SILAR GIDAN AIKI

1.6K 95 11
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*PAGE 4⃣4⃣*

Haleemace zaune tayi tagumi, tana Mai bakin cikin rashin zamar mahaifiyarta a gida, kullun yawon siyasa, tsaki tayi ta Kira kawarta mamashow tana sanar da itafa sunsama matsala da Mubeen, yanzu hakama tana gida, Toofa tace gatanan zuwa

Tazo suna hira sosai saiga mahaifiyar haleeman ta dawo, tagansu a gidan! Tace yadai Allah dai yasa lafiya

Haleema duk tai wani iri Tace mum inako lafiya mubeen ya sakeni! Gyara zama tayi tace yame? Tace ya sakeni

Mahaifiyarta tace me kikaimai kodai wulakancinshine ya tashi zai sakar mun ya'ta, Tace Eh mum banmai komai ba tana magana kamar Mara lafiya Dan wasu kuraje sun fiffito Mata

Tace" karki damu za'ai uwar watsi kuwa Dan sunja ma Kansu tonan silili, duniya saitaji kosu waye sirrin da ake boyewa kuwa ya kusan fitowa, Haleema tai murmushi tace OK Mum that's why I love you

*****
Bangaren Su Mubeen kuwa hankalinshi kwance Dan yayi kyau, Mata sekaimai hari sukeyi tunda sukaji ance ya sake matarshi, Shi kam basa gabanshi

***
    Mansur ne zaune a daki, Yaga dai gaskiya bazai Iya zama da mace daki daya ba Dan tsoranshi sharrin shaidan, Ya Kira Nazeefa yace yace zo muyi magana! Ta ziro hijab dinta har kasa tazo ta zauna a kasa

Kallonta tsab yakeyi Dan wani Sonta kara shigarsa yakeyi! Ce Mata yayi tell me more about you wai ke bakida iyaye ne? Hawayene masu zafi suka zobo Mata tace inadasu mana

Dasauri yace suna Ina?

Fashewa da kuka tayi, yana lallashinta, Yace ta Dena kuka tunda Allah ya hadasu inshaa Allah komai zaizo da sauki

Fara magana tayi kamar haka Tace" nima yarinyace kamar kowa amma Mara gata, saboda tun tasowa na tsintar kaina nayi kaskantarciya saboda yanayin dana sama kaina a ciki, iyayena basuji tausayi na ba tun Ina karama suka kaini aikatau, anan na hadu d gwagwarmayar rayuwa, bashi labari tayi har alakarsu da Mubeen, Daka Mata tsawa yayi yace dakata malama, kawai kicemun bakida kamun Kaine

Kukan tane ya tsananta tace" ba haka bane inda kasan waye ni bazaka fada hakaba, kawai yana cikin kaddarar rayuwatace, Kuma ba laifin kowa bane na iyayenane da Ina tare dasu wani abun bazai faru da niba

Taci gaba da bashi labarin Silar barin Gidan aikinta har izuwa jiya da suka ganta

Hawaye sosai Mansur yayi yace gaskiyane ko karya Dan bincike sosai zanyi tana kuka Tace wallahi Kai bincike kaji gaskiya na fada maka

Nan take yaji yana sonta, kishinta da tausayinta, Kallonta yayi yace sannu lalle kinga rayuwa Kala Kala

Kallonta yayi yace zaki Aure na!! Mikewa tsayi tayi Tace" aurefa kace No bazan Iya aurankaba saboda bandace dakaiba

Kallonta yakeyi yanda take magana daki daki Kara burgeshi, yace yes inshaa Allah I'll marry you, rufe idonta tayi ta tashi ta shiga room dinta wai kunya takeji

Mansur kuwa fita yayi, direct gidan Abdallah ya nufa, ya samesu tare da matarshi suna zaune gwanin sha'awa, suna buga soyayya, Abun ya burgeshi sosai

Ya kalle Abdallah yace inason magana dakai, muje waje yace.OK

Fita sukai Abdallah ya kalleshi yace lafiya kuwa? nan Mansur ya kwashe labarin Da Nazeefa ta bashi kaf

Sake Baki Abdallah yayi yace are you serious? Yace wallahi that's what she told me kuma nasan bazatai karyaba

"Ikon Allah Abdallah yace"

Ya kamata kam muyi kokari Mu kaita garinsu ta hadu da iyayenta, Mansur yace nima haka nace

Yace Masha Allah zamui magana idan na koma Nagode abokina

Abdallah yace bakomai Ana tare

@freshummieyxeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now