SILAR GIDAN AIKI

1.2K 78 6
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

   _Awwwn My fans I'm back zamuci gaba da gashi daga inda muka tsayaaa...One love💎_

*PAGE 6⃣9⃣*
  
Mum mansur ne tace Nazeefa fada mana meya faru?

     Nazeefa ta Fara ba mum din Mansur labari tace mum kintuna time din Da mansur ya kawoni gidanku?
   Mum Mansur tace na Tina Nazeefa,

Nazeefa tace ai daga gidansu nake, ta nuna suhaihat da Jamila tace Su sukai mun sharrin wai na sace gwalagwalan Hajiya, Mum Mansur dafa kirji tayi tace Subhanallah, how comes kikaje gidansu? Nan Nazeefa ta bata labarin Gwagwar mayar da tasha agaban Su suhailat, jikinsune ya fara rawa, Hassan kuwa harararsu yayi yace munafukai

   Anan dai Nazeefa ta basu kaf labarinta, Sarki yai shuru yana nazarin Wani Abu

Hajiya Bilkisu kuwa hawayene ya zuba a idonta, Tace yanzu kina Ina Nazeefa?

Nazeefa tace da temakon Mansur naga iyayena Ina tare dasu,

Mum Mansur kuwa ta qarajin tausayin Nazeefa Ashe yarinyar Tasha wahala, Mum mansur ne tace Hajiya Bilkisu infada miki Ashe babanta babban Dan kasuwane qilama kisanshi, Wani Alhaji Nalado Wanda duk garin nan shine Me shugo da flour mekyau Chan shekarun baya? tace eh Naji shine mahaifinta? Mum mansur tace shine kuwa, Sarki innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yace, yarinya kiyi hakuri ki yafe mana

  Hajiya bilkisu ma Matsowa kusa da ita tayi tace Yar Mu please kiyafe mana, Wani Ajiyar zuciya Nazeefa tayi idonta ya cika da kwalla, tace nayafe maku Hajiya ai ba laifinku bane laifin Jamila Da suhailat ne, Duk Su suka sa muku kiyayya na a zuciyarku

   Nan Jamila da suhailat kunya ta rufesu kamar su nitse kasa, Sunataba Nazeefa hakuri suma, Hussaini yace munafukai a chan gida bana tabajin kuna fadan akan kun siyar da wani gwal ba kuna fada akan kudi da nazo na tambayeku ai nunamun kukai ba komai, yanzu gashinan Asirinku ya tono

Nan suka Fara inda inda munafukai sak cos magana ma sun kasa,

Mansur ne yai wani ajiyar zuciya gaba daya hankalinsu ya koma kanshi, Kakarin amai yake tayi shi beyi aman ba kuma be dena kakarin ba

Seda aka Kira doctor sannan ya dubashi yace sunyi yawa a dakin a arage surutu, kuma yanason bacci Dan haka gaba dayansu suka fita, Reception suka sama waje suka zauna dukansu kowa da abun da yake sakawa a zuciyarshi

   Nazeefa ce kadai da Abdallah a dakin, Riko Hannun Mansur tayi tace please ka kwantar da hankalinka, kar abunda kaji sunmun yasa hankalinka ya tashi, ni na yafe musu har abada kaji habeebe nah
    Murmushi yayi yace are you sure tace yes, ni kawai abunda nakeso dakai shine ka kwantar da hankalinka I'm yours forever inshaa Allah, Kara riko hannunta yayi ya damke sosai yana mata wani irin kallon ga eyes dinshi kamar yanajin bacci,

Itama kashemai ido tayi tace Sorry my love, KO zakasha ruwane, wayau tamai cos rike mata hannun dayayi gam tasan be daceba

   Daga kai yayi ta dakko Mai ruwan Swan medan sanyi ta sa Cup ta bashi,

Yasha sosai yace love naji Dadin ruwan nan fa cos kirjina har yadanyi sanyi, tace yeah nasan kanada bukatane Kuma KO lafiyanka lau is good kadinga shan ruwa akai akai
   Bin lebanta da ido yayi yace Wow hakane gimbiyata

  Tace how are you feeling now yace Alhamdulillah tace Masha Allah

Abdallah ne na gefe yana kallonsu, Tsantsan so sukewa junansu, Nazeefa a hospital din ta wuni se Chan yamma ta koma gida

    Koda ta koma Gado ta fada se tinanin MAN Dinta takeyi, time din kuma Su mubeen sun koma Chan gidansu

   Umma hafsatu ne da malan nalado suna Zaune a falo suna shan A.C se TV a kunne kana ganinsu kasan suna cikin jin dadi
   Nazeefa ce ta fito sanye da doguwar riga kanta ba dan kwali se wayarta a hannu, Gashin kanta ya kwanta, Zuwa kusa da ummanta tayi tace Dan Allah gobe inaso gobe kuje Ku gaida Mansur please

   Malan Nalado ne yace mamata ina dankwalinki taba kanta tayi tamarairaice kamar Wata karamar yarinya tace laaa bansaniba Ashe ya fadi

Babanta yace OK kidinga kula dai, Kuma Allah yakaimu goben zamuje da murna ta tashi ta shige Daki ta fada kan gado, kawarta Ameerah ta Kira tace kee nadawo fa, gobe pls ki shirya zamuzo Mu daukeki Love of my life ba lafiya

Ameerah tai wani ihu tace yaushene nai tinaninki Ashe kindawo, Allah yakaimu goben, Kawata Tace Ameeen

Nazeefa kuwa bayan ta fada gado, lafewa tayi ta bude gallery din wayarta, kallon pics din mansur ta fara tsintar kanta tayi tana smiling sosai ahaka bacci ya kwasheta


Muje Zuwa.

Don't forget to FOLLOW, VOTE AND COMMENT



*THANKS yours Ummieyxeey*

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now