SILAR GIDAN AIKI

1.1K 73 4
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad #Freshummieyxeey*

*PAGE 7⃣7⃣*

Tunda Nazeefa ta dawo gida hankalinta na gun Mansur jitai tana bukatar ganinsa, Dan haka ta kirashi tace yazo, Yace kamar kin shiga raina nima I really want to see you, murmushi tayi tace tom Seka zo I love you darling muaahhh
     Tashi tai a dakinta ta shiga room din mahaifinta tace baba na kara dawowa

Yana kwance yanajin radio Ta shugo yace Yar baba ya akaine,
   Tace kan maganar gidansu Ameerah plz

Murmushi yayi yace AI tun jiya akasai musu gidan anadan Kara fentine sai yasa nasan zuwa gobe zasu gama se muje gaba daya mugani, gidan nanan kafin a karasa gidan su inda suke

    Rungumeshi tayi tace you're a darling dad, kasani farin ciki sosai, Yace bakomai Yar baba

Daki ta shiga ta kwanta a gado iskan fanka na shigarta tanajin dadin yanayin, Wani murmushi tayi Tace nagodewa Allah da yasa iyayena suka amsa maganata

Dan Allah nayi kuma inason Mubeen ya gane Na wuce shi a komai, Dan nasan tabbas Shima yanada niyyar gyara musu Ko chanza musu gida

Kwance take tana kallon silin, Tinanin Mansur ya fado Mata, smiling tayi sannan ta fara tina rayuwarta na da, Alhamdulillah tace Tabbas ba Wanda ya dace dani sai Kai MANSUR

   tana cikin tinaninshine Phone dinta ya Fara ringing, dubawa tayi taga LOML murmushi tayi tai picking Hello Sweet Heart ganinan a kofar gidanku, OK My love tace ganinan fitowa yace alright

    Tashi tayi ta chanza rigar da tasa, tasa wata atamfa, Tai daurin chakwar (tuge kaga tsiya) sedan gyalenta a kafada tai bala'in kyau, Flat shoe ta dakko ta fesa turara ta shiga tace wa ummanta da babanta Zata Dan fita sukace OK

   Tunda ta fito Mansur ya kafeta da ido kamar yaune ya fara ganinta, Jiyai ta karamai kwarjini kodan besaba ganinta da atamfa bane, ga dinkin ya amsh jikinta ko Ina na jikinta ya fidda shape kamar ka saceta ka boye

Tabarakallah Masha Allah yace a mind dinshi

Tana matsowa bude mata kofar motar yayi ta shugo ta zauna irin a giccen nan ta gefe tana facing dinshi

Kamshin turaranta ya dake hancinshi, Lumshe ido ya farayi yace Sannu da zuwa gimbiya, Na taso ki ko cikin Rana? Soma magana tayi Murya kasa kasa tace ko kadan habibi nah, Ina fatan kananan lafiya

Bin lebenta yai da ido gashi yasha lipstick, yace inanan lafiya sumul balle dana ganki se naji kamar ankaramun power (Karfi) murmushi tai ta kasa ma magana

Yace Baby dama nazone mui maganar Bikin wani event da wanne kikeso ayi?

Kara gyara zama tayi tace kasan dai bawani frnds gareniba, Kamu se bridal shower kawai zanyi, Yace Alright bakomai Amma kamar nawa zai isheki da komai da komai tace eh senayi calculating Zan maka text yace ok

Suna cikin hakane Abdallah ya kirashi yace yana Ina? Yace wlhi ganinan gidansu Nazeefa

Abdallah yace Kaimun congrats dazu munje asibiti Madan nada Ciki

Wani ihuuu Mansur yayi yace Masha Allah, Nayi muku murna, Allah ya inganta yace Ameen

Matar Abdallah ce ta fisge wayar tace Ango ai Ina fushi dakai ko amarya baka taba kawomun itaba to bazanzo bikinba nama fadama

Afuwan yace Mata inshaa Allah yau Zan kawota, tace banaso seda na roka

Itama Nazeefa ce ta amshe wayar tace Yar uwa kiyi hakuri gamunan zuwa tace to Allah ya kawoku

Matar Abdallah ta bashi wayarshi, itama Nazeefa ta ba mansur wayarshi, 

Mansur yacewa Abdallah matan nan fa da gaske suke, Dukansu sukai dariya sannan suka kashe wayar

Are you ready mutafi yace? Tace nop bare na shiga na sanar dasu Umma yace hakane

Shiga tai ta samesu suna zaune tace Dan Allah Abba zamuje gidan matar abokinshine shine nace bari na tambayoku

Umma tace to bakomai kardai a dade kuma a kula sosai tace Inshaa Allah, Baba ma yace saita dawo.

