5

365 27 0
                                    

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                          

loadιng...........✍🏻

    🌐  *RUDIN DUNIYA!*

*PG 5*

*Vote@wattpadkhairi_muhd*

*✍🏻by khairat up*

Haka ta rubuta jarrabawarta sedai wulakancin da aka mata dszu yana ranta.

A bangaren me kyau kuwa likkafa ta cigaba alhaji ya samu shiga dan tana samun abunda take so sossai a gunsa kuma gashi sun gama tsara zuwa wajan bikin nan duk ankon sun samo shi hatta gate pass duk da ta yarda da alhaji still tana san zuwa ta kuma yin kamu dan ta hada tudu biyu hatta booking din kwalliya sun yi tankar dai bikin en gidan su ko en uwan su ko kawa ta jiki har gara ita kawar tata tasan wadda tasan amaryar ita ko me kyau ai gayyar sodi ce.

       _cikin shiga ta alfarma ya fito idanuj shi sanye da glassess fari da alama medical ne.yana da manyan gabbai, fari ne amma ba can ba,dogo ne,yana da manyan kyau sedai da kaga fuskar sa kaga me karancin fara'a da zallar miskilanci a tare dashi.wayar hannun sa ys duba ya dan saki siririn tsaki ya kuma kallon kofar dakin da yake tsaye a gun ya kuma sakin wani tsakin yana niyan barin gun ta fito cikin shiga ta alfarma ta sha make up,ya bita da wani shu'umin kallo ya watsar hakika tasab ma'anar kallon sedai ita kam baya biye masa sede in ya fasa fitar da ita haka ta bishi jikinta bs kwari dan tsab halin mutumin nata. Tuni yana cikin motar daga bangaren dama ita kuma ta zauna a bangaren hagu haka aka yi tafiyar kurame se kamshin turaruksn su ds sanyin ac dake ratsa cikin motar ya bada wani kamshi me wuyar fasaltuwa da mashe jikin me numfashi. Driver a cikin ransa ya cs oh alhaji dai haka yake da kowa har matar ma be barta ba na dauka mu kadai yake ma haka ashe kowa da kowa ne da alhaji yazo a jinin sarauta da an shiga uku izzar seta fi haka.tafiyar kurame aka yi tsakanin ma'aurtan haka suka je gidan iyayyen sa wanda yake cike da mutane ana ksiwa da kawowa ya kuma jan wani tsakin tabbas badan girma na uwa ba babu abinda ze kawo shi gida yau. A dan dikile yace maya kice ma mum ina wancan side din.to ta fada ita ma jikinta na kerma dan tana mugun tsoron mijin nata_

_Mum zaune cikin wani tsaddan less ya na kirga kudi gabanta en mats ne masu aiki guda hudu cikim shuga iri day seds ta gama sanar musu da sakon da za a siyo mata tukuna ta juya ta kalli surukar tata na ganki ke kadai yana ina? Tsugunawa ta fara yi tace ina wuni mum? lafiya lau alhamdulilahi kunzo lafiya?wallahi lafiya lou to madallah ina megidan naki?mum wai yana wancan side din kinsan baya san mutane ko kadan bslle da yaji ana ta hayaniya da kaiwa da kawowa.kai halin *A.K sai shi ina zuwa bara naje na same shi yaushe ze ce bazai zo bikin auta ba saboda mutane ai bama magana bace me yuwuwa ba bara naje*to sekin dawo mum autar na nan? Tana cikin dakin ta ita dasu manal.tom bara naje na same su._

      _cikin daya daga cikin kujerun ya zauna yana jiran isowar mummyn tasu,yana duba emails a wayar sa ya jiyo kamshin mum dinsu da azama ya mike ya nufe ta ya taro ta yana sakin murmushi ya tsuguna ya na gaida ta,cike da jindadi ta amsa tana shafa kan sa. Zama suka yi suka kuma gaisawa ta tambaye shi gajiyar hanya ya amsa ko kaifa har naji dadi bayan ksine babban su kace baza kazo bikin er uwar taka ba ai be dace ba itama baxata ji dadi ba mutane ai rahama ne ka dinga sakewa kana yin mu'amala da kowa kaji. Insha Allah  mum zan daure._

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now