9

258 20 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

    🌐 *RUDIN DUNIYA!*

*KHAIRAT UP*

    *PG9*

*Vote@wattpadkhairi_muhd*

Kwance yake kan daya daga cikin doguwar kujerar da ke cikin falon gidan,ya hakimce cikin pjms da singlet ,gaban sa plate ne dan madaidaici da cake a kai irin cup cakes din nan me shape din love, da kuma glass cup da lemu a ciki na kwalli ecxoctic yana mugun kaunar lemon ecxoctic kamar dan shi aka yi shi. Hannun sa waya ce yana dube_dube a ciki hankalin sa na kan wani chart daban wanda yake yi da abokin sa a can canada.

Request din mekyau ne ya fara masa sallama da kamar bazai bude ba sai kuma ya duba.Hoton ta ne ya dauke masa hankali wanda ta dauka tana zuba murmushi ta sha make up , (kwalliya na d'aya daga cikin abinda A.K yake so shi kuma a rayuwarsa, sedai yana da kishi in har ya ga abu ya masa to abun nan nasa ne shi kadai saboda haka nema be cika son faridat tayi make up taje unguwa ba inko tayi ranan ba sauki a gun miskilanci da fushi, ya fi so ayi masa kwalliyan shi kadai ya gani ya yaba.)

Saffiya Abubakar (sopie) ya ga an rubuta, folder ya shiga ya dinga ganin hotunan ta haka kawai wata zuciyar tace masa ya mata magana.

Hannayen sa suka soma rubuta:-

"Salamu alaikum"

Mekyau na tsaka da hira da alhajinta taji shigan message din ai ta waro idanuwan ta waje cike da mamaki a fili tace"so early?" lallai zamu da kai, cingum din bakin ta,tayi kwai dashi ta saki murmushi tayi wal da idanuwan ta!. Bata yi masa reply ba seda tayi kusan mintina biyar sannan ta tura masa:-

"Wa'alaikum salam"

  Yana amsawa Samir ne yaji alamun sak'on hakan yasa ya bawa Samir amsa a gurguje ya duba sak'on.

"Ya kike?"

"Alhamdulilah."

"Okey".

"Uhm ita ma ta fada".

Shiru ya biyo baya shi ya rasa abun cewa, ita kuma tana jan class ne wata dabara ta fado mata ta sake tura masa da wani messg din.

"Erm Abdul ne ko?".

"Yeah!".

"Youwa koda naji kwana biyu shiru ina ka shiga muna ta cigiyan ka?.

Shiru yayi a fili yace "ni kuma ina na san ta?.

"Kayi shiru ina ta magana".

Uhm bara na tambaye ta inda ta san ni ko kuma ni inda na santa.

"Ban gane ki ba?.

"Kamar ya".

"Kamar yadda na fada miki ban gane ki ba".

"Sofie ce fa , sofie me kyau".

"Yeh na ga sunan sedai ban gane ki ba duk da haka ki karan haske a kai".

"💃🏻 haka nake so dama 😊. Ko ba abdulazeez kabir bane wanda yayi legal A.K?".

"Gaskiya ba shi ba ne ".

😂 zaka yi bayani ne ai ka kusan zuwa hannu saura kiris.

"Oh dan ALLAH yi hakuri na dauka wanda na sani ne ,am sorry kaji dan Allah.

"Ba komai".

"Se anjima".

"Okey".

Daga nan suka sauka dukkan su sedai sopie ta so ya tsaida ta su yi hira sossai, shi kuma A.K be wani wai maida abun serious bane ba ya mike ya nufi dakin sa inda ya shiga bandaki ya watsa ruwa yasa kayan barcci ya yi sallah ya kwanta dake faridat na gidan su.

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now