SILAR GIDAN AIKI

1.4K 68 5
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

   *Ina ganin ruwan comments dinku da sakon alkhairi...Ina godiya sosai💋❤*

*PAGE 5⃣6⃣*

Nazeefa ce tai dariya tace Ameerah ba kama bace nice! Rungume juna sukai suka shiga gidan

   Iyayan Ameerah Rik'e baki sukai sukace Nazeefa aure kikai ne ba labari, Smiling tayi ta tsugunna ta gaisheshu tace a'a Mama, Ameerah Tace mu shiga ciki mana Tace toh
   Daki suka shiga ta kawo Mata ruwa tasha, Ameerah kam binta da kallo tayi kamar bata taba ganintaba, tace ikon Allah kinga yanda kika koma kuwa? Kamar bakebe meye sirrin?

Nazeefa tai smiling tace it's a long story amma bari kiji, Nan ta gyara zama ta kwashe labarin komai tun barinta gidan aiki har izuwa yanzu da take bata labari

Ameerah Tace ke Dan Allah cikin Ihu!  Nazeefa Tace Wallahi dear, Ameerah fita tai ta kira mamanta da kishiyar mamanta take basu lbarin Nazeefa taga iyayanta

  Alhamdulillah sukace mun miki murna, Ashe ke yar gata ce! Ikon Allah kenan ashe gidan yan mahaifinki kikai Aiki, Allahu Akbar

  Nazeefa Tace sosai, kam, Sukace sannu yar nan, Gaskiyane duk Wanda yai hakuri tabbas yana tare da nasara! Sannan suka fice a dakin suna mamakin Lamarin nan

   Bayan fitarsu sukaci gaba da hiransu na kawaye, dama zancen yan Mata be wuce na samari Lol

Ameerah tace ansamun rana fa kafin azumin nan za'ai bikina

  "Nazeefa ta riko Hannunta Tace ke Dan Allah tace da gaske nake, Nazeefa tai murna sosai Tace" wazaki aura?

Tace wani doctor ne Allah ya hadani dashi, Allah ya dauramun sonshi sosai! Nazeefa tace Wow Allah yabarku tare, Ameerah Tace Ameeen!

   Sunsha hira sosai, Zasu fito kenan wayar Ameerah yai ringing! Tana dubawa taga My Doctor, da murmushinta tai picking yace hello my princess

Tace hea Likita na ya kke, yace I'm fine yace ganinan a kofar gida Tace OK ganinan zuwa da wata Frnd Dina Ku gaisa yace OK!

Yana kashe wayar ahankali yace Allah yasa ta fiki kyau na kwaceta!

Yana jingine a jikin kofar motar suka fito!

Tun lolacin da ameerah tace ga kawarta nan ta zatazo su gaisa taji gabanta na fadi

Fitowar da zasui kenan Taga Dr Bashir abokin Mubeen! Kutamah tace aranta Tana karemai kallo

    Shi sam daya kalleta sau daya ya rasa gane ina yasanta, but yasan confirm yasan face dinnan

    Murmushi ya Fara mata, Ameerah Tace sannu da zuwa ga Frnd Dina nan Ku gaisa!

Washe baki ya farayi yace sannu baiwar Allah, Kallon fuskar Nazeefa da zasui suka ganta a tsuke ta hada rai, Dakamai tsawa tayi Tace Malan Dakata! Macuci Kawai

Kana nufin baka ganeni ba? Dr Bashir jin kirjinshi yayi ya Fara bugu da karfi, muryanshi na rawa yace banganekiba

Wani murmushi tayi tace tabbas bazaka ganeniba, nice nan Nazeefan Mubeen a da kenan amma fa!

Zare ido yayi Yace Nazeefa innalillahi.......

Tace wato ka lallabo ka yaudararmun kawa kamar yanda mugun Abokinka ya yaudareni KO? To karyanku ta kare!

Ameerah dake tsaye tana jinsu Tace meye haka kenan dama kunsan junane?

Nazeefa Tace eh nasanshi through Mugun Brother na mubeen,

Sannan ta kalle Dr Bashir Tace halinka yaja maka, seda ka gala lalata yaran mutane sannan zaka lallabo wajen saliha?  Ai baka isaba, good wifes are for good husbands,  indai Ina nunfashi bazan taba bari ta aureba koda kuwa tana sonka! Tana magana tana hawaye tace ba abun da zance maku sedai ince Allah ya Kara shiryaku

   Dr Bashir ya tsugunna yana Mata magiya dan Allah tayi hakuri wallahi yanzu ya tuba, Tace tuban mazuru ba, kana daya daga cikin wanda ya ziga mubeen ya yaudarene sannan ta fashe da kuka

   Ameerah Tace kawata kidena kuka! Ta kalle Dr Bashir Tace kasani inasonka Amma bazan boye maka ba nafison kawata fiye dakai saboda Ashe dakaine aka hada baki a ka cutar da ita? Gashinan kunfara gani tun yanzu ai sukai Mai tatas Sannan suka shiga gidan madadin Nazeefa ta tafi gida

Sororo yayi a waje ya rasa mekemai Dadi, Ashe munfunci zuwa take ta dawo kanka, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun ya fada, Dandan me karfin haline da kuka zaiyi Sosai, Shiga motor yayi yace dole na nema mubeen duk inda yake

   Koda suka shiga gida iyayansu suka gansu wani iri, tambayarsu sukai meya faru?

Nazeefa cikin sheshekin kuka wani hikima yazo Mata Tace mayaudarine, munyi alkawarin aure na nemeshi na rasa Ashe Wajen Ameerah ya dawo

Maman Ameerah Tace Ahab, ni dama tun farko ban aminta dashi ba, yarinyar nan ta kafe, Ai yanzu kinji da kunnanki ko?

Itama tanta a bace Tace mama naji, Allah ya Kara mana tsari da irinsu, Zan kirashi yazo ya kwashe kayansa na sa Rana! Sukace gwanda

   Su Nazeefa shigewa daki sukai, sunata wa junansu jajee






MUJE ZUWA

FOLLOW
VOTE
COMMENT

#Ummieyxeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now