22

263 20 2
                                    

🌐 *Hikimah Writer's Association*

✍🏻 *Khairat Up*

🌐 *Rudin Duniya*

🌐 *Loading....*

🌐 *Pg 22*

*vote@wattpadkhairi_muhd.*

    Falo ya cika fa dankam da mutane an tarbi 'yan kawo kaya faram faram suma yan 'uwan su daddyn.

Umma ta gama cika da mamakin bakin nasu in bata yi karya ba gwal ne a jikin wuyan su da kunnuwan su da hannayen su, ga kuma akwatuna guda goma sha biyu masu dan banzan kyau, bata ma san sanda ta gyara zama ba ta ce dasu "sannun ku bayin Allah,"

Youwa sannu.

Anya ko nan ne inda aka ce kuxo?.

Murmushi gwagwon AK tayi tace nan ne mana ba nan ne gidan su Muhaseen ba?.

Nan ne kam.

To ai surukanta ne mu, mu din kanen baban shi AK din ne.

Ikon Allah.

Ita ko Sopie tsabar bakin ciki kuka ta fashe dashi ta bar gun jamcy ta bita.

Yafindon su Sopie tace ai yarta ce ,kukan rabuwa suke tun yau.

Aka sa dariya wasu ko Allah sarki suke fada.

Komai cikin raha aka yi da zasu tafi aka basu tukicin dubu hamsin sai kayan snacks da aka sa musu a mota.

Bayan wucewar su ne aka soma bubude kayan masha Allah,alhamdulilahi kawai ake fada dan kaya sunyu mugun kyau harkar ta manya ce, dan sarkan gwal hudu ne a ciki da zinare biyu designs masu kyau.

Sopie kam kuka kawai take yi an rasa gane kanta gaba daya.

Umma kam.kanta kumbura yayi murmushi kawai take zubawa,aka maida kays dakin da yake sama.

Se bayan an watse , umma ta sami jamcy na rarrashin Sopie tayi shiru.

Mekyau kinga kayan kanwar ki ko?.

Umma murna ma kike?.

Ya ko zan ki farin ciki kinga kayqn da aka tara mats kuwa masha Allah,ni mamakin da nake ma a ina ta samo hamshakin me kudi bayan nasan bata zance?.

Umma gaskiya ban ji dadin abinda kika ce ba.

Ikom Allah kamar yaya kenan?.

Kamar baki ga tarin dukiyar da aka mata ba,ni Muhaseen ba kowa bace bata isa ta kai matsayina ba,a kawo min kaya masu tsada ita ma a kawo mata kai ,in zauna a gidan daula ita ma haka? ,in sa in cire ita ma ta sa ta cire?,gaskiya da sake Umma ki hana auran nan.

     Gaskiya Saffiya kin ban mamaki da ke da Muhaseen duk ya'ya na ne,kuma son da nake nuna miki bashi ne yake nufin bana san Muhaseen ba ,ita ma ina son ta.

Sabida kinga an kawo mata abin duniya ko?

Saffiya , ki shiga hankalin ki fa ai dukkan ku abinda ya same ku ni ya sama ,kuma abinda ya shafe ku ni ya shafa sabida haka ki nutsu kar ki fada
Min magana,kuma ki daina yi wa er'uwar ki hassada dukkan ku daya kuke a gun mu dama buri na ku huta a rayuwar ku ,ku samu mazaje masu abin hannu saboda bana so ku dawama a cikin talauci kamar yadda nayi rayuwn babu ba.

Takaici ne yasa ta mike ta bar dakin ma.

Umma tace jamcy kinga kawar ki ko?.

Umma ayi hakuri zan mata magana kar ki damu. (Ita ma ranta fal kishin su Saffiya sboda sun samu daula ita kuma ko oho.)

Da magariba kuwa Muhaseen ta shigo garin kano kuma da gajiya a jikin ta,napep ta shiga ta masa kwatancen inda zata.

   Suna tafiya ne AK ya kirata da fara'a a kan fuskarts ta dauka.
    Salamu alaikum
Wa'alaikum salam masoyiya ta.
   Da fatan kana lafiya?
Wallahi gani nan ne dai bana jindadi.
Subahanallahi,meya same ka?.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now