47

237 25 1
                                    

RUDIN DUNIYA

KHAIRAT UP

PG43

Ihu ma'aikatan gdn suka sa kun San mata da ruruta abu ,wata cewa tayi ”ta mutu” nan gida ya hautsine da kururuwa.

Ak da saurin shi ya shigo gidan ya nufi bangaren da ake zuba ihun ai mamakin yanayin dakin ne ya kama shi tamkar gidan da aka ajiye mahaukaciya haka falon ya koma duk wani Abu me amfani an lalata shi hatta TV an lalata shi lallai faridat bats da hankali.

Aminan ya hsngo a yashe a kasa tamkar dai gawa haka ya ganta da sauri ya matsa kusa da ita ya taba hannun ta da Sauri ya cicibeta yay waje da ita

Ko ba a fada ba an San asibiti ze kaita.

Faridat kam Fita  tayi ta koma dakin ta wanka tayi ta sauya kaya zuwa wani runtsatsan material ta yi ado ta zuba gwal ta dau key din mota ta yi waje ko alamar nadama balle damuwa babu a fuskarta.

Mamakin ta kawai suke ji ita ko muhaseen dakin ta ,ta koma ita ma tayi wanka ta dauro alwala sannan ta tada sallah hakan nan taji gwara tayi ta sallah ko ta samu ragin damuwarta .

*ASIBITI*

Likita ne ya duba ta lafiyan ta lau saidai shock data shiga ga kuma targade a hannu nan aka gyara mata aka sa mata bandage,aka mata allurar pain relief sannan suka sa mata drip.

Gidan  ya koma bayan ya gama biyan bills din kan shi ya gama daukar caji shi kam ga shi iya jin yunwa be bi takan faridat ba dakin muhaseen ya nufa direct, budewa yayi ya afka cikin dakin da farko ji yayi kan shi ya bada wani irin sara tamkar an buga masa wani irin karfe a kai haka yaji, sedai muhaseen na sallah hakan yasa ya dafa goshin shi ya juya ya bar dakin.

Sallama tayi ganin ya fita yasa tayi tunanin ko yana bukatar wani abun ne hakan yasa ta ta shi ta fita ta bi bayan sa.

Bata gan shi ba seta kira wayarsa.

Seda ta kusan tsinkewa ya daga hello

Hello yaya naga kazo ka tafi lafiya dai ko?.

Eh lafiya Lou kawai na leqo ne.

OK ya me jikin?.

Da sauki maybe anjima mu dawo tare.

To Allah kara sauki, ko za ayi mata girki ne?.

No kar ki damu zan mata take away ita kadai CE ai.

Aa yaya ba komai zan mata.

Cike da kosawa yace nace miki kar ki damu ko aha dole ne wai mtsw ya kashe wayar.

Ita kam tabe bakin ta ta yi kawai tace maza Kennan ai bani na kar zomon ba rataya aka bani.

Gidan su yaje nan ya fadawa hajiya abinda ya faru sossai ranta  ya baci ita ma,ta dinga yin tsaki INA faridat din?.

Ban ganta ba da na koma.

Zan yi maganin ta haka ake yi kishi hauka ne? A kanta aka fara ba ita ta bawa kawar tata fuska ba harta aure mata mijin ba?kaima in banda jaraba mata biyu basu isheka ba? Gashi ai tun kan kaje ko INA an fara hada gobara a gidan naka .

Hajiya wai ya zan yi ne?

Kaddara ce Nima ban San me ya kaini ba yin auren nan.

Mtse shashasha kawai kuyi ta wasa da addu'a haka kuka iya ba zama da alwala ba yin adduo'i ba bin dare kayi sallah ko kayi koyi da matar ka ai ita kuka cuts ma duka duka yaushe kayi auren bata more ba sai ka auro mata wata ga shi gidan naka ya ci wuta.

Hajiya kiyi hakuri addua zaki min wallahi ban jin dadi ko kadan.

