41

239 22 0
                                    

*HIKIMAH WRITER'S ASSOCIATION*

*KHAIRAT UP*

*RUDIN DUNIYA*

*LOADING.....*

*PG 37*

  *vote @wattpadkhairi_muhd.*

Ranan da za a fara prgrams din bikin Saffiya ranan AK ya dawo sedai be fadawa Muhaseen ba yana so ne ya mata bazata.

Gidan shi ya wuce saidai be samu Faridat ba kamar yadda yayi tsanmani dan kuwa ya gama karantar ta in baya gari bata zama a cikim gidan kuma ta kasa dainawa duk da ya nuna mata baya so.

To ina Faridat?.

      Faridat na can gidan su Amina suna shafta dan Amina zuge Faridat take yi a kan irin wulakacin da zata na ma AK tunda ya mata kishiya a wannan hudubar ta koma gidan ta.

Ga mamakin ta AK ta gani a waje kan kujerar roba fara yana duba wayan shi duk da gaban ta ya bata dam bata ki fuskewa ba ta maze ta hade masa rai ,shi kam dariya ma ta bashi wai ta masa laifi amma zata masa shan kunu bara yaga iya gudub ruwan ta. Illai kuwa wuce shi tayi tana sauke ajiyar zuciya.

Faridat baki gan ni bane?.

Na gan ka man mene? .

Faridat haka ake tarban miji?.

To mezan ma goya ka zan yi ko kuwa kai din jariri ne daukar ka zanyi?.

Faridat...

Pls ni a gajiye nake se anjima.

Ta wuce ta barsa a gun ya saki baki yana mamakin canjin Faridat me take nufi?.

Se yamma lia wajan karfe shidda ya shirya cikim.shadda fara kak ta sha aiki ya sa hular shi ya fesa turare yana ta bada kamshi ya zura takalmin sa ya daura agogo aljihun sa dama da hagu ya cika da kudi ya dau key din motar shi ya fito.

Tana zaune kan dinning tana cin spagetti tabass mijin ta me kyau ne kuma dan gayu me class take taji wani irin kishi ya turnuke ta , sossai take son AK saidai shi taga alama bata ita yake ba ta wata cab daban yake.

Ya hade rai shi ma saboda yaga alama raini ya gifta musu ko kuma yana shirin gifta musu, ya sa kai ya fice yana gyara hular shi.

Wani iri taji ai seta saki kuka ina za shi to?

(Oho miki sakararar mata inji khairi mijin  ki ze fita ba dan rakiya ba addu'a ba soyayya, ba wani hug ko kiss ba kulawa kina kallon shi kawai ya fice. Mata mu gyara muhimmim abu ne a cikin aure tsakanin mata da miji suna mutuntunta juna ,kuna girmama juna da bawa juna lokaci,da kulawa,da kalamai masu sanyi ,ya kamata ko kina fada da oga kar ki daina masa duk abinda kika saba yi masa, hakan yana nuna mutuntaka, in ze fita ki masa rakiya ki jera masa addu'oi ki rungumesa ki masa kiss har yaje inda zashi da tunaninki zai dawo pls ladies take note.).

A bangaren me kyau kuwa ta sha ado kuma hakika ta zuba kyau ta saka mekyau sai kyalli take ansha make up ga gown matsataa tana jan kasa (lol dream marriage).

Dankareriyar mota aka kawo mata angon ta ma ya yi kyau ba laifi.

Can gida kuwa motoci keta kwashw en zuwa biki, inda na zura ido inga ta inda Muhaseen zata bullo.

Cikim hadaddan less ta fito ta yafa mayafin ta ,an mata make up me zafi gaskiya tayi kyau skirt aka mata da riga sun zauna a jiki ta kaman an gwada ta dala dala, har gyaran jiki Umma tasa aka mata sossai kayan sun amsheta kam.

Tana kokarin shiga wata mota ne taji wayarta  na vibrating daukowa tayi taga num mijinta

Fadada murmushin ta tayi ta dauka hade da yi masa salama.

Daga bangaren shi ya amsa mata hade da cewa my sunshine kin yi kyau kuma kin haska gun saidai am jelouse fa .

Ta ya ka gan ni ?.

Kina zumudin daukar wayata baki lura da num ba?.

Cirewa tayi ta kalla num nigeria ne.

Lah ya 'am wayyo ko zuwan bazata ni zaka ma haka ta fada cikin ahagwaba kamar zata yi kuka.

Dariya yayi yace am sorry ki miko gani a moto ki daina wannan shagwaban a gaban wasu ana kalle min ke kinji honey na.

Ni ai ba ruwana da kai

Ayi hakuri kizo na lallaba ki kinji ko?

Ta saki murmushi ta ajiye wayan ta nufi inda ya kwatanta mata sedai tana zuwa ya fito ya ce "masha Allah hakika am very fortunate da na same ki  muhaseen am relli the mosy luckiest husband ".

Ta kulle fuskanta tana jin kunya ya jawo hannun ta ya ji jan lalle yayi kyau yayi maroon ga baki da aka zana das besan ma sanda ya rungumeta ba forgeting cewa a waje ne suka fa kuma gun biki ne ahi dai kawai matar shi yake bida wani irin sirritancan kamshi yaji tana yi masa ya kuma matse ta gam kamar za a masa kwacenta.

Ya'am a waje fa muke .

And so?.

Ana kallon mu fa.

Shi ne me?.

Nidai ka sake ni

Barsu Muhaseen suga yadda mijin ki yayi kewar ki yake kuma son ki.

Pls mu shiga mota me mutane zasu ce.

I dnt care ni dai kece tawa.

Da kyar ya cikata suka shiga mota.

Yanmatan dake gun suka dinga santin AK dan kuwa ya yi musu karshe.

Ashe shi ne mijin Muhaseen lallai tayi sa'ar miji sun dace sossai da sossai.

Suna zuba life din su kam.

Zance dai rututu kala kala.

Seda ya gama neman maganan shi ya ja su zuwa gun bikin.

Lokacin ma an fara gudanar da taron amarya da angonta ma sun karaso suna high table.

Ak da Muhaseen suka shigo tare suna rike da hannun juna.

Dj ya fara ga kanwar amarya nan da angon ta ku basu hannu dan Allah

Saffiya ta dago idanunta zuwa gun ai kadewa tayi ta mike tace what? Mijin Muhaseen wannan tycoon din? Mutumin da yace yana sona? Ze kira ni yaki ashe kanwata yake bi tabdi impossible 😡
Muhaseen dani kike zancen tabbas bazan barki da wannan hadaddan guy din ba am coming for you.

Manage pls sister's

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now