28

259 21 0
                                    

🌐 *Hikimah Writer's Association*

🌐 *Khairat up*

🌐 *Rudin Duniya!*

🌐 *Loading.......*

🌐 *Pg 29*

*vote@wattpadkhairi_muhd*

Koda suka koma gida, Muhaseen a daki ta zauna dan Hajiya ma dakin ta ,ta wuce dan suna bukatar hutu.

Sallah tayi tayi addu'a Allah ya bawa yayan su Muhibat lafiya a can india.

Wajan karfe daya na dare barci ya dauke ta.

Hajiya ma sallar tayi ta jima tana addu'oin ta ita ma duk dan samun lafiyar dan ta Abdulkareem.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐

*INDIA!*

*Jeevandan hoapital*, suka nufa dake nan ne asibitin da suka yi komai,ambulance din asibitin ne suka dauko su daga airport.

Karkashin kulawar DR.vedant shirvastav,shi ne likitab da ze duba shi be wani jima ba ya duduba shi kusan hour daya yayi a kan sa.

Kamin ya rubuta magunguna da za a soma amfani dasu for changes.

Yayi wa su Daddy bayanin abinda ake ciki zasu yi wa AK aiki amma se an sa shi a under observation na three week's tukuna.

Daddy yace masa "jikin nashi ze ji sauki ko?".

Nan yayi counsolling din shi ya ce masa "we ll try our best,but waraka daga Allah ne (cikin harshen nasara suke maganar dan Dr.vedant baya jin wani yare se turanci da kuma Indiyanci.)

Daddy yaji dadi suka samu taxi ya kaisu masaukin su can Meera road suka nufa nan aka kama masu gida.

Wanka suka yi tukuna sannan Ayman yayo musu order online na abinci rice da biryani se lemu da pizza ,da paratha aka kawo musu.

Sun ci kuma ba laifi yayi dadi,nan suka sha tea, black tea sannan suka kwanta bayan sun rama salolin su.

Barci suka yi dan a gajiye suke sossai.

Karfe goma na dare suka tashi bayan Faridat tayi wani wankan tasa sleeping dress ta dau wayan ta , mum amina ta kira kuma tayi sa'a a kunne take wayar.

Kawata,
Mutanen India kice kun sauka?.
Sossai ma tun dazu bab kira ki ba ne saboda ina barci.
Ayya to ya gajiya?.
Alhamdulilahi.
Masha Allah to ya jikin AK?.
Jiki da sauki dan naji dazu Dr ya ce zasu yi observing din shi na sati uku tukuna zasu masa aiki dan an dora shi a kan magunguna.

Allah dai ya bashi lafiya.

Amin.

Ina kishiryar taki?.

Hhhh , wallahi kin cuce ni,ni zaki ce ma kishiyata? Yarinyar da bata wuce in take ta ba in tumurmusa ta ba ai na fita class,ko kin manta ni ce uwargida kuma amrya?.

Hmm ke kina wasa da damar ki Fari ya kamata ki mike tsaye ki nutsu dan kuwa wannan da kika raina she ve everything.

Mtsw,kina kawata kina kod'a wata daban?.

Ba kod'a ta nake ba ina fada miki kalubalen da yake a gaban ki ne, dan tana da kyau kar ki ganta black but she ve everything namiji yake so ga ido,ga hanci,above oll ta na da diri me kyau me daukar hankali babe tana da da shape me kyau,her hips oh my God kin san AK kuma ko? , he Love's mace me kyan figure da iya ado.

Hmm!,Amina seda safe is olready latr hare gobe zan je asibiti early morning.

But Far....kamim ta karasa tayi cutting call din.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now