SILAR GIDAN AIKI

2.2K 135 3
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

🎂🍇🎂🍇
*HAPPY BIRTHDAY MY LIPTON GIRL (Khadija S Dogarai)* _May this day be the beginning of another beautiful year for you. May there be pleasant surprises, loads of joy and infinite happiness. Wish you a very happy birthday._🍇 _Have fun dear it's your dayyy...Miji nagari shi nake miki fata_

*PAGE 1⃣2⃣*

Da jajayen idonta Nazeefa ta ke kallonshi cik'e da mamaki tace Mubin I told you to go out banason Ganinka ka fitaaa tana magana tana kuka muryanta na rawa

Yace" i'll go out but... Sai kuma ya tsugunna yana rokonta akan ta temaka ta soshi, shi Sam beson Haleema, Kara kallonshi tayi tace inhar bazaka fitaba ni Zan fitan maka a dakin, kasan dai matsayina a gidan, mezakai da Yar aiki

Bata gama rufe bakiba saiga Hajiya ta sakko daga Sama! jin hayaniya tayi a dakin ta leka, Ganin mubin tayi a dakin ranta a bace ta saukar Mai da Mari, Sannan ta juya kan Nazeefa itama ta mareta tace" yan iskan yara, Wannan iskancin ba anan gidan za'ai ba

Ta kalle mubin tace" Kai Dan bakada hankali ka Tina wacece Nazeefa nan da bakinka kake yawan kawomun karar Tana bin Maza, this n that sai yanzu kuma zakace kana sonta nidai na fada maka a anan gidan ba!

Nazeefa saboda tsaban bakin ciki Kasa komai tayi in banda innalillahi wa inna ilaihir rajiun da take ambata a zuciyarta

Hajiya tace ma Mubin wuce muje! Auranka da Haleema ba fashi Wallahi, Mubin saboda bacin rai yace" anwani andama mutane sai kace banine Zan zauna da Mata na ba a barni na aura Wanda nakeso mana

Hajiya ko sauraranshi  batai ba ta wuce ta zauna a parlor shi kuma daki ya shiga ya kulle, Nazeefa kuwa suna fita ta Kafa sabon kuka tace" aranta wannan wani irin tashin hankaline, Ta roka Allah daya kawo mata mafita

***********Chan Gida Kauye

Baban Nazeefa ne Zaune a waje yanashan iska yana jin radio Saiga wasu matanan guda biyu sunzo wucewa ta kofar gidan, Dayan tana ganinshi ta Fara rufe fuska

Kyalla ido yayi Malan Nalado mahaifin Nazeefa, Yace Malama sahura kidena rufe fuska naganeki sarai Ina yarinyata???

Inda inda ta farayi yace" Mu shiga ciki

SAHURA itace me Kai yara aikatau birni, ita tazo ta ziga mahaifiyar Nazeefa akan yanda take dakyau dinnan akaita akatau Zata samo musu kayan arziki masu yawa

Samun Waje sukai suka Zauna a tsakar gida, Saiga Maman Nazeefa ta fito tana ganinsu tace" Alhamdulillah, Malan Nalado yace ki rufemun Baki se yanzu kika sama bakin magana?

Malan Nadalo ya kalle sahura yace Ina yarinyata daya tilo Kika kaita? Nan ta Fara magana muryanta na rawa tace" tsaya kuji, Malan yace" A zaune ma muke, Sannan ya Kara maimaita Mata ina d'iyata?

Sahura tace Malan kaimun aikin gafara yanzu haka bazance ga inda takeba, ainihin gidan  da na kaita, Shekarun da suka wuce naje Ance sun tashi, Sunyi sabon gida a garin Kaduna

Tana Magana tana kuka tace Dan Allah kuyafemun, Maman Nazeefa najin haka ta tashi ta chakumo rigarta tace Wallahi Ko ki nemonin y'ata ko ai biyu babu, Kakari ta Fara Malan Nalado Yace wa matarshi ta saketa

Nan ta saketa amma tanata wurga Mata harara

Malan yace" Sahura kodai kinsaida mana yarmuce Mu hakura

Idonta yai kananu tace Wallahi bantaba saida kowani yaro ba, Yace" shikkenan Ki tafi akwai Allah, indai tanada rai da lafiya zata dawo wajenmu Dan Addu'a gaskiyane kuma munanan munayinta

Tace Nagode Sannan suka fita suka wuce da kawarta

Maman Nazeefa ta fashe da kuka ita dole tanason yarta

Malan Nalado yace" kinyi shawara danine? Wai meyasa sau tari Mata saisu dingayin Abu batare da mazajensu sun saniba?

Nan itama yai Mata nasiha akan addu'ace kawai mafita Dan Malan nalado mutun ne me tawakkali da Allah, Komai nashi addu'ane Kawai

     ******Kaduna

Kwanan biyu Mubin da Nazeefa basuga juna ba dukda suna gida daya, Nazeefa kuwa ta dau kudirin duk wani abun da za'ai mata bazata daukaba, Shi kuma mubin gaba daya baya cikin hayyacinsa Dan bala'in son Nazeefa yakeyi kamar kullun karamai akeyi

Washe gari MONDAY Mubin ne ya tafi wajen aiki, Yana cikin office kanshi namai ciwo, yace Bari yadan fita cikin hospital din yaga make faruwa

Fitowarshi keda wuya yaga yan Mata yan practical cik'e a Kofar office dinshi, Good morning sir sukai Mai ya amsa sannan yace me kukeyi anan? Sukace Kai muke jira ka fito muje ward round!!

Oh yace musu, kun fito da kayan? Sukace yes sir, Kowaccensu da a bun da take sakawa a zuciyarta idan anbarsu sai suce suna son mubin Haha

Tafiya yake suna binshi a baya kanshi na ciwo but hakanan ya kokarta har suka gama!  bayan yadawo office ne ya zauna wata Mufeeda me shegen kaudin tsiya ta Shugo office din tayi tace" Doctor sannu kasha magani? shouting yai yata yace" get out of my office yanzun nan ke wacece? Aranshi yace ance maki Ina dealing da yarane, Ko manyan ma Inba Nazeefa banga wata Mace ba

Fita office din tai ranta a bace, kawayenta Suka kwashe da dariya alamun ba market, Wata a cikinsu tace kuma in banda abunku high class Guy kamar Doctor zaku tusa kanku? Nikam ban iyawa, kunsan ma Dan wanene kuwa?

Sukace waye ubanshi? nan ta zayyana musu komai AI mahaifinshi babban mutun ne yanada kudi da companies da dama rike baki sukai

Mufeeda ta taba baki tace I love him Kuma sai ya soni nan suka kwashe da dariya suna Mata kirari Dan a cikinsu itace bataji SosaI.....

Manage this please

Don't forget to FOLLOW & VOTE,

*Comment dinku yanamun kadan aradu Adan kara😍🤣*

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now