31

293 31 3
                                    

🌐 *Hikimah Writer's Association*

🌐 *Khairat up*

🌐 *Rudin Duniya*

🌐 *Loading.....*

🌐 *pg 31*

*Vote@wattpadkhairi_muhd*

An samu AK ya dan ji dama dan numfashin sa na fita normal  ba kamar da ba da seda  taimakon oxgyn ba.

   Dakin suka shiga dukanin su yayin da gaban ta ya tsanan ta bugawa fat fat kamar me, ita ce daga karshe so ba ta samu ganin waye a kwance ba..

Seda suka raba suka raba junan su biyu tukun ta dago kanta da niyan cewa wani abun sedai idaninta ne suka yi mata gamo da abinda bata taba tsamanin sa ba da hanzari ta je bakin gadon tace "innalli llahi wa inna illahir raj'un ya Abdool meya same ka?, kai ne?".

Ha'a kin san shi ne dama inji  Hajiya.

Tana kuka tace shi ne wnda nake so aka aura min wani wallahi shi ne Abdulkarim da muke soyayya dashi.

Dady yace what? Kina nufin kece wadda ya rasa a sanadiyar ki ya shiga wannan halin?.

Ta kuma sakin kukan wai duk a kan ta ne yau AK ke kwance rai a hannun Allah subahanallahi.

Alhaji ashe lalube muke tayi a cikin duhu muna ta neman maganin AK ashe maganin na kusa amma rashin sani yasa bamu lura ba.

Faridat ta katse su "haba Hajiya taya zamu yarda da magan ta na cewa AK ya san ta? A ina ma zasu hadu da ita? Bayan Dady ne ya hadasu kuma wai dama saboda soyayyar wata ne AK ya kamu da ciwon zuciya?.

Kwarai ma kuwa nan ya fada musu komai..
Tabdi shi ne kalmar da Faridat ta fada a fili ta zumburi baki cikin ranta kuwa fal damuwa ce da tashin hanakali taya ya ma ze so wata..

Muhaseen ke kadai ce maganin ciwon AK ki taimaka kar ki bar d'ana .

Hajiya wallahi da nasan cewa AK shi ne mijina da ban tura mishi da sakon rabuwa dani ba, na kasance me kaunar mahaifina hakan yasa bana tsalle maganar shi duk abinda yace min bana kin yin sa ko me kuwa shi yasa da ya fada min cewa ya hada aure na da dan abokin shi ban ki ba saboda kaunar da nake wa AK bata kai na ki yiwa Baffana biyayya ba,dukkanin mu nida shi bamu san juna a matsayin mata da miji ba  bamu san juna a matsayin ya'yan abokai ba,wallahi ba da gayya na karya zuciyar masoyina ba sedan bani da wani katabus dole na bi iyayena 😭.

Wannan haka yake wannan dalilin yasa na aura wa AK ke saboda na yaba da hallayarki da nutsuwar ki da kuma biyyar ki,kuma kar ki takurawa kan ki kina tunanin kece silah ta shigar shi wannan halin aa ko daya kadara ce kuma rubutacen al'amari ne dole seya faru alhamdulilahi tunda mun samu lafiyar shi dan kuwa mun samo maganin damuwar Ak.

Muhaseen na tsorata nayi tunanin zan rasa AK saboda AK be taba neman abu ya rasa ba ko ya nuna abu yana so a hana shi ba shi yasa muka tsorata da yace yana son wata amma ya rasa ta .Amma mun godewa Allah da ya kawo saukin abun Allah ya bashi lafiya ya tashi ya gan ki.

Kuka ta saki ta kama hannun AK tana jin tausayin shi sosssai mikewa tayi ta fita waje ta zauna kan wata kujera ta hada kai da gwiwa ta ta saki kuka tana cursing kan ta a matsayin wadda ta jawo faruwar al'amarin, ashe mahaukacin so yake min wanda rashi na ze kawo shi ga kwanciya a asibiti be ma san wanda yake kan sa ba Allah ka bashi lafiya ta fada hade da amsawa amin.

Faridat kam kiris take jira ta fashe a fakaice ta bar dakin ta hango Muhasen da sauri ta je inda take ta fixgo ta.

"To munafuka me satar mijin wata to ina so ki sa a cikin ran ki AK yafi karfin ki ni Faridat na fi karfin in yi kishi dake wallahi ki daina ganin wai AK na son ki kiyi murna ni na  Faridat sena illata miki rayuwa gwara ma tun wuri kisan nayi shashasha kawai er gidan talakawa tsinanniya me suffar aljannu wallahi karya kike ki kwacen miji ta hankadata ta koma da baya ta doke hannun ta a jikin kujera.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now