SILAR GIDAN AIKI

1.5K 91 5
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

   _Masu mun kofarin inkara tsawon page kuyi hakuri faa, Bawai bazan I ya bane, haka kawai na tsara, Ina da abubuwan yini da yawa sai yasa ma bakwa samu a ko Yaushe...thanks_

PAGE 4⃣9⃣

Hajiya Haleema tun a cikin motor ta Fara kuka tana yau na shiga uku, yan sandan da suke tare sukace idan baki mana shuru ba sai kin sani

mubeen Kuwa, hankalinshi gaba daya ya tashi, aranshi yace ace arzikin Su Nazeefa ne Innalillahi wa inna ilahir rajiun, hawaye suka zubomai se addua yakeyi Dan yasan ba wanda zai iya kwatansu sai Allah, bare irin wulalancin da sukaiwa Nazeefa

  ****
Bangaren Hajiya Zainab kuwa Maman Mansur sun koma gida, zama sukai gaba dayansu a falo se tattauna al'amarin nan sukeyi, lalle yanzu duniya ba gaskiya, Uwa daya Uba daya sai ka cutar da Dan uwanka!

Alhaji yace" kibari kawai Yanxu yazamui? Hajiya Tace yanzu maganar na wajensu ai, duk yanda sukeso haka za'ai dasu Mu dama Namu temako ne kawai

   Sannan Alhaji ya kalle Mansur yace" Sannu da kokari, kayi hakuri da zargin da mukai maka,

Mansur yace" haba dad ai hakan da kukai daidaine, yanzu ai da temakonku kuma, Ina alfahari daku sosai da bani goyon baya, Allah ya Kara maku lafiya

Hajiya tai smiling itama Tace that's my son, Tarbiyan da muka baka still yananan, keep it up. Allah kuma ya Kara tsaremu baki daya yace Ameen

***
  Bangaren Su Nazeefa, Sun shiga gidan se kallo suke tayi, Malan Nalado yace sannu ya'ta kinsha gwagwarmayar rayuwa, kiyafe mana please,

Umma Hafsatu kuwa rungumo Nazeefa tayi tana kuka itama tana mai Kara bata hakuri, Tace bakomai Haka Allah yaso yanxu finally gashi na hadu daku!

Baba megadi kuwa se zirga zirga yakeyi, shima da yaji maganar kasa sukuni yayi. Yace tabbas Allah da girma yake, Yar aikin da tazo gidan Ashe gidan wan mahaifintane uwa daya uba daya hmmm

     ****
Kwanansu Biyi a prison, duk sun fitaa hayyacinsu

Nazeefa kuwa Kullun dakyar take bacci Dan tinanin Mansur hanata sukuni yakeyi, abincima dakyar take ci, Seda mahaifiyarta ta lura da hakan take tambayarta me yake damunta sedai Tace Mata bakomai

Bangaren Mansur kuwa, Shima hakan take, Dan 2days dinnan dabe gantaba jinshi yake kamar a daure, Cos he's missing her irin Sosai dinnan

    Washe gari bayan kwana uku!
Yai wanka ya kintsa yace wa mum dinshi zaije gidansu Nazeefa suji ya za'ai da mutanan nan

    Tace kamar ka shiga raina, ya kamata muji ta bakinsu, Dan yanzu komai yana hannunsu, amma dukda bansan hukuncin da zasu yankeba ba please ka basu hakuri karsu dau wani mummunan mataki akansu Dan Allah

   Mansur yace OK Mum zanje duk yanda ake ciki Zan sanar daku, Tace alright ba komai, Dad dinkama tun 6 ya shirya sunada meeting a Abuja driver ya kaishi, Yace OK naga call dinshi kam this morning tace yauwa

Saika dawo A kula da hanya please, kiss yai Mata a kumata yace mum inshaa Allah

Mansur ne sanye da kayan track suit, (Sport wears) Black a jikinsa saboda lokacin sanyine yayi kyau sosai, sannan ya dauko motar mamanshi Fara Sol

Tada motor yayi, me gadi ya bude Mai gate ya fita, tunda ya fita yaji gabanshi na mugun fadi yace Allah yasa lafiya Ameen

Tafe yake a hankali har ya Isa gidansu Nazeefa, knocking yayi mai gadi ya fito

Yace Dan Allah ya kiramai Nazeefa, Yace angama ranka shi dad'e

Da sauri yaje dakin ya samesu suna zaune suna having break fast around 10:00AM,

Yace Wai Nazeefa tazo inji Mansur, dasauri ta tashi Tace" OK je kacemai ganinan zuwa

Shiga daki tayi ta dakko hijab dinta, tace Mama Ina zuwa wannan mutumin ne daya temakeni suka ce madallah Ki gaishe Shi tace zaiji

Fita tayi Cikin natsuwa abunta Hijab dinta har kasa!

   Shi kuma Mansur yana cikin mota yana kare Mata kallo ta glass, yana gainta yaji hankakinshi ya kwanta, Amma kirjinshi nata bugun uku uku

    Bude mata motor yayi yai Mata alamu data shugo, Dag'a kafada tayi wai ita bazata shugo ba, Dan haka shi ya fito, Yana fitowa sallama yai Mata ta amsa

Kowa yai shuru Dan gaba dayansu sun tsinta kansu cikin kunya🤸🏻‍♀










FOLLOW
VOTE
COMMENT

#UmmieyXeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now