43

259 25 0
                                    

*KHAIRAT UP*

*Rudin Duniya*

*Loading......*

*Pg 39*

*vote@wattpadkhairi_muhd*

Saukowa yake yi cikin nutsuwa da hankali,fuskar nan dauke da fara'a , sumar shi ta sha mayuka dan se zuba kyalli yake yi, ga wani irin sanyin kamshi dake bin inda ya wuce,dakakkiyar shadda ce a jikin shi irin coffee din nan,.

Kallon gaban shi yake yi yana jin wani irin dadi musamman ma da ya kalli fukar tauraruwar shi , .

Faridat ta maida kan ta gun Muhaseen wadda ta raina kanta dan kuwa Muhaseen akwai kyau ga diri me kyau musanman ma yanzu da ta saka fitet gown ta atampa sai ya fito da shape din ta ga gashin ta ya cunkushe a cikin dankwaki bakikirin ana hango shi ma.

Sai kamshi take me daukar hankali.

Ita din ma Faridat din cikin less take blue dinkin skirt da riga ta sha ado tayi kyau ba karya.

AK da ya nufo su yaji wani irin sanyi a ransa,dan shi mutum ne ma'abocin san ado da kwalliya,mace indai me yin kwalliya ce to AK na gun dan abun da ke dauke masa hankali a gun mace shi ne kwalliya da kamshi.

A ranshi yace " *MATAN AK*" kennan ina ji daku.

Zaman shi keda wuya Muhaseen tace "barka da fitowa ya ma'abocin kamala".

Dadi ya cika shi ya mata wani irin kallo da shagidadun idanuwan shi ya juya ga Faridat .

"Sannu Yaya AK kayi kyau."

"Wannan yarinyar ta gama raina ni, ta manta abunda ta min se yanzu zata...kwafa yayi amma seya basar "

Sannu Faridat ya kuke?

Lafiya lou yaya..

To masha Allah.

Gyaran murya yayi dan kuwa yasan yana bukatar hankulan su duk cikin su babu wadda taji zancen bikin shi ,dan yanzu haka bikin ma saura wata biyu kacan hatta lefe ankai suma nasu ya kawo yau wato kayan fadar kishiya.

Ina bukatar yi muku magana,sedai ina san ku bani hankulan ku,sannan ku nutsu,ku fahimce ni ku kuma bani hadin kai, abinda nake shirin fada muku me amfani ne me muhimmanci nima ba yin kai na bane ba haka Allah ya rubuta min a cikin kundin qaddarata ni da ku mun riga mun zama abu guda daya sedai ina bukatar hadin kan ku.

Duk da gaban su ya fadi babu wadda ta nuna alamun hakan a fuskarta gudun raini daga junan su.

Faridat , Muhaseen kuyi hakuri da abinda zan fada muku,zan fada muku ne badan bana son ku ba,komai ya faru da bawa daga Allah ne,kuma duk abinda mutum zeyi an riga an rubuta shi ba haka naso ba , kuma ba haka na tsarawa kai na ba sedai haka Allah ya rubuta min bani da yadda zan yi ne.

Yaya AK kawai ka fada mana,a kan ka dinga yi mana wannan kwana kwanar dan wannan kwanar da ka ke yi tana tsorata mu ne.

Haka ne ya Abdool kawai muna jin ka Allah jishe mu alkhairi.

Harara Faridat ta banka mata hade da yin tsaki bana san ana min shishigi a al'amura na wallahi.

Kiyi hakuri ba shishigi bane maganar ta shafe mu ni da ke ne shi yasa.

Oho ke kika sani .

Ehem!, nasan kun lura da cewa ana gyaran wancan part din?.

Dam dam kirjin Faridat ya buga ta ce a zabure "badai aure zaka yi ba?"

Muhaseen ita kanta seda taji faduwar gaba ta kura masa idanun ta.

Mazewa yayi irin ta jaruman maza,ya dake yace "Faridat dadi na dake saurin fahimta,haka ne aure zan kara kuma saura wata biyu an gama komai lokacin kawai ake jira."

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now