SILAR GIDAN AIKI

1.2K 79 4
                                    

*SILAR GIDAN AIKI*

          
NA
    *UⓂMIEY XEEY*

*Wattpad@Freshummieyxeey*

*Dedicated this page to Slimzy house of novels, Inayinku over❤💥*

*PAGE 6⃣7⃣*

    Nazeefa ne zaune a 2seater tana mamakin wai sune a wannan babban gidan, Tana cikin tinani faeeza tazo ta katse mata tinanin da takeyi tace dear 6s kije kici abinci mana

    Murmushi tayi tace OK, Dining table suka nufa, Taga abinci Kala Kala, Ga wani kamshi da yake tashi hannu tasa ta dauka cinyar kaza soyayye taci Sannan ta kurba strawberry juice yayi dadi sosai, zama tayi tasha juice din sosai, Mubeen kam duk inda tayi seya bita da kallo cos heart dinshi na beating duk sanda ya ganta, Fita waje yayi ya dakko wayarshi ya kirata yaji wayar a kashe, tsaki yayi sannan ya koma falon

Su baffan Nazeefa kuwa da umma hafsatu abincin suma yai musu dadi sosai gashi sun kwaso gajiya dan haka suka zauna suka kwasa girki

    Nazeefa kuwa tuni daki ta shige, Tana ganin room din tasan bana kowa bane se nata, Dan hanyar shiga room din wani flowers tagani tasan confirm natane, dakin tabi da kallo taga komai sabo! Ga Dan gadonta madaidaici ga wardrobe harda wajen karatu kamar dakunan yaran yan kasar waje, Fadawa a gadon tayi hade da cewa Alhamdulillah, Silar gidan aiki yamun Rana and na koya abubuwa da yawa, Allah kasa mucika dakyau da imani, sannan ta tashi zumbur kamar wacce aka tsungula

Toilet ta nufa naga ta wangale baki, ita tunda take bata taba ganin toilet mekyan haka ba kawai taji tana sha'awar yin wanka Dan haka ta shige ta cire kayan jikinta tai wanka ta fito ga mayuka Kala Kala nan ta shafe jikinta se kamshi takeyi

    Nan ta tino kayantafa kamar na dakin Ummanta, Dan haka ta kwallawa Faeeza Kira Tace Dan Allah ta dakko mata karamin akwatin kayanta na ciki tace Ok

nan take ta dakko Nazeefa ta sa wani kaya jallabiya irin na 20K dinnan Wanda mansur ya siyo Mata, Yar Karamar jakarta ta dauka, ta fesa turare sai ta yafa Dan karamin gyalen, kallo daya zakai Mata kasan ta hadu, dukda duguwar rigar da tasa be hana fitowa da shape din jikintaba..

Tana fitowa suka hada ido da mubeen, Gabantane yai mugun fadi amma ta fuske, Zuwa tai kan dining table Tacewa iyayanta zataje wajen Kawarta Ameerah sukace OK Sai kindawo karki dade, Su Mubeen kuwa da faeeza sun zama yan kallo _uhmmm rayuwa kenan fa na gaba ya koma baya duniya makaranta_

Tunda ta fito mubeen Binta da kallo yayi yaji Sam bazai Iya hakuraba, kararaf yayi yace tom muje in kaiki

Aranta tace Za'ayita kuwa, Umma hafsatu ne ta katse Mata tinanin da takeyi tace kije yakaiki din, Tai maza ta washe baki tace OK Muje tom aranta kuwa ita kadai tasan me take ayyanawa

Fitowa sukai ya bude mata sit din gaba yace ta zaune tace nop, you're my driver so baya Zan zauna KO so kake in zauna a gaba a aza budurwanka ne?

Smiling yayi Dan shima yasan Akwai magana a bakinta

Fita gidan sukai ya hau kan titi ya Fara driving Ahankali, kallonshi tayi tace malan driver meye haka kayi Abu da jini mana kana tuqi kamar Wanda kwai ya fashewa a ciki

Tsayawa chak yayi yace bazan tuka motar ba kuma ya kulle Ko Ina dan yasan ba karamin aikinta bane ta bude tace zata fita

Rantane yai matukar baci tace Kai wani irin wahalalle ne nace maka banasonka banasonka sai shigemun kkeyi ko to wallahi ka saukeni ko na fasama glass din motan da takalmina tana magana tana kokarin Cire takalminta

    Dayaga da gske take tuni yai unlock din motor ta samu ta fito tana wurga Mai harara

Shikam mubeen na tsaye ya rasa irin zuciyar Nazeefa

Mansur kuwa se juyi yake a kan gado ga frnds dinshi maza da mata harda Abdallah a ciki zagaye dashi, Yan matan wajen se iyaye suke ko akwai wanda zaice yanaso cos duk wacce kuga gani a wajen son Mansur turaki takeyi

***
   Nazeefa kuwa napep ta Tara tace akaita gidansu Mansur, tana zuwa tace me nepep ya jirata tambaya zatai, Zuwa tai ta tambaye gate man din wani hospital aka Kai Mansur
   Da yake ya ganeta nan take ya sanar da ita sunan Hospital din harda room din da yake tace OK nagode

    Yima me nepep din magana tai yakaita hospital din yace angama
    Tafiya kadan sukai suka Isa asibitin

Ciro 1000 tai ta bashi yace ga chanji tace kabaari kawai, yanata jinjina mata yana sa mata albarka tafiyan da befi abaka 250 amma tabashi 1000 lalle yau akwai sa'a

     Da sauri ta shiga asibitin hankalinta a tashe, batasan wani yanayi zataje ta sameshi ba

Kai tsaye ta shiga room din da aka kwatanta Mata, Sallama tayi gaba daya yan dakin suka juyo suna kallonta, Wani kamshi kawai yake tashi, ahankali ta karasa gadon da yake kwance

    Riko hannunshi tayi tace Mansur, idonshi a kulle, jiyai anrike hannunshi ya fara bude ido ahankali

Bude idon da zaiyi kenan sumai 4 eyes da Muradin zuciyarshi

Kashe mai ido tayi ta sakar Mai wani murmushi, yunkurin tashi yayi tamai alamu da Nooo ya kwanta kawai

Abdallah kuwa kallonta yayi yace sannu da zuwa madam

   Tace yauwa amininmu ya jikinmu? Yace jiki da sauqi hajjaju

     Gaba daya yan wajen maida idonsu sukai wajen Nazeefa se a lokacin suka kare mata kallo sosai gaskiya yarinyar ta hadu, Matan wajenma sunsan ta hadu bare mazan wajen

Watace Ta ce Abdul 6ter mansur ne KO?

Murmushi kawai yaimata yace she's more than a 6ter

Kowa yai tsuru tsuru yanason jin dangartakar dake tsakaninsu

Mansur da nazeefa kuwa kallon juna suke Kamar zasu hadiye kansu, Dan mansur ya ma manta beda lafiya wani Iron kallon yake jefa mata hade da kashe ido

   Abdallah ne yadan buga gadon da Mansur yake kwance

Se a time din ya tina akwaifa mutane a dakin🤣

_Muje zuwa_

Don't Forget to

VOTE
FOLLOW
COMMENT


taku Har abada #Ummieyxeey

SILAR GIDAN AIKIWhere stories live. Discover now