin shi hade da cewa "good morning".

"Idanu kawai ya lumshe ,ya zauna,tea da toast ya ci ya gama ya goge bakin shi ya tashi ya dau mukullin mota ya fita.

Tsaki ta buga cike da takaicin abinda ya mata amma ya zata yi?, ita take nema ai dole ta shanye duk wani wulakanci.

     Wayar jiya ta uwar mijin ta da bata daga ba ta kira yau saboda tana san samun information.

    Salamu alaikum hajiya!.
     Wa'akaikum salam!.
         Hajiya ina kwana?.

Lafiya lou.

Madalla,.

Hajiya kiyi hakuri dan Allah jiya ashe kin kira ni ban gani ba saboda wayar a silent take se yanzu na gani.

Ba komai dama nasan kina busy ne shi yasa baki dauka  ba dama mijin ki ne ya kawo min korafi a kan ki.

Hajiya nasan ban kyauta ba amma ayi hakuri bazan kuma ba.

Nidai ki kiyaye kinga nina hada auren ku kar ki jawo abinda zesa muji kunya da ni da ke pls kina kiyaye dokokin shi kinji.

To hajiya insha Allah 😏 (iyayin banza wai ita babba.) .

Youwa ina fata ya fada miki zancen auren shi?.

Da kissa tace 'eh ya fada min.

To kina ji ko?.

Eh.

Kar ki damu ,kar ki daga hankalinki,hakuri zaki yi kinji?.

To hajiya.

Youwa ,shima alhajin shi ne ya zaba mishi matar da zai aura wani watan ne bikin.

Hajiya wacece ita?.

Ni kaina ban san ta ba,shi ma AK besan ta ba,hasalima alhajin shi kadai yake abun shi kawai kiyi ta addu'a ,nasan alhaji bazai zabo wadda zata daga maku hankali ba.

To ai ba komai hajiya nagode insha Allah zan kokarta kauda kai na.

Haka nake son ji,Allah miki albarka..

Amin .

Ashe ma tsohuwar bata san komai ba, ita ma hoto ce, amma zasu sani shi alhajin zega aure zewa d'an sa dani suke zancen mtsw munafukan banza munafukan wofi wai su masu d'a.

Misalin karfe hudu na yamma , ya kira num Muhaseen dan yaga kiran ta.

   Num jiya ta gani ta kuma kira cikin sauri ta daga wayar.

Salamu alaikum!.
    Wa'alaikun salam!.
Gaskiya kin wahalar da zuciyar wannan bawan Allahn da yawa.
   Wake magana?.
Sunana ABDULKARIM!.
Ta maimaita sunan,ban gane ka ba gaskiya..
Hmm wanda kuka hadu a jos.
Sai lokacin ta tuna tace "oh" sannu.
Au sannu ma zaki ce dani kawai?.
   Hmm to ina wuni?.
Lafiya lou sedai ina cike da kewar ki.
   Banbarakwai taji tace "kewata kuma ta me?."
    Baki gane bane ko son ganewa ne ba kya yi?.
   Ban gane bane gaskiya.
Are you innocent or u re trying to be 1?.
  Murmushi tayi me sauti. "Da gaske ban gane ba".

To shi kennan "in a simple and short language *INA SON KI*."

*WHAT!*

SHARE

LIKE

COMMENT.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now