18

264 21 0
                                    

🌐  *Hikimah Writer's Association.*

🌐✍🏻 *Khairat up*

🌐 *Rudin Duniya*

🌐 *Pg 18*

🌐 *Loading*

   *vote@wattpadkhairi_muhd*.

    Da magariba suka sauka garin kano lafiya lou, Dawaki road suka nufa inda gidan shi yake,a matukar gajiye yake hakan yasa da confidence din shi ya karasa gida a tunanin shi Faridat na nan, tun daga corridor yake sallama sedai me aikin su olu ce fito tana masa sannu da zuwa.
   Amsawa yayi ya ce ina madam?.

Taje unguwa ne.

Unguwa?.

Eh!.

Ok koma gun aikin ki.

Da kan shi ya shiga ya hada ruwan wanka, yayi wanka ya fito ya canja kaya, sai da ya dan sha green tea tukun ya dau key ya fita yana duba agogon shi karfe bakwai takwas saura gyada kai kawai yayi.

Gidan su yaje.

A falo ya tarar da hajiyar su, ta ko fadada fara'arta tace yanzu kakr tafe?.

Wallahi,ya tsuguna har kasa ya gaida ta amsawa tayi cike da jindadi da kulawa irin ta uwa tsce ya hanya kuma?.

Alhamdulilahi hajiya ya kuma kadaici?.

Uhm gani nan dai,dazu ayman ya koma ai yace min kunyi waya kace ya koma akwai aiki.

Wallahi hajiya wasu client din mu ne suka zo da wasu samples ganin ni bana nan yasa na aika shi sedai nima ina ganin jibi zan koma dan mun bar aiki pending sossai.

Gaskiya ne.

Nan ta kira me aikin ta Harira.

Na'am hajiya.

Ki kawo wa oga abinci.

To hajiya.

Ta dauko wasu flask masu kyan gaske cikin tray me kyau tasan ba wani san zaman dinning yake ba sabida haka a gaban shi ta ajiye masa.

Ya mata sannu.

Nan ya bude sakwara ce miyar agushi ta sha nama a ciki da dry fish se kamshi take yi.

Seda ya gama tas ya wanke hannun shi a cikin bowl din ruwan wanke hannu, Harira tazo ta kwashe yace ta dafo masa Lipton da kayan kamshi.

To.

Kan kujera ya zauna yana ajiyan zuciya.

Ashe kuma aure zaka yi?.

Uhm hajiya waya fada miki?.

Daddyn ku mana ya ban kudin hado lefe na gani na fada.

To abun yazo kennan?.

Ban gane ba?.

Nidai yace min zan auri er abokin shi amma wallahi ban dauka so early bane ba.

Aiko ka shirya dan a yanda nake ji ma kaman next month ne.

Gaban shi ya buga hajiya wallahi ban san ta ba, ko kina da labarin ta?.

Aa son ni kaina yaki fada min wace ce , ina ta mamakin boye min ita da yake yi,sedai koma wacece Allah yasa me tarbiya ce kuma wadda zata kula da kai.

Amin.

Hajiya gaskiya zan fada mishi bayan bikin ba wani jimawa zan yi ba zan yi aure nima na ga wadda nake so.

Tayi murmushi irin nasu na manya tace to kace mata hudu za kai?..

Dariya yayi hajjaju kennan ko kadan ban da ra'ayin auren mace fiye da daya ba sedai KADDARA ta riga fata kuma dole in muku biyayya.

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now