30

284 20 0
                                    

🌐 *Hikimah Writer's Association*

🌐 *Khairat up*

🌐 *Loading.....*

🌐  *Rudin Duniya!*

🌐 *Pg 30*

*vote@wattpadkhairi_muhd.*

Mekyau ta ce "duk ku barni da ita nasan maganin ta,ni zan koya mata hankali naga kanta yana rawa saboda ta yi aure to ni zan nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane ba tayi tsaki."

Ahayee wai namiji da suna hajara yadda kika hau haka zaki dirgo kasa wanwar karamar alhaki da mu kike xancen.

Kawata yau kam ki basu mamaki ni nasan Alhaji yana ji dake kece fa wadda ya bawa mota katuwa,ya baki driver,ya baki waya,ya baki kudi,ya baki duk wani abun jindadin rayuwa kece fa Saffiya Gimbiya Mekyau waya isa ya ja dake ya kwana lafiya? ,waya isa ya ce bake ba? An buga dake an bar ki,kinga jiya kinga yau kin zubda kananan maza a kasa wanwar in sun gan ki matsawa suke yi su baki hanya.

Wani kumburi yazo mata ta hade bakin ta game da turoshi gaba ta gyara zaman kafafuwan ta tana murmusawa, ita ala dole an kurantata.

"Hmm! Munafuka zan ga yadda zaki zauna a gidan naki lafiya ni kika munafunta ai shegia, wallahi se na ga bayan ki er kunama inji Jamcy."

Zee ko da iman zunde suka yi mata ta keya suna dariyar keta.

😔 o duniya ina zaki damu?.

Karfe hudu da rabi Hajiya tazo danlami ne ya kawo ta da me aikinta suka kawo pepper chiken nan suka zauna da Umma suna ta hira kamar an saba kuma Muhaseen taji dadin hakan se taji tana kara ganin girman Hajiyar.

Karfe shidda saura aka kawo lefen Mekyau,kuma alhamdulilahi kaya masha Allah sun zubu kuwa ita ma seti biyu sedai ba irin na Muhaseen bane gwal dinma guda daya aka sako mata dankareriya mekyau,ana ta zuzuta kaya ,mutane suna ta cewa yaran malam Habu sun yi goshi kowacce gidan manya ta koma ikon Allah ba wanda ya cire tsamani da rabo.

Bayan sun tafi Hajiya ma ta ce zata wuce, Muhaseen ta mike ita ma, ina zaki ne Muhaseen?, Hajiya wai mu tafi tare tunda an gama.

Aa zauna ki kwana gobe se ki dawo ki taya yayar ki murna duk da rowarta ake mana ni ban taba ganin ta ba.

Lah bara na kira miki ita Hajiya.

To.

Da dan gudu2n ta taje dakin Saffiya ta tarar da ita cikin kwalliya me kyau.

Ke kuma fa? .
Uhm dama yaya Hajiya ce tace kizo ku gaisa inji Umma.

Wace Hajiya?.

Siruka ta ce.

To se me?.

Wai da ku zo ku gaisa.

Ban zuwa uwata ce?.

Kai yaya...

Jeki Muhaseen tana zuwa .

To.

Ai kinsan bazan je ba ko?.

Saboda me?

Kawai.

Ke dalla sokuwa ce ke kika sani ko ki samo yan cash kinsan masu kudi fa akwai sadaka.

Yanzu ai nafi karfin haka sedai na bayar.

Naji ni ina so ban fi karfin haka ba, in ta baki ki bani.

Mtsw mayya kawai da kyar taje.

A kan kujera ta zuna ta gaida Hajiyar.

Ta amsa mata da fara'a kuma ta mata Allah sanya alheri.

Tace amin dan.ita ba wani kunya taks ji ba.

To mi ma tafi.

To ki gaida gida Haj mungode.

Lah ba komi ai mun zama daya.

Hka ne se da safe Allah huta gajiya.

Amin.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐

*India*

Sossai AK yake samun kulawa a asibiti  kuma an dora shi kan magunguna masu kyau.

Ana saura sati daya aikin da za ayi Daddy ya ce su Hajiya su fara shiri ayman zezo su tafi tare.

Dama an gama wa Muhaseen cuku cukun visa da duk wani abu da ake bukata na tafiya.

Har sallama suka je suka yiwa su Umma.

Wai ranan ran Saffiya kamar wuta wai Muhaseen zata keta hazo ta riga ta zuwa wani garin wallahi Allah ya isa na an cuce ni yasin har guntuwar kwalla tayi.

Ayman ya dawo 9ja ,dan washe gari da safe zasu wuce ta lagos zasu bi a can zasu hau jirgi so doublr plane zasu bi.

Saffiya kuwa tunanin ta daya meya sa AK be kira ta ba bayan ya amshi num ta to me yake nufi? Bazata mori kudin shi ba? Ko irin selfie din nan bazaya yi dani ba na dan dora a duniyar sama a gan ni da young tycoon.

Wayarta ta duba wai ko zata ci karo da ko messge din shi ne.

Sedai kash bata gani ba tay ta zuba tsaki tana harareharare kila ma ya manta dani dan masu kudin nan makaryata ne munafukai ne wallahi.

  Washe gari suka nufi lagos da daddare suka tafi india harda Muhibbt da mijin ta dama zeji wani bussiness garin se suka wuce tare tafiya ce aka yi ta irin ta lakwas dinnan saboda ana fargabar aikin da za ayi wa AK.

Kwana suka yi dan 24hrs ne tafiyar.

Daddy ne ya tarbo su basu wuce asibiti ba gida ya kaisu seda suka yi wanka da sallah suka ci abinci tukuna suka nufi asibitin.

Tun daga bakin kofar shiga gaban ta ke dukan uku uku hakan nan taji sabon feeling na daban wai meke faruwa da ita duk sanda ta doshi gun mutumin da aka ce mijinsu ne seta ji wani iri to meyasa ina da wani connection ne da shi.

Tofa muje zuwa fan's ko ince team *AK*

Share
Like
Comment

   RUDIN DUNIYAWhere stories live. Discover now