52

285 23 7
                                    

RUDIN DUNIYA

KHAIRAT UP

PG47

Votes wattpad khairi_muhd

Wayyo Allah jama'a a taimake ni xa a kashe ni, na kawo kaina gun da za a kashe ni wayyo Allah duhu a cikin duhun taji an cafko hannunta tamakar za a fitar dashi daga kafadunta wani irin wawan ihu ta saki har numfashinta na sarkewa a hankali ta ga wani haske kamar ana kunna fitila idanunta suka sarke cikin idanun wata iriyar hallita zundumemen mutum shi kamar ma aljani kamar dodo ga wani irin gurnani da ake yi fuskar nan bakikirin idanun jawur dasu Rabin fuska a kone ta tartare GU daya kai wannan hallita dai da muni take ai wata kara ta saki saboda munin abun da tayi tozali dashi ta sulale a gurin sumammiya.

Dariya aka Bushe da ita ”duk wanda yayi kokarin shiga tsakanina da saffiya sena yi ajalin sa ya yi wuf da zee a hannun shi ya bar dakin”.

Tamakar an jefo  bola haka ya wurgar da zee a tsakar gidan su babanta yana alwala ita ko babarta tana hura wuta a tsorace suka mike jin Abu ya fado Tim.

Innallilahi wa inna illahir raj'un ×3

Malam zainab CE fa

Ya matsa kusa da ita ya tattabata saidai ba alamun nimfashi a tartare da ita, hakan ya kuma kada iyayyen nata a daburburce ya mike jikin shi na rawa yayi waje.

Jim.kadan ya dawo tare da wani saurayi Wanda yake tsantsan kama da zainab suka dauketa suka yi waje.

Asibiti suka nufa da ita koda likitoci suka dubata ta Riga ta mutu jiki a sanyayye suka fada musu ai yarinyar su ta mutu kuma zuciyarta CE ta buga kila wani Abu ne ya razanata ga kuma kanta ya bugu daga keya.

Jikin su yayi sanyi haka suka koma gida da gawarta aka yi mata wanka aka tafi kaita gidan ta na gaskiya kowa yana tambayar kansa *INA zainab take*?

Amsar da ta tafi tare da zainab babu Wanda yasan meya sameta.

Mahaifiyarta ta sha kuka kamar me tana son diyarta tilo dake ita kadaice mace yayyunta duk maxa ne guda Biyar ita CE ta shidda.

Koda saffiya suka ji labarin mutuwar xainab sun girgiza musamman ma jamcy ita ko saffiya kuka ta saka mun Shiga uku me muka yi wa wani yake illata mu ga jamcy ga zee saura ni Kennan ta fada cikin ta yana bada wani kugi kulululu.

Umman su ta CE bana San shashanci kinji ko ki shirya kizo muje muyi musu gaisuwa muyi mata addu'a Allah ya yafe mata kawai shi ne gatan da zamuyi mata ba kuka ba.

Jiki a mace ta mike ta nufi dakin mijin ta dake iya nan tambayar shi tayi yace seta dawo hade da bats kudin sadaka.

Muhaseen ma wayr umman ta yi mata ita me saurin kuka da tausayi kuka ta saki  ita ma taje gun hajiya tana kuka kamar ance baffan ta ne ya rasu.

Lafiya muha? Meya faru? .

Hakiya mutuwa aka mana.

Innallillahi wa inna illahir raj'un Allah ya jikan musulmi Allah sa ta huta tashi kije kin ji?.

Hijab ta saka ta yo waje daidai kofar fits sukayi kicibis da AK baki ya saki galala yana kallon muhaseen wani irin kyau ta mass tayi kiba ta murje kamar ba ita ba tayi haske sossai kamar me ga jiki da ta kara saidai hawayen da ya ga tana yi shi ya daga masa hankali.

Muhaseen meys faru?

Waje take kokarin fita amma ya hana ta ya mata rumfa ke me  haka wai ? Ina zaki a haka kina kuka?.

Babu ruwan ka jeki muhaseen bala na jiran ki.

Rabawa tayi ta bi gefen shi ta fits.

Binta yaso yi hajiya tace kul wallahi kana kara taku days da sunan bin muhaseen sena daga maka soko kawai.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now