SILAR GIDAN AIKI

2K 125 7
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

_This page goes to my wattpad Fan *@Meelat85* ina yinki over n over...Ina ganin comment dinki, Thank you so much_

*PAGE 1⃣5⃣*

Misalin karfe 4 na yamma Abban su Mubin ya dawo daga Dubai, yan unguwa sai leke akeyi saboda jiniyar da sukaji sunsan inba Alhaji Sada ba to babban mutun ne ko wani kosa a gwamnati

   Nan aka shiga tsegumi yan unguwa dan Su abun mamaki yake basu wai yaushe Alhaji Sada yai kudi, Gashi koda yai kudin ba temakawa mutane yakeyiba, Kowa tambaya yake shin a Ina ya gaji wannan kudin? Wasu kam suce Dan yankan Kaine! Dan kan kanin lokaci ya mallaka abubuwa da dama

    Tunda ya shiga gidan escort dinshi sai zagaye sukeyi da bindiga a unguwa, Mubin kam kanshi kato yayi shi gashi a dole Dan me kudi

Bangaren Su Faeez kuwa Sunyi exams aranar zasu dawo hutun semester Dan haka Dad dinsu ya tura driver yaje ya dakkosu

Faeez Da Faeeza sai zumudi sukeyi sun kosa su dawo gida su hadu da farin cikinsu Mahaifinsu

Misalin 6 na yamma suka dawo gidan, Da gudu faeeza taje gun mahaifinta Dan ta dade bata ganshiba, Yanaji da ita sosai saboda ita kadaine yarshi Mace, kuma me kama da uwar yayanshi, Se makalewa takeyi a jikinshi, Mamanta ta harareta tace kinfa girma, dad dinsu yai dariya tace" KO tsufa tayi she's still my baby Ki kyaleta.

     8:00PM kowa ya halarta a dining table, kallo daya zakai musu kasan kowannansu na cikin farin ciki da annashuwa, Sunci sunsha kowa ya koshi Alhamdulillah, Suna tashi Hajiya ta kwalla ma Nazeefa Kira akan tazo ta kwashe kayan dasukaci abinci, Faeez yadanji ba dadi arai Dan yasan duk me aikin da aka kawo guduwa sukeyi Dan wahalar aikin gidan

    Batace komaiba tazo ta kwashe ta shiga kitchen ta wanke na wankewa sauran kuma tasa a fridge ta gyara kan dining din

    A falo din babansu suka baje sunata hira har kusan karfe 11 na dare, sannan Dad dinsu yace kowa yaje ya kwanta akwai gobe sai suci gaba da hiran nan yaran suka tafi Hajiya kuma ta Fara nunuwa mijinta soyayya da kauna tace" Alhaji akwai magana nan ya rungumeta yace" su Bari gobe zasuyi maganar! Tace OK habibi nah

       ******
Bangaren M.T kuwa koda mahaifinshi ya dawo direct asibiti aka wuce Dashi aka bashi gado Dan inbanda fisge fisge ba abun da yakeyi, hankalinsu yai matukar tashi sosai

Abun ya daure musu kai sosai, Hajiya kuwa inbanda kuka ba abun da takeyi, Dan KO makamanshin haka Mansur betabayiba

Alhajine yake ta bata hakuri, akan ta Dena tada hankalinta sudai sumai fatan Samun sauki, Nan dai nabarsu.....

   Tun Asuba Nazeefa ta tashi ta daura breakfast, Soya Arish tayi sannan ta dakko raguwar farfesun kazan jiya ta dumama masu, Sannan ta soya kwai, Tasaka ruwan zafi a flask!

D.table tazo ta jerasu Sannan ta share ko Ina tasa turaran wuta, Tadan kunna A.C saboda lokacin Zafine, Kowa ya Shugo fallon Seyace Wow a a zuciyarshi Dan wani sanyin kamshi da yake tashi

Alhajine da Hajiya suka fito rik'e da hannunsu a daidai lokacin mubin shima ya fito daga room dinshi yar karamar tsaki yayi aranshi yace kun tsufa amma kullun cikin soyyayya kuke, nima kubarni na aura wacce nakeso Mana, Da tinani barkatai yaje kan dining table din, Suna cin abinci amma da kunga Mubin kunsan baya cikin hayyacinsa Feelings yakeji sosai, Babanshi na Lura dashi yace Kai tashi ka wuce Daki Lol, Alhamdulillah yace a ranshi dan se ahankali yakeji, yana shiga daki as usual lemon ya dakko yasha sannan ya zauna yana nazarin Wani Abu

Bayan sungama breakfast Faeeza na manne da babanta, Kallonta yayi yace" yarinyata kije daki zamui magana OK tace ciikin shagwaba,

Tana fita Hajiya tace" yauwa Alhaji muyi maganar daya kamacemu please, Alhaji yace Ina sauraronki

Tace" Mubin ne ya dage wai bazai aura Haleema ba kuma Tace inbar bahakaba Sai ta tona *SIRRIN* da muke boyewa, Kan Alhaji ya dau chaji ya kwalla ma Mubin Kira saigashi ya Shugo, Samun waje yayi ya zauna nan Dad dinshi yadingamai Fada akan beda hankaline ze aura Yar Aiki, Ko so yake *sirrin* da suke boyewa ya fito

Mubin ne ya dago Kai a gigice yace" Wani sirri, Dad Sirrin ya Dade be fitoba ni Nazeefa nakeso ita kuma Zan aura, Alhaji ne Kai ma Mubin Mari........

mubin ya rike kumatunsa, Dad yace yaron banza Kawai, in badan nayi kokari akan wannnn sirrin ba da yanzu......Sai hajiya tai sauri ta rufemai baki tace" be kamataba Alhaji

Mubin Bude room din yayi ya fita ya ja kofar da karfi ji kake ghamm, Dad zama yayi yai tagumi yace"  bazaiyuwa ba, Tunda yaron nan ya Fara haka akwai matsala

AI Hajiya kinga irintanan, Dan me aka dakko wannan Yar aikin? Yanzu gashi tanaso ta zaman mana karfan kafa! 

_Hahaha Ina daga waje nai shewa nace ai tukunnama senan gaba zata zaman muku karfan kafa_

Alhaji yaci gaba da fada yace gaskiya a fitar mana da ita anan gidan bansan ganinta

Hajiya ta riko hannunshi tace".  ta fadamai wani sirri a kunne  tace irin sirrin da mukasha yi wannan karon ma shi zamuyi

Murmushi yayi yace to angama sai yasa nake Kara sonki habibty.....

Shin Wani Sirrine wannan wai dasuke boyewa?

Kuma Wani sirri zasuyi?

Chakwkiya.......haha





*Lemme stop from here kuyi hakuri da short pages din da nakeyi*

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now