Daki ta shiga ta chanza gyale tasa babba sannan ta dako jakarta da wayarta ta fito

Kyau yaga ta karamai sosai, bude kofar motar tayi ta shiga, Mansur sake baki yayi yace A'ah wata kwalliyar aka sake Dan ingani,

Tace laa kawai gyale na chanza fa, Yace gskiya kinyi kyau sweet Heart, Matso muyi hoto, Matsowa tai ya dakko IPHONE X dinshi sunata Snapping pics sun bala'in  yin kyau, sannan ya dauketa itama ita kadai

WhatsApp ya shiga Yasa a status maza da abokan arkinshi se comments sukeyi wai sun bala'in yin kyaiu gasu perfect match sedai yai murmushi

Driving yafarayi ahankali sunajin sautin wakar Umar m Sharif har suka Isa gidan

Suna isa Abdallah ya fito yai musu barka Da zuwa sannan yai musu iso har falon, sunyi kyau sosai, Abdallah kasa hakura yayi yace Kai Masha Allah kungankune wallahi kamar anyi, Mansur yace kamar anyi mene? Abdallah yace auren mana, Nazeefa rufe fuskarta tayi Dan kunya

Mansur kuwa yai murmushi suka shiga dakin

Mansur yace Ina madam, fitowa tayi tace ai ba ruwana dakai amaryace tawa,

Mansur yace Duk kuyi ku gama, Maman unborn Itama rufe fuksa tai Dan kunya tace Amaryanmu tashi Mu shiga ciki abunmu, room din matar Abdallah suka Shiga

Sannan taje ta kawo masu Abdallah couscous da miyan kaji, Se ruwa da 5alive ta jiye masu sannan ta shiga da nasu ciki

Nazeefa na gani tace laa dama yunwa nakeji,

Matar Mansur tace yauwa haka nakeso Ashe  ke Yar garice da wasune sai suce wani yunwa

Nazeefa tace baruwana nidai bana wasa da abinci tace yauwa kawata, taci ta koshi sosai sannan suka Fara hita, tora kofa sukai abunsu

Abdallah yace Kaga matan nan fa karsu hada mana Kai, Mansur yace kaima kasan sedai kar a kuma amma mata se Allah ai sukaci dacin abincinsu suna hira

Matar Abdallah ne tace saura befi kwana 6 bako? Nazeefa tace eh Wallahi sannan tace wani shiri kikeyi?

Nazeefa tace se ahankali dama gobe nakeso naje gidan kawata intasan wani gidan gyaran jikine ta Kaini

Matar Abdallah tace kinzo gidan so karki damu

Yanzu dai bani number wayarki zuwa gobe Inkinshirya Zan kiraki sannan kuma ta bata wani sirri tace idan kinkoma gida ki jika kanunfari kinasha Da Zuma idan ma kinada madara ki Kara akai kisha

Tace Kai nagode Sosai

Basu gama magana ba sukaji Abdallah na kwankwasa kofar sukai shuru

Yace Angama gulmar

Matarsa tace bamu gamaba Dan dai ka buga mana kofane yai Dariya

Yace Amarya kizo angonki na jiranki

Fitowa tai suka hada ido da mansur ya kashe mata ido sannan ya daga mata gira yace I love you ahankali, tana kallon labensa tagane me yace Smiling tayi taji kunyarta ya karo

Rakosu sukai har haraban gidan seda sukaga sunshiga motar sunfita sannan suka dawo cikin daki

Matar Abdallah tace Ina ya samo wannan kyakkyawar yarinya haka? Yace it's a long story semun zauna tace Masha Allah

Muje Zuwa

Don't forget to

FOLLOW
VOTE
COMMENT

Thanks

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now