SILAR GIDAN AIKI

3K 184 3
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

~It is better to be hated for what you are than to be loved for what you are not.~

*PAGE 0⃣6⃣*

Mubin ne a tsaye sai huce yakeyi, ranshine yai matukar baci, sai kwafa yakeyi

Faeez ya kalle faeeza yace what did you understand? Ta rufe littafin dake hannunta tace I don't understand anything, meyene plz tell me

Faeez ne yace ke kwalwarkarki bataja Sam,  yanzu baki gane ya mubin na son Nazeefa ba? Kara tsuke fuska tayi tace" Allah ya kyauta yayana yaso yar aiki, yar aikin ma kaskantatciya

Faeez ne ya bita da kallo shi yana mamakin halayyar yan uwanshi, halinsu Sam daban danashi, meye aibun Yar aiki, Karamar tsaki yayi sukaga mubin beda shirin fitowa suka bude Kofar motor suma sukai cikin gidan

   A tsakar gida suka samesu shida Hajiya duk a tsaye

a daidai lokacin baba me gadi ya shugo da sauri yana afuwan Oga Mubin

Cillomai key yayi yace" aika iya mota kaje ka shugo da ita Sannan yasa Kai yayi pallow Suma suka bishi a baya, kowa da abun da yake ayyanawa a zuciyarshi

Baba me gadi jiki na rawa yaje ya bude get din  ya Shugo da motor sannan Ya kawo mai key din

Tunda ya shugo ya shige Daki becewa kowa uffan ba, Kulle dakin yayi yana Tinani barkatai

*********
Misalin karfe daya Saiga Nazeefa ta bude get ta Shugo, tafiya take ahankali kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, Ta window ya leko yaga itace Sai yaji yadan sama natsuwa but heart dinshi na bugu fast fast (dasauri dasauri)

Mik'ewa yayi ya fito pillow  adaidai lokacin itama tana stepping legs dinta, Hada ido sukai dashi yaga ta kalleshi ta watsar

juyawanta tayi zata shiga dakinta janyo Mata hijab yayi, da sauri ta juyo

Kallon idon juna sukai sosai na kusan 1mins sai kuma ta saukar da idonta

Mubin yace" dazu motar uban wa kika hau, Dama ke yar iskace ko, Sainayi maganinki, to ba anan gidanba, Sai bambami yake ta Mata

Ajiye school bag dinta tayi kamar zatai tambe, ta sa hannu a kugu" Tace" karka kara zagina, Kuma niba yar iska bace sedai Kai

Mamakine ya cika shi sosai, a ranshi yace Wanna yarinyar akwaita da taurin Kai, takaicine ya isheshi yace" village girl kawai, Dan ansamu ankawoki zaki Ma mutane iyayi inba iskanci kukeje yiba nameye da shiga motor mutun

Maganarshi tai mugun 6ata Mata rai tace" eh din, anyi iskanci, Nan dai suketa fada har hajiya taji hayaniyarsu ta fito

"Tace me ya faru"

Nan Ya hada Karya da gaskiya ya fada mata yace" dazun ne naje daukarta a school wai tana ganina taje ta shiga motor wani Dan iska kowa sai kallonsu yakeyi, Ina tazo muje mutumin sai d'aga mata gira yakeyi, Yana tambayarta ta sannine, bodar bakinta tace" wai bata ta6a ganina ba shine nazo ina Mata fada tanamun rashin kunya

Nan ma Hajiya ta hauta da fada danme zatahau motar wani mutun gashi ance sai kallonsu ake!

Zata bude baki kenan tai magana tajiya" tace karkicemun komai yawancinku yan Kauye haka kuke da kunzo birni sai labari ya Chanza

Kwallane ya cika Mata ido bayanda zatai kawai tace" to Hajiya bazan karaba inshaa Allah ayi hakuri,

Tajiya tace" yauwa Ko kefa! Hajiya ta koma Upstairs ta kwanta itama ta Shiga daki ta huta Dan ta gaji sosai, Shima Mubin ya shiga daki yai wanka yasa blue shadda yayi kyau sosai Ya tafi masallaci

kamshine ya bada ko Ina da turaran da yasaka, Bike (mashin) dinshi ya dakko yahau yaje masallaci ya dawo

_Nasan fans Zaku kosa kuji waye wannan mubin nan kuci gaba da biyoni_

Sallamar wata budurwace najiyo nai sauri na duba bakin gate naga wata kyakkyawar yarinya Rike da trolley a hannunta, Tasha glass me suna (Cat eyes) tahowa ta farayi ahankali. nima na bita a baya......

Muje Zuwa

Please Comment and VOTE And Also follow me on wattpadd

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now