SILAR GIDAN AIKI

1.5K 90 3
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

_This page goes to you My *REAL KHADY💜* kiyi komai ba komai bane ki huta Dear....Allah ya Kara miki lafiya ya raya mana yaranmu_

*PAGE* 3⃣0⃣

A tare suka had'a baki sukace wacece ta haihu kuma? Hajiya bilkisu dariya tai musu tace" ba wacce ta haihu, baridai Ku ganta yanzu nayi yarinya wacce zata ebemun kewa, Alhaji dake kan kujera yanacin Apple shidai binsu da kallo yayi

    Hajiya bilkisu ne ta kwalla ma wata baiwa kira a cikin gidan tazo ta tsugunna a gabanta tace" mata kije dakin Chan na yan Mata ki kiramun Nazeefa, angama tace, Minti 2 saiga Nazeefa ta shugo dakin sanye da dogon hijab dinta, se kamshi takeyi, dukansu saukar da idonsu akanta sukai, Hajiya Bilkisu tace" kungantanan KO?

Nazeefa d'ago Kai tayi Dan kallon samarin nan biyu suma at the same time suka Kara Kai idonsu gunta, tana kallonsu taji wata muguwar faduwar gaba, lalle suna kama sosai kuma fuskarsu tai mata kama da wani! Nan take ta nema natsuwarta ta rasa se dabur dabur Takeyi

Hajiya ne ta Lura da ita tace" lafiyarki kuwa? Girgiza Kai tayi tace" kantane ke ciwo, Sannu tace Mata sannan ta kara da cawa AI dole kanki yai ciwo yanda kukasha hanya, eh tace mata but gabanta na ci gaba da faduwa

Samarin nan biyu suma ko wanne da abun da yake sakawa a ranshi, lalle yarinyar nan dakyau take, ko Ina suka samo ta oho

Nazeefa ta shiga tinani taji Hajiya Bilkisu me gadon zinari tace" ga yarana nan Su biyune kadai maza babban yayansu tayi aure, So kome kikeso Ki daukesu tamkar yayyinki kome kike so ki tambayesu, sannan ta koma gunsu tace" ga kanwa na maku Ku rik'eta amana, Sukace inshaa Allah

Sannan ta kalla Nazeefa tace kije kice Su Suhaila Su baki magani akwai achan dakin, Allah ya Kara sauki tace" Ameen, suma sukai Mata sannu tace" yauwa

     Bayan Nazeefa tabar dakin ne Hassan yace" Ina Kika samo ta? Hajiyarsu ta murmusa nan ta gyara zama ta basu labarinta tsab, sun tausaya Mata sosai sannan sukace zasu rik'eta amana

Bangaren Mubeen kuwa biki nata matsowa iyayanshi sun gama shirya komai part din Da zai zauna an Kara gyarashi abun se Wanda yagani

Tun bayan tafiyar Nazeefa Mubeen be zama a gida ya rasa abun dake mai dadi, Nadama kam yayi na cutar da rayuwar nazeefa da yayi, shi tsoronshi Allah yasa ta fada hannun nagari Dan sonta da tausayinta ya mugun Kama shi

******
    Kwance tashi asarar Mai rai bikin Mubeen da Haleema yau saura kwana uku. Mubeen kam in banda bakin ciki ba abun da yakeyi, dukda iyanshi sunkaishi wajen boka shi Sam har yanzu be taba jin sonta a ranshiba, kawai umurnin iyayene

Yana zaune yana tinanin Allah yasa lokacin bikin a tura shi wani course Cyprus Dan sunce Cikin week dinnan zasu turasu text din Haleema ne ya shugo kamar haka _angon kwana uku hope you're fine plz ya Kama ta kazo fa muyi maganar bikin Mu, cos inata kiran numbernka baka picking_

Ya na gama Karantawa ma yai switch off din wayar Dan shi kadai yasan abunda yakeji a zuciyarshi

Bangaren Haleema kuwa shuru shuru bataga reply ba, ta Kira numbern Taji a kashe, Hawaye ta Fara ta wuce direct wajen mamarta ta zube a gabanta tana kuka, Maman ne tace what happen Amarya

Haleema cikin Kuka tace Mum Sam Mubeen be sona kinga yaushe rabon da yazo gidan nan ni gaskiya na fasa auranshi,

Maman tane ta zare ido tace bakida hankaline zakice kin fasa auranshi? Ke kinsan tanadin da nakeyi? Kar in sakejin irin wannan maganar

Zunburo baki tayi ta tashi Cikin shagwaba ta shige dakinta ta haye gado tana kallon wayarta hawaye na zubo Mata!

Tino da saurayin da suke shakatawa tayi, number shi tai dialing taji number busy, takaici ya kara kamata

Tsaki tayi ta sake dialing for the 2nd time ya dauka muryanshi na rawa, ranki ya Dade yace" tace tare da naka ya al'amurane?

Yace se ahankali fa inanan inata missing dinki, murmushi tayi tace realy? Hararar wayar yayi ya wani tabe baki yace" da gaske nake!

Tace karka damu, inanan tare dakai, Yace OK Madam, nace ba!

Tace mene? Yace Zan sama koda 10k? I'm broke ne, tace karka damu masoyina yanzun nan zaka alert I love you ta kashe wayar

Kallon wayar yayi yace" Wahalalla kawai, da ba kudi kike bani ba kina tinanin da yanzu muna tare ne mtsww , Alamun message yaji ya Shugo Mai yana dubawa yaga alert na 30K wani ihu yayi yace yau akwai zuwa club, (Allah) ya shirya

KO thank you be ai ka mata ba yahau tsohon bike dinshi se ATM




Thanks for your time










More Comments plz

*UMI33Y X33Y*💋

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now