SILAR GIDAN AIKI

1.2K 82 2
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*Dedicated this page to you my Nazeeephy I love you to the moon and back*❤💎

*PAGE 6⃣8⃣*

   Kowa a dakin tsuru tsuru yayi yanason jin wani dangantaka ne ke tsakaninsu

   Nazeefa ajiye jakarta tayi, Sannan tacewa Abdallah yaci abinci kuwa? Yace aa rabonshi dacin abinci tun jiya fa

OK tace Ina abincin? Aka nuna Mata, dakkowa tayi ta fara feeding dinshi ahankali, kowa abun ya Bashi mamaki, seda ta tabbatar ya koshi sosai sannan ta bashi ruwa hade da magani tasha tace please yana bukatan hutu kubarshi ya huta

   Watace tai dariyar sheqiyanci tace woo Ina ganin soyayya, halan ke budurwansa ce KO? Kafin Nazeefa ta bata amsa Mansur karaf ya amsa Mata yace ba budurwa ta ba ce, jinin jikina ne kuma inshaa Allah ita zata zama uwar yarana very soon, Matan sunajin haka suka Fara zunbure zumbure, daya bayan daya sukabar dakin Dan takaici da bakin ciki, sauran frnds dinsu maza kuwa sukacemai congrats daga gani ya sama abokiyar rayuwa Dan tanada hankali sosai

Anan ta wuni se chan dare ta koma gida, ganinshi datai kamar an soka mata kibiyan sonshi itadai tana kaunar bayan Allah nan

*WASHE GARI*

Mum da dad din Mansur suna asibitin sai Abdallah, Dad ne yace Yau zamui baki fa daga masarautan Mu ta Chan tunda na fada musu Mansur beda lafiya hankalinsu ya tashi, Mansur yace" Abba za azo dasu Hassan da hussaini amma KO? Dad yai murnushi yace yes hardasu jamila da suhaila zasuzo wacce naso a hada auranku

Mansur dai na kwance bece Komaiba, Amma gaba daya yaji gabanshi na mugun fadi

Sallama sukaji, gaba dayansu suka waiga, Nazeefa ce ta shugo sanye da hijab har kasa se hannunta rik'e da basket

   Ahankali ta karaso ta tsugunna tagaisheshu, Dad da mum suka Kara tabbatar da natsuwan yarinyar

Sukaji ta Kara shiga ransu sosai, Ahankali tace yame jiki? sukace jiki Alhamdulillah, Tace Allah Kara sauqi sukace Ameen

    Suna zaune kowa yayi jum a dakin, wayar dad ne yai ringing yana dubawa yaga SARKI, kallon maman Mansur yayi yace gasunan sun karaso,

Nan take fuskar Nazeefa ya chanza dan ta tsana taji gabanta na fadi tasan surely wani abun ne zai faru, Kallon mum tayi tace zantafi mum

Maman Mansur tace bazakije KO inaba ki tsaya yan uwan Mansur zasuzo Ku gaisa mana, Daurewa kawai tayi tace OK ta sama waje se innalillahi wa Inna ilaihir rajiun take ambatowa a a zuciyarta

Sallama Sukaji suka amsa sannan mutanan suka shugo

Kallo daya nazeefa tai musu tagane wanchan Sarkine, da Hajiya bilkisu da Hassan da Hussaini da Jamila da suhaila, Mikewa tayi tare da fadin innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Mezan gani!

Gaba daya suka maida hankalinsu wajenta, Hajiya bilkisu ne Ta kalleta tace kamar nasan fuskar nan

Dukansu suma sukace tabbas sunsan face dinnan amma sun manta inda suka sansu

Nazeefa hawaye ta fara tace tabbas kunsanni, NAZEEFA Ce wacce Sarki ya kawoni gidanku

Jamila Da suhaila Nan suka Fara tari suna zare ido, Nazeefa tace hmm Suhaila kenan da jamila

Hajiya bilkisu shuru tare tana mamakin chanzawan Nazeefa, Hassan da Hussaini kuwa suma kallonta sosai sukai sukace Nazeefa kece Ashe zamu sake haduwa wallahi munyi kewarki sosai meya kawoki nan wajen dama kinsan mansur ne?

Iyayan Mansur kuwa suna tsaye suma sukace duk bamu gane komai ba dama kunsan tane?

Nazeefa ta sake kallon suhaila da nazeefa, Nan take sukai tsure Tsuru, Hajiya bilkisu kuwa hararar Nazeefa ta so mayi tana makira, Allah ya Isa tsakanina dake

   Mansur ne ya mike daga kwanciyar da yake yana Mum Metai miki Nazeefa ce

Tace Eh din itafa, kaga wannnar yarinyar!

  Nazeefa tace Alhamdulillah, Hajiya kiyi hakuri Bazan daukar kazafin da wa ennan makiran yaran nan suka kulla mun ba

    Nan Mum Mansur tace meke faruwa ne dama kunsan tane?

Sarki dai na zaune, Yana mamaki

Nazeefa tace Mum Bari kiji duk abunda ya faru yanzu inada bakin magana

Hajiya Bilkisu tace karku saurareta karya takeyi

Sarkine yai Mata magana yace, Tai shuru,

Mum Mansur ita kuma Tace Fada mana meye faru?

Muje zuwa

FOLLOW
VOTE
COMMENT

UMMIEYXEEY

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now