SILAR GIDAN AIKI

1.3K 74 4
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

    _Sorry 2days kunjina shuru kuyi Hakuri...Ina busy ne da yawa_

*PAGE 5⃣7⃣*

Sundau kusan awa daya suna ta hira, Nazeefa ta bata labarin Dr bashir sosai, tace kiyi hakuri fa na katse soyayyar dake tsakaninku, though bansan irin soyayyar da kike mai ba, nidai a ganina baki dace dashi ba gaskiya

Ameerah ce ta nunfasa Tace hmm nayi mamaki fa, maza sai Allah gaskiya, Allah ya bamu nagari kawai, Nazeefa Tace Ameeen sys nan ta bude Mata WhatsApp group din da take, da yake an turo addu'oi sosai ta sama taji ta rubuta, Sannan Tace ta daure ta dinga yin sallah raka'a biyu fatiha da qulhuwallahu, a kowani raka'a bayan tayi sallama sai ta koma tai sabuwar sujjada ta karanta _La ilaha illa anta subhanaka innee kuntu minaz-zalimeen._ Sau 41 sannan ki roka abunda kikeso, insha Allah, Allah zai karba, kuma ki yawaita istigfari da hailala da salatin manzon Allah S.A.W zakiga chanji a lamaranki

Ameerah Tace amma Nagode sosai, Allah yabarmu tare Tace Ameeen ni Zan tafi, har baking hanya ta rokota sannan ta karasa gida cike da Tinani

  ****
Bangaren Dr Bashir kuwa, tun da yabar Wajen  Ameerah kwata kwata ya kasa natsuwa, Gabanshi se dukan Tara tara yakeyi, gashi sunyi uwar watsi da mubeen yanxu ta yaya ma zaije ya sameshi, Wata  zuciyar Tace gwandama ka je ka sameshi kaji kan labari, cos yaga Nazeefa ta chanzamai sosai so yanason jin ba'asi ya hakan ta faru

***
   Mubeen na kan sallah yana karatun qur'ani Feeza ta shugo Tace yaya Ana sallama dakai a waje! Yace alright kije kice ganinan zuwa, feeza sanye da hijab take ta fito, ta sanar da Dr bashir, kallonta yayi yace anya ba wani Abu a kasa wai yau faeeza ce dasa hijab lalle kuwa, da yarinya sai rashin kunya dasa kaya matsatsu girgiza kai yayi

   Dr Bashir na tsaye a jikin motarshi Mubeen ya fito, Kallo cikin ido sukai wai juna! Mubeen yai ajiyar zuciya sukadai gaisa, Suna tsaye saiga Nazeefa ta sauka a daidaita sahu taba me napep 500 yana Hajiya ga chanjinki tace katafi dashi kawai

   Sake Baki Dr bashir yayi, Nazeefa ce tazo ta wuce ta gabansu ta gansu Su biyu, Wani tsaki taja ta balla musu harara Tace Allah ya shirya kawai, tai shigewarta gidan

    Tana shiga Dr Bsshir yace how comes ta dawo gidan bangane ba ne, still tana aiki a gidan ne ko ka aure ta ne?

   Wani kallo mubeen yamai seda hanjin cikin Dr bashir ya kad'a, Mubeen ya furta ka cucece,

Dr bashir yace kodai ka cuceni, yanzu daga gidan Ameerah kawar Nazeefa nake, tana ganina ta zazzageni, Wai ni ba mutumin kirki bane, kaga abunda kaiwa Nazeefa nima ya shafeni KO?

Mubeen sa hannu a aljihu yayi yana karewa Bashir kallo, yanzu wallahi badan giwa tayi lafiya ba daka sani ayau dinnan, ai dama mugun abu zuwa yake ya dawo, duk abunda kasa naiwa Nazeefa shike dawo maka,

    Inda kasan yanda Nazeefa ta dawo gidan nan Seka yi mamaki, tabbas na yarda, duk abunda mutun yai mekyau zai gani inma mara kyau ne zaigani

   Bashir yace ni duk bangane me kke nufi ba ka fito a mutun kaimun bayani

   Nan Mubeen Yace tun da za'a auramun Haleema, Nazeefa Taji labari tabar gidan ai ka sani! To from then dai ta hadu da that guy dinnan (MANSUR TURAKI) har yakaita gidan Su sukazo nan gidan, intakaice maka dai Nazeefa she's my cousin, babanta da babana Uwarsu daya ubansu daya,

  Dr Bashir zare ido yayi yace" did I heard you well kuwa? Mubeen yace yanda kaji haka maganar yake, mune fa har prison aka kaimu, yadai boyemai dad dinshi yaiwa Baban Nazeefa asiri saboda gori da tonan asiri Ko nan gaba!

Innalillahi wa Inna ilahir rajiun, Dr bashir yace lalle Allah baya zalunci,

    Mubeen ya kara da cewa tabbas kuwa, Ashe dad dinta me kudin gaske ne, intakaice maka dai duk kudin babana, Mahaifinta ya fishi kudi, shuru Dr bashir yayi ya kasa cewa komai

   Nan sukaci hirarsu nidai nai gaba abuna nabi Nazeefa dan jin ya ta dawo gida!

   Nazeefa na dawowa gida Taga ummanta da Hajiya asmau suna kitchen suna dafa abinci, ajiye jakarta kawai tayi ta shiga kitchen din itama ta tayasu,

   Faeeza kuma da yake bata iyaba tana zaune a kujera tana game a waya

   Tana ganin Nazeefa ta shiga kitchen itama ta bita tana ganin yanda sukeyi har suka gama

Sunci abinci sun koshi sosai dare tayi kowa ya shiga daki danyin bacci

Nazeefa kuwa waya sukai sosai da Mansur se kusan 11 tai bacci, while Faeexa itama sunata ta chats da fri3nds dinta a group, Har zasu kwanta Nazeefa Tace inaso inyi miki magana though bansan KO zakiji dadinta ba, kinga duk sanda Mamanki Tana dafa abinci kidinga zuwa kina tayata, if possible ma kije kiyi kawai

   Faeeza Tace hakane zandingayi kinsan amma ban iya girki ba har yanxu, Nazeefa tace OK KO dinga kallon tashar girke girke, kuma Zan bada number dinki ai adding a group Tace OK Nagode

*NOTE* Please iyayanmu ba gata bane wai kace bazaka dinga ba Yaro girkiba, kodan kunada kudi kace zaka nemo Yar aiki no, Yayankunr Ku kuka haifa ai da dadi ace danka ya Iya girki sosai, sannan yaran kuma koda bazasu baka ba on your own kadinga dafawa, Kana kwabawa, *practice makes perfect* wata rana zaki Iya



FOLLOW
VOTE
COMMENT

#Freshummieyxeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now