Tashi kaje anjima in kun koma zan zo gidan naku.

Tom se anjiman.

Ehe.

*FARIDAT*

Faridat ko ba Inda taje se gidan su Amina aiko taci sa'a baban nata ma na nan aiko rants kal ta Shiga gidan ko sallama babu da buta ta fara toxali data yi wata iriyar ball da butar seda suka mike dama hira suke yi, ta yi watsi da kurfeto da aka Dora girki a kai ji kake abincin ya zube har seda ya kona kafar Babar amina.

Innallillahi Faridat mezan gani?

Au tambayata ma kike? Tsohuwar banza me koya wa erta satar mijin wata ni zaku ma  butulci Ku aura wa erku mijina ni za a ciwa amana lallai kun tabo wuta wallahi sena yi maganin Ku.

Subanallahi me kike....

Ke wallahi yau a sama nake yanzun nan na kai yarki asibiti ta mutu ko tana da rai oho amma ni nafi so ta mutun ma to ki Bini a hankali kar na mika ki kema a baki gado kusa da ita.

Innallillahi wa inna illahir rajun faridat me ya faru kardai kice min mijinki amina ta aura?.

Hehe gulma da tsugudidi Kennan ni zaki ma bariki kin koya mata snatching zaki nuna min baki sani ba? To wallahi kiyi gaggawar Neman mata saki ko na aika miki ita barzau.

Wallahi er nsn bamu San mijin ki bane abdulkarim bsmu sani ba.

Ta zabga mata harara ta nuna ta da key din mota gargadi ne wannan akwai saura matukar erku bata rabu da mijina ba,wato an gaji da cin tuwo miyar kuka da alkubus shi ne zs a mannrwa gidan cin kaji to karya ne tayi tsuks ta fice daga gidan.

Gidan su Ak ta wuce direct ganin kiran hajiyar tasan sauran zancen kuma ta shiryawa kowa Dan an yaudareta harda ita hajiyar da bata ankarar da ita ba ita ma muhibbar zata ci ubanta wallahi munafukai kawai 😡.

Shima in be wasa ba sena yanke masa abar 🙊 in yaso in ga ta jarraba mtsw.

✨✨✨✨✨✨

Muhaseen kam amai ta dinga yi bayan sun gama waya da AK duk ta galabaita ta kasa cin komai ma har zaxzabi take ji.

Kwanciya tayi ta huta kamar jira zazzabin yake take yace sallamu alsikum ruf ta rufe jikin ta saboda wani irin sanyi da take ji ga ciwon kai.

✨✨✨✨✨

Asibiti Ak ya koma. Kuma ta tashi sedai tausayi da dariya ma ta bashi lallai faridat ta iya Abu ji yanda ta sauys wa amina kamanin fuska duk ta yi wani iri fuskar ta kumbura ta yi suntum, ga gefen idanta ya yi wani malolo ga karaya bakin ta ya yi wani irin ja juyawa yayi seda yayi me isarsa ya koma dakin....

Ita kanta haushin kanta taji wai ta tsaya kishiya ta mata wannan dukan ai wannan raini ta jawo wa kanta, bats kuma kullewa ba seda taje toilet taga fuskarta kuka ta saka kawai lallai faridat zamu gamu dake se kin san cewa ni kika yiwa haka.

Katse mata tunsnin yayi ta hanayar yi mata magana.

Ya jikin?

Da sauki ta fada .

Ba Inda me miki ciwo?

Eh se dai hannun.

Ai Dama se a hankali wannan ki tashi zamu wuce gidan an bamu sallama.

To.

Nan yasa wata nurse ta taimaka mata ta kaita mota, ya mata ihisani sannan ya ja mortar.

Kwantawa ta yi jikin kujerar rants na mata suya lallai faridat baki San ni ba ni zaki yi wa tijara? Muje zuwa yanzu aka fara.

Pls manage!

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now