SILAR GIDAN AIKI

1K 142 10
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad #Freshummieyxeey*

_This page goes to my Wattpad fans, Love you so much❤_

*PAGE 8⃣9⃣ SEMI FINAL*

Kai Nazeefa asibiti sukai, Koda sukaje chan zazzabine me zafi ya rufeta, Gwaje gwaje akai mata Sannan Ta samu tadanyi bacci

   Bangaren Ummie kuwa koda suka dawo gida kakus sata agaba tayi sosai tanata Mata fada, Ummie duk taji ba da dadi ga mutuncinta daya zube gaban su hajiya, ba Wanda ya bata shawara ita da kanta tace zata koma gida lol Dan wannan abun datai da kunya

    Washe Gari, Umman Nazeefa ce tazo ta zauna da ita saboda mansur ze fita wajen aiki, koda yaje duk bayan 20mins yake Kira ya jikinta sai Umma tace da sauqi
   Haka ya dinga Kira har ya gama aikinshi sannan yai resigning letter yakai musu, sukaimai fatan alheri Dan Dama cikin week dinnan Da zamu shiga zasu tafi Chan garin

   Ya rabu da kowa lafiya wajen aikinsu sannan suka nuna dai basuji dadiba Dan yana daya daga cikon masu kwazo na wajen aikin

    Koda ya dawo, nan nan ya farayi da matarshi, har Umma tadanji kunya Dan soyayya yake nuna mata a gaban kowa shi ba abun daya shafeshi, Umma kuwa komawa gida tayi Dan bazata iya ganin wannan soyayyar tasu ba
   Chan da yamma result ya fito Nazeefa is positive tanada Ciki, Kara kallon result din yayi yace Alhamdulillah, tana kwance yakai mata wani irin kiss yace Maman boy ko baby

Binshi da kallo tayi tace uhmmm, yace kinada cikifa! Wani yunkurin tashi tayi yai sauri yace nooo kwanta babyn baby, maman baby kuma, wani murmushi tayi ta daga hannu sama tace Alhamdulillah... Murna sosai yayi

  Kiran mahaifiyarshi yayi tace har muna shirin zuwa, Yace Mum albishirinki? Tace goro, dad ne ya kalleta da tace goro yasan albishir za'ai Mata

Yace Nazeefa nada ciki, mik'ewa tayi tace Alhamdulillah Alhamdulillah

Dad yace meya faru kashe wayar tayi tace Alhaji tashi mu tafi Nazeefa nada ciki, Kai Alhamdulillah.

Baban Mansur kuwa shima daga hannu yayi yace Alhamdulillah, Allah ya inganta nima nace Alhamdulillah Ameen

    Tashi sukai suka tafi hospital din, koda sukaje su mansur ne kadai, a dakin, Kiran Umma hafsatu yayi ya sanar da ita, kai Alhamdulillah tace itama baban Nazeefa na zuwa tamai albishir shima yace Alhamdulillah kowa yayi murna matuka

    Dr Ne ya shugo ya basu supportive drugs (magungunan) dazai Kara tema ka Mata, yace kuma ta dinga yawan shan ruwan gishiri Da sugar, Sukace sungode

  Gida suka wuce, mansur kuwa se kiran yan uwa da abokan arziki yake tayi yana sanar dasu, kowa sedai yace Alhamdulillah, Allah ya inganta Amen

   Tunda suka dawo gida daidaida cukali Nazeefa bata ta dauka komai Mansur yake Mata

   Hajiyar Mansur itama kullun seta Kira kusan sau 7 tana tambayarta ya jikin nata, tace da sauqi

  Chan Gidan sarkin yobe kuma, An gina ma su Nazeefa katafaren gida da inda Su hassan zasu zauna da matayensu, Su Hajiya kuma suna tare da su hajiya asma'u da sarki Chan zasu zauna tare

    Ana Jibi zasu tafi Nazeefa ta roka beloved husband dinta tacemai Dan Allah zataje gidansu ta kwana tayi bankwana da Iyayanta, Qin yarda yayi wai zata barshi Shi kadai wazai tayashi kwana

    Hajiya ta Kira tace Dan Allah taiwa mansur magana tanaso taje gidan ummanta ta kwana, tace ok diyata ba matsala, Suna gama waya ta kirashi tace ya barta
   Aikuwa dakyar ya barta, kafin yakaita kuwa yasha shawaba mansur ya dawo kamar wani karamin Yaro, kwana day an nan dazatai ji yake kamar zatai shekara
  Hakanan duk wasu abubuwa da takeso ta kwashe takai wa mamanta Dan chan gidan Sarki sabon zubi za'ai musu, ciki harda mota ta Kai gidansu, sannan aka sama wani Dan amana yana kula da inda Nazeefa ke zuwa aiki

